*NIKAAH*
*Marriage for Rent**By*
*HANAADY*
Rahama Aminu Bala*WhatsApp*
*09064767796*HE HAD THE COURAGE
TO REMARRY.
WILL HE FIND THE COURAGE TO
LOVE AGAIN?Marubuciyar
BAHAAR paid book
And now NIKAAH(Rental Marriage).......
Free book*Page 3*
___Karime bata dawo part nasu ba sai bayan sallar la'asar koda ta shugo zaune ta tarar dashi falo , wucewa bedroom tayi abunta ba tareda tayi masa magana ba.
Toilet ta shiga domin watsawa ruwa baki sake tabi pants da bra d'inta cikin ruwa.
Fuu ta fita zuwa falo ,idanuwan sa a lumshe shuke yana sauraren karatun Qur'ani mai girma.
Tsaye tayi saman kansa ,hannuwanta saman 'kogunta masifa na cinta tace ya naga kayana a cikin ruwa ??
Jin hayaniyar ta saman kansa yasa , a hankali ya bud'e idanuwan sa ,ji tayi gabanta yayi mugun faduwa ,janye idanuwan ta tayi daga kallonsa .Tashar da yake kallo ya canza zuwa wata tashar sannan murya k'asa k'asa yace bakya ganin karatun Qur'ani ake amma ,kike ta d'aga murya kaman kinje kasuwa.
Banza tayi dashi
Ganin yanda tayi banza dashi yasa ya Mi'ke tsaye,yana mai tattara wayarsa da keys d'insa .
Bedroom ya shige abunsa , da ido ta bisa harya 'bace mata da gani ,zama tayi saman kujerar tareda d'aukar remote ,canza tashar ma Hjy Karime ba iyawa tayi ba ,gashi kuma tana son yin kallo.Bedroom d'in ta shiga ,zaune ta tarar dashi yana latsa system, d'an nesa dashi ta tsaya sannan tace,nace dan Allah ko zaka d'an canza mun tasha ,banza yayi da ita d'an satar kallon sa tayi sannan tace dan Allah ka taimaka mun .
Daina latsa system d'in yayi ,murya k'asa k'asa yace a wane 'kauye aka auro ki , bata ji meya fad'a ba sosai iya auroki taji sabida haka washe baki tayi sannan tace kasan Jangefe , d'an ta'be baki yayi sannan yace aaa.
Kyara tsayuwa tayi sannan tace garinmu na can wajen Poly Katsina , murmushi tayi sannan tace yanzu garinmu ya kusa had'ewa da cikin garin Katsina .Jin yayi shuru yasa ta mayarda kallon ta saman fuskar sa , had'a idanuwa sukayi saurin janye idanuwan ta tayi .
Mi'kewa yayi tareda ficewa zuwa falon , remote control d'in ya d'auka ,wane channel ya fad'a k'asa k'asa, canza na gani sai in za'ba ta fad'a tana mai kwurama 'katuwar tv d'in ido.
Canza channel d'in ya fara , yana kai wata tasha wasu turawa ne mace da namiji keta sumbatar juna saurin canza tashar yayi ita kuwa Karime saurin janye idanuwan ta tayi daga kallon wurin ganin yanda yake ta canza channel ta'ki za'ba yasa a kai mata Zee Cinema kasancewar Star time ce ,juyawa yayi ya fara tafiya , nagode ta furta bai ansa mata ba illa bedroom d'in sa daya shige bedroom.
Zaune take ta kurama tv d'in ido ,wata matashiya ce ta shugo falon da sallama ,cikin ladabi tace ma Karime Hjy tace nazo na tafi dake sashenta ,cikin mamaki Karime tace wacece Hjy , cikin mutuntawa tace itace mahaifiyar mijinki ,jin abunda tace yasa Karime mi'kewa , bedroom d'in ta shiga zaune ta tarar dashi yana karanta wani littafi na addini , d'an matsowa tayi kusa dashi tazarar su ba wani mai yawa bace remote control ta mi'ka masa da kallo ya bita , murmushi tayi sannan tace dan Allah ka tsayar mun da tashar da ka kai mun naje na dawo ana kirana kuma kallon ya fara mun dadi'.
Ganin bai anshi remote d'in ba yasa ta d'aura shi saman gado ,cikin sauri ta figi hijab d'inta tareda ficewa ,da kallon tausayi ya bita domin yasan wula'kanci , tozarci da cinmutunci suna can suna jiranta.
Haka Momynsa tayi wa Sa'adatun sa washe garin kawota gidan, tasa aka kira ta ita da Hjy Mariya suka tozarta masa ita wanda lokacin da hakan ta faru baya da masaniya ,abunda zai iya tunawa shine bayan dawowar Sa'adatu daga part d'in Momy zaune ta tarar dashi saman gado bata yadda sun had'a ido ba ta shige toilet acan ta sasha kuka kaman ba gobe.
Ta dad'e sosai cikin toilet d'in sannan ta fito Koda ya tambaye ta akan yaya ga idanuwan ta sunyi ja ce masa tayi wai ruwane data sakarwa kanta shine ya shiga idanuwan ta ,sai bayan rasuwar Sa'adatu sannan ya samu labrin irin u'kubar da Sa'adatu tasha wajen Momy, ba komai bane yasa take tsanar Sa'adatu sai rashin auren d'iyar kawar ta da beyi ba.
YOU ARE READING
NIKAAH ( Marriage For Rent)
RomanceHE HAD THE COURAGE TO REMARRY WILL HE FIND THE COURAGE TO LOVE AGAIN? NIKAAH (Marriage for rent).