MENENE ILLA TA ?

18 2 0
                                    

       MENENE ILLA TA ?
      (True life story)

              06
     

Juyi kawai yake yana kallon hasken farin wata, yanda zuciyarsa ta ‘kagu da son ganin Bintu gani yake tamkar gari ba zai waye ba, ya shafe awanni uku a kwance yana tunanin bintu tun yana jin motsin mutanen gidan har ‘kafafu sun d’auke alamun kowa ya nufi makwancinsa.

Soyayyar da yake ma bintu ta wuce duk tunanin mai tunani saidai abinda yake d’aure mishi kai yanda mai babban allo da Hajiya basa nuna goyon bayansu akan maganar bintu musamman mai babban allo, ya san ‘kudurin mahaifin nasa a kansa saidai ya’ki amincewa ya bada fuskar da mahaifinsa zai bijiro masa da zancen dake cikin zuciyarsa, ya kan ji hajiya da mai babban allo suna tattauna maganar tsakaninsu amma bai ta’ba sani ba domin a zuciyarsa babu d’igon ‘kwayar zarra na soyayyar Aminatu, ko ba don soyayya ba halayen Aminatu da masifar sangartarta ya sanya baya jinta a ransa da wani matsayin da ya wuce na ‘yan uwantaka, uwa uba tazarar shekarun da ke tsakaninsu, saboda haka zaici gaba da kakkaucewa maganar Aminatu har lokacin da zai tsaya da ‘kafafunsa ya nemi auren bintu yasan Mai babban Allo hazai cr komai ba a wannan lokacin.

Da wannan tunanin bacci ya d’aukeshi abinda bai ta’ba aikatawa ba wato bacci babu addu’a, hakan yasa baccin ya gaza mishi dad’i kiran sallar farko ya farka wanda gaba d’aya baifi awa d’aya da rabi da samun baccin ba. Tashi yayi ya fito cikin sauri ya d’aura alwala yana jin Mai babban Allo yana yiwa Ibrahima fad’a a kan tashi sallar asuba da wuri.

Bayan sunyi jam’in sallah an idar Idrissa ya zauna a wurin ya fara bitar karatu domin a yanzu baya bu’katar yayi amfani da allo, yayi saukar ‘kur’ani tun yana shekaru 9 hadda kuma yana shekara 11 hakan ya bashi damar tilawa a kai a kai, soyayyar Idrisa da karatun addini ya sanya mai babban allo yake jinsa sosai a zuciyarsa fiye da sauran ‘ya’yan ɗan uwansa dake gidan. sannan da kasancewarsa d’a d’aya tilo daga matarsa guda ɗaya tal da yafi so kuma yake ƙauna. amma dattako da sanin ya kamata ya sanya mai babban Allo ko da wasa baya nuna banbanci a tsakanin idrissa da ƴaƴan ƙanin nasa.

Saida d’alibai suka fara taruwa sannan idrisa ya tashi ya shiga gida ya nufi d’akin hajiyarsa, daga waje ya dur’kusa ba tareda ya shiga ba yace “Hajiya barka da Asuba”.

Kafin ta amsa yaji an banko labulen Aminatu tayo waje tana doka uban tsalle ta ce “yaya Idrisa ka ga an bani na siyo ƙosai zaka ci?”

Girgiza kai kawai yayi ta taƙe bakinta tace “ka yiwa kanka” ta wuce da gudu ta fice daga gidan. fitarta tayi dedai da fitowar hajiya yaya fuskarta ɗauke da murmushi ta ce “Allah ya shiryaki Aminatu bansan yaushe girma zai zo miki ba”. Murmushi sukai gabaɗayansu  sannan ta amsa mishi gaisuwar ta fito mishi da abin kari, kallon tuwon yayi yana murmushi ya ce “shiyasa Aminatu ta fita sayo ƙosai kenan”.

“Ka san halinta ai, kawai ta tashi tace ba zata ci tuwo ba babar tata kuma taƙi sauraronta shine tazo nan. Uhmm na dai bata mun rabu lafiya” cewar Hajiya

“Hajiya ai da kin rabu da ita kema”. Ya furta yayin da ya fara cin tuwon dake gabansa, yasan ba sauraronsa hajiya yaya zatayi ba domin yanda suke ririta maraya ko da d’an maƙwabta ne abin zai baka mamaki balle nasu, hakan yasa Aminatu ko ƙuda ya taɓata wasu lokutan sai ta ɓare baki saboda gata.

“Yaushe zaka je yan leman?”

Shiru yayi ya sunne kai cikin kunya sannan a hankali ya furta “idan na duba gona an jima zan wuce insha Allah”.

“To ka gaishe su dan Allah, akwai saƙona wurin Baaba azumi da zaka karɓomin idan kaje”. Amsawa yayi da toh sannan ya ‘karasa cin abincinsa a lokacin da Aminatu ta shigo tana tsalle tsallenta, wani zama tayi ta bankad’e zaninta hankali kwance ta fara cin ‘kosanta wanda ya baiwa Idrees takaici ya tashi ya fice daga d’akin yana jin hajiya yaya na mata fad’an wawan zama.

MENENE ILLA TA?Where stories live. Discover now