MENENE ILLA TA ?
Tunda idrissa ya sunkuyar da kansa saida ya d'auki tsawon minti uku zuwa biyar bai d'ago ba saboda tsananin tashin hankalin da ya shiga na maganar mai babban allo. "Lafiyarka kuwa akwai wata damuwa ne?"
"Ba..." dakatar da kansa yayi domin yasan matu'kar yace babu damuwa to ya amince da auren aminatu kenan kuma bai ta'ba mafarkin auren aminatu ba yarinyar da gaba d'aya bata san menene hankali ba balle ta mallakeshi, bata san kanta a mace ba balle har ta san wanene namiji, yarinyar da dududu shekarunta goma a duniya amma mai babban allo ke son had'a aurensu?
Danne zuciyarsa yayi yace "Baba Aminatu fa? Aminatu 'karamar yarinya ce har yanzu sannan zuwan da nayi gidan malam hamza naje wurin bintu ne mun gama fahimtar juna har malam hamza yace yana son ganinka a tsaida lokaci".
Shiru mai babban allo yayi ya kafe idrissa da idanu kafin ya ja dogon numfashi yace "to... hakane? Shikena tashi ka shiga daga ciki zan duba na gani".
Daga yanayin da mahaifin nasa yayi maganar ya san babu alamun amincewa saidai bai kushe kai tsaye bane dalilin amintakar da take tsakaninsa da mai goro wadda ta zarta 'yan uwantaka. Tashi yayi ya shiga gida ya samu Aminatu har wannan lokacin tana zabga kukan korarts da mai babban allo yayi, tana kallonshi ta goge hawayenta cikin sauri ta tashi tana buge zaninta tareda bankad'e zanin ta sake d'aurawa ko a jikinta wanda ya sanya idrissa kau da kansa cikin sauri ya ja tsaki yayi gaba ya barta a nan, hakan ya sake sosa ma Aminatu rai ta koma ta cigaba da borinta a 'kasa saida Baba sahura ta fito ta maketa ta jata zuwa d'aki.
Hajiya yaya kuwa tunda taga idrissa ya shigo bai le'ka sun gaisa ba ta fara tunanin akwai abinda ya faru, babban tsoronta kar ace mai goro ya hana idrissa auren Bintu domin ita kanta shaida ce irin soyayyar da d'an nata ke ma Bintu kuma tana jin a ranta babu wadda ta dace da shi sai Bintu.
Tana zaune tana sa'ke sa'kenta taji sallamar idrissa, amsawa tayi tace "bismillah" ya d'aga labule ya dur'kusa ya shiga d'akin tare da tura fitilar aci bal-bal d'in da ta haskaka d'akin gefe, da murmushi Hajiya yaya yace "mutan yanleman an dawo lafiya? Ya ka baro su?"
"Lafiya lau baba azimi tace a gaidake amma na manta aiken da kikace na kar'bo". Murmushi Hajiya yaya tayi tace "babu komai zata aiko bibalo ai ranar kasuwa, ga abincinka nan a gefe".
Girgiza kai yayi yace "na 'koshi". Saidai neman hanyar da zai sanar ma hajiya maganar mai babban allo yake yi, haka dai suka gama zamansu tana ta janshi da hira tana 'ko'karin bugun cikinsa amma tamkar wanda akan dannewa baki ya kasa furta komai gashi damuwa ce fal zuciyarsa har ta gama bayyana a fuskarsa, a haka sukayi sallama da hajiya har zai fita tace "idrissa nasan akwai abinda yake damunka amma ka kasa fad'a min, ba zan tilastaka ka fad'a min ba zan taya ka da addu'a Allah ya kawo maka mafita a ko ma menene".
Take yaji idanunsa sun ciko da 'kwalla yace "Amin hajiya". Ya fita da sauri, yana zubewa kan katifarsa ya goge 'kwallar da ta zubo masa ya hau aikin tunanin da ya aureshi a 'yan kwanakinnan.
Hajiya yaya kuwa zuba ido tayi jiran mai babban allo tana so su tattauna kan idrissa, ta san ko da mai babban allo bai san damuwar idrissa ba yana da hanyoyin da zai bi ya gano mecece damuwar a sau'ka'ke fiye da ita, dukda sha'kuwar dake tsakaninsu kasancewarsa d'anta d'aya tilo a duniya amma basu da kusancin irin wanda mai babban allo da idrissa ke dashi, kunya da kawar da kai na mutanen da yasa basu da wannan kusancin dukda ta yar da wata kunyar tana iya kiran sunansa a bayyane, tun ana zund'enta a kan hakan har ya zamo jiki.
Sai can dare sannan mai babban allo ya shigo saida ya tabbatar dukka almajiransa suna makwancinsu ya kuma sallami d'aliban dake da gidaje a kewayen ya tabbatar sun isa lafiya sannan ya shigo gida. Hajiya yaya macece mai fara'a haka ta tari mai gidan nata tana ta zuba mishi sannu tana mishi addu'a, mai babban allo yana matu'kar alfahari da matar tasa hakan ya hanashi tara mata kamar yanda sauran abokansa malamai ke yi, ita kad'ai tana wanzar masa da farin cikin da yake nema shima kuma yana 'ko'kartawa wurin faranta mata.
YOU ARE READING
MENENE ILLA TA?
Non-Fiction"Idan kina ganin hakan shine dai-dai a zuciyarki to kiyi hakan BINTOU. ni kuma nayi alƙawarin cewa bazan taɓa dakatar dake ba, sai dai kafin ki zartar da hukuncin da kike ƙokarin zartarwa ina so kiyi tunani Akan ƴaƴan dake tsakanina dake...." cewar...