Daga Baba Sahura zuwa kan Hajiya yaya babu wanda kalmar daya faɗa bata girgiza ba. Tsit gurin yayi aka rasa wanda zaice ƙala saboda halin tu'ajjabin da Idris ya jefasu a ciki, ganin yanayinsu yasa ya ƙara yin ƙasa da murya cikin alamu na miƙa ƙoƙon bara ya ce,"nasan ni mai laifine a gareku amma idan akai duba da ƙaddara zanan ubangiji ce, wannan kaɗai ya isa yasa kuyi min afuwa bisa kuskuran dana tafka baya. Nasan kunada cikakken sani a kan hakan tunda kune kuka ɗora tunani na akan yarda da ƙarfin ƙaddara tun ina ƙaramin yaro, ku duba girman Allah ku tsaya min a karo na biyu ni kuma nayi alƙawarin ba zan taɓa watsa ƙasa a idaninku ko in karya alƙawarin dana ɗauka akan Aminatu ba...."
Hannu Baba Sahura ta kai ta share gumin daya fara barazanar keto mata, yayinda a ɓangaren hajiya yaya takejin kalaman Idris tamkar saukar aradu a tsakanin kunnuwanta. Rage girman idanunta tayi waƴanda suka fito waje sabida mamaki ta ce,"a iya sanin da nai maka sam baka shaye-shaye Idrissa. Amma yau da kayi wannan furucin yasa na fara tantama anya baka shan wani abu kuwa?" tayi maganar tana ƙureshi da idanunta ma'abota kwarjini da haiba tun daga tsarin Halitta, bata jira jin amsar da zai bata ba ta miƙe ta shiga ɗaki zuciyarta na harbawa cikin matsanancin tsoron data jima bata tsinci kanta a ciki ba.
Ganin haka yasa Idris ya matsa kusa da Baba Sahura cikin yanayi irin na ƙasƙantar da kai ya ce," irin kallon da Hajiya yaya ke min irinsa nake gani kwance a tsakiyar idanunki baba. Dama nasan za'ai haka muddin na futo muku da abinda ke ɓoye cikin tsokar zuciyata, sai dai banida wani zaɓi amma wllh har cikin zuciyata nake kallon Aminatu a matsayin zaɓin mafi dacewa da rayuwata."
"kar mu fara haka da kai Idrissa. Na tabbata don ka rasa Bintu ne yasa ka rarrafo don kayi madadi da Aminatou, sai dai bana jin zakayi nasara cimma burinka akan wannan murɗaɗɗen al'amarin da kazo dashi. Idrissa ni uwa ce, koda bani nayi naƙudar Aminatu ba a ƙalla nasan zafinta kasancewarta ƴar ruƙo a gareni kuma amanata. Bazan hanaka Aurenta ba muddin ta tsaida kai a matsayin zaɓin ranta, nafi kowa sanin halayenka kaf babu na yarwa balle a ƙyamata, sai dai, duk da kasancewarka adali idan Aminatu bata amince da soyayyarka ba wllhi babu wanda zai mata dole. kamr yanda lokacin daka zaɓi Bintu akanta Aminatu babu wanda ya tilasta maka aurenta....." Baba Sahura ta faɗi hakan cikin sanyin murya gamida ɓoye ɓacin ranta akan abiɓda Idris yaiwa Aminatu a shekarun baya....
Sarai ya fahimci inda kalanta suka dosa, wannan yasa yai bakare ya kasa furta komai saboda nauyin da tsokar harshensa tayi. Hannu ya kai ya share gumin dake ratsowa ta tsakanin saisayayyen gashin kansa, ajiyar zuciya ya sauke mai nauyin gaske sannan yay ƙasa da kansa cikin jin kunyar tsiyar daya tabka a shekarun baya ya ce,"shikenan nagode ƙwarai Baba, kuma in sha Allah i will try all my best wajen ganin na samu yardar Aminatu ba tareda tilastawa ba, a duk lokacin da nayi nasarar yin hakan zan tako har gabanki in rusuna inyi godia, saboda kin bani damar da mahaifiyata bata bani kamarta ba....." yana gama faɗin haka ya miƙe a hankali cikin tsayayyen takunsa ya nufi ɗakin hajiya yaya cikin kamewa irinta cikakken namijin daya san ciwon kansa.....
Hakanan sai baba sahura ta samu kanta da bin bayansa da kallonsa har ya ɓace mata da gani, ta jima a gurin tana saƙawa da kwancewa a har Baba Sama'ila ya shigo ya sameta a nan inda take zaune. Yanayinta kaɗai ya kalla jikinsa ya bashi akwai wani da take juyawa a cikin ranta, in badan haka ba da tuni ta jima da shigewa ɗaki. Saboda tunda Hajiya yaya tabar gidan Baba Sahura ta haramtawa kanta zaman tsakargida da zarar al'muru yayi, a nitse Baba Sama'ila ya zame takalmin fatar dake ɗaure a ƙafarsa, sannan ya haura kan tabarmar ya zauna daga gefanta. Cikin taushin murya ya dubeta ya ce,"na jima banga uwar Aminatu a cikin irin wannan yanayin dana sameta ba, ina fatan ubangiji yasa kunnuwana su jiye mini alkhairi." ya faɗi hakan cikin azancin magana kamar yanda yake mata a duk lokacin da yake son bugun cikinta
Ajiyar zuciya Baba sahura ta sauke sannan ta dubeshi cikin alamun son ta shanye damuwar da maganar Idrisa ta jefata a ciki ta ce,"yaushe ka shigo gidan baban Aminatu?"
"yanzu na shigo gidan amma na jima da dawowa, na tsaya a ƙofar gida munyi kalacin dare tareda Malam ne. Amma mai ya faru na ganki duk a dame?" yayi mata tambayar yana tsareta da idanu
"hmmm bari kawai Baban Aminatu wai idrissa ne ya sameni yake gaya min wai yana so ya Auri Aminatu." tayi maganar cikin rashin baiwa abin mahimmanci
"se ke kuma kikace masa me?"
"cewa nayi yaje ya nemi yardanta, idan ta amince dashi shikenan ni banida matsala da haka, amma idan bata amince ba to ya sani wllahi babu wanda zai tilasta Aminatu kan dole saita aureshi."
Murmushi mai sauti Baba Sama'ila yayi lokaci guda ya kai hannu ya fara zame safar dake ƙafarsa. Sai da ya gama cirewa tsaf sannan ya ɗaga kai ya dubeta ya ce,"a cikin abinda kika faɗa sam banga laifinki ba Sahura, amma dai ina gargaɗinki koda wasa karkice zakiyi yunƙurin cusawa Aminatu ra'ayin da banata ba akan Idrisa, saboda ina jiye miki tsoron abinda ka iya zuwa ya dawo a nan gaba."
"hmmm Baban Aminatu kenan. Koda wasa bana jin zan iya aibata Idrissa a idanun Aminatu don kawai ya zaɓi wata saɓaninta, kawai dai banason wata matsalar ta ƙara ɓullowa ne kwatankwacin irin wadda ta faru a wancan lokacin."
"Allah ya kyauta." baba Sama'ilah ya faɗi hakan cikin son ya katse hirar gudin karta samu gurbin yin tsaho a tsakaninsu.....
*** *** ***
A nitse Idris ya ɗaga labulan ɗakin bakinsa ɗauke da sallama, a zaune ya samu hajiya yaya bisa kujerar da aka ƙawata ɗakin da ita ta rabka uban tagumi, cikin sanyi jiki ya shiga ɗakin bayan ya zame takalman fatar dake ƙafarsa, kai tsaye inda take ya nufa ya zauna cikin rashin guzari gamida baiyananniyar nadama ya ce,"kiyi haƙuri don Allah. A matsayina na ɗa guda ɗaya tilo a gareki na gaza baki farin ciki kamar yanda ƴaƴa nagari bawa iyayensu, amma in sha Allahu a wannan karon aurena da Aminatu shine zai zama sular gyara kurkuren da muka aikata...." ya firta hakan cikin sanyin murya
"ga dikkan alamu ka manta abinda ya kawo mu Kankia Idrissa, sulhu mukazo nema akan matsalolin da suka faru a baya, na roƙeka don Allah karka ƙara gaiyato mana wata matsalar a karo na biyu.." Hajiya Yaya ta faɗi hakan cikin alamun roƙo.
Jikinsa ne yai sanyi don haka ya gaza cewa komai, a ƙalla sai da ya shafe mintuna uku sannan ya ɗaga kai ya kalleta ya ce,"in sha Allahu zaki sameni mai ƙoƙarin kiyaye duk abinda zai janyo maki saɓani da Mai babban Allo a karo na biyu."
Jinjina kai Hajiya yaya tayi cikin alamu na gamsuwa da maganarsa ta ce,"ubangiji ya baka iko." da wannan gajeriyar Amsar data fito daga bakinta hirarsu ta dasa aya, cikin yanayi irin na wanda ke fafutukar ɓoye damuwar a ƙasan zuciyarsa Idris ya miƙe ya fita daga ɗakin. A haka ya isa ɗakinsa ya tura ƙofar ya shiga, a nitse ya fara ƙoƙarin rage kayan dake jikinsa sakamakon zufar da yake ji tana bibiyar jikinsa.
Fankar dake ɗakin ya kunna bayan ya zare rigar farin yaɗin dake jikinsa, hakanan sai ya samu kansa da jin nauyin maganar daya firtawa Baba Sahira, ɗan gajeran murmushi ya saki tareda nannauyar ajiyar zuciya a haɗe.
Haƙiƙa yayi rashin kunya shi kansa ya san hakan, amma wutar muradin dake ci a cikin tsokar zuciyarsa ya shallake tunanin mai tunani. Zamewa yayi ya kwanta bisa bisa gadon da aka ƙawata ɗakin dashi, hakan daran ranar ya shuɗe a gareshi ba tareda ya cimma matsaya ba. Sai dai, ya ƙudurtawa kansa cewa zai tsunduma cikin maneman Aminatu koda ace zai sha mafi ƙololuwar wahala kafin ya mallaketa.
Washe gari da safe, cikin hanzari ta shirya cikin doguwar riga maroon, kyakkyawar fuskarta wadda nisawar shekarun ta suka taimaka wajen fito da kamewarta tai haske sosai, yayinda chocolate skin ɗinta ke baza glowing tamkar matashiyar ba'amirkiya. Cikin nutsuwa take gudanar da komai don Aminatu sam bata da gaggawa ko garaje a cikin lamuranta, wayarta ƙirar Samsung A25 ta ɗauki ruri cikin sassanyar waƙar Neha kakkar.
A nitse ta ƙarasa gefan gadon ta ɗauki wayar tana bin screen ɗin wayar da kallo. Sunan Dr. Saifuddin Alƙali ne ya baiyana cikin tsakiyar idanunta, a nitse Aminatu tai picking call ɗin tareda karawa a kunnenta na dama ta ce,"Assalamu'alaikum."
Daga can ɓangaren Dr. Saif ya numfasa sannan ya kada baki ya ce,"wa'alaikumussalam." ya firta hakan yana mai gyara zamansa bisa kyakkyawar kujerar da yake zaune akai, jin yayi shiru baice komai ba ne yasa Aminatu tayi saurin cewa,"a gafarce ni ranka ya daɗe, ina bisa hanya nan da gusawar mintuna shabiyar da yardan Allah."
Lumshe kyawawan idanunsa yayi waƴanda ke ɓoye cikin gilashin ƙara ƙarfin gani sannan yaja dogon numfashi ya ce,"Gareki Ƴar mutan kankia." yayi maganar cikin tattausan sauti
Mamakine ya ida cika zuciyarta, don haka ta gaza sauke wayar daga kunnenta kimanin wucewar wasu sakwanni, ganin da tai tsaiwar bazata kaita ko ina bane yasa ta sauke wayar tareda rarumar jakarta ƙirar kamfanin Gucci ta saɓa a kafaɗarta. Har zata fita sai kuma ta dawo saitin inda Mami ke kwance ta shafi gefan fuskar yarinyar cike da ƙauna, sannan ta juya da hanzari ta nufi ƙofar fita daga ɗakin.
A nitse Take ɗaga sawayenta harta isa ƙofar ɗakin Baba Sahura ta tsaya daga bakin ƙofar tayi sallama, bata jira amsawarta ba don tasan wata ƙila bacci takeyi, zama tayi a kan kujerar dake falon tana ƙoƙarin gyara zaman agogon fatar dake ɗaure a tsintsiyar hannunta Baba Sahura ta fito daga ɗaki.
Mamakine ya kama Baba Sahura ganin yanda lokaci ya tafi ba tareda ta farka ta ɗoro musu abin karin kumallo ba, dariya Aminatu tayi sannan ta kada baki ta ce,"Baba kwantar da hankali dama yau da gobe sai Allah, nace ki dinga baiwa kanki hutu amma sam kinƙi yarda, dole ne a samo ƴar aikin da zata kula da ɗawainiyar gidan nan. Girma ya fara kamaki Baba atlist ya kamata ace kina samun hutu." tayi maganar tana kawar da murmushin dake kan fuskarta.
"To naji uwar magana da tsari, lokacin fitarki ya wuce ya kamata ki tafi karki makara."
Bata ce komai ba ta miƙe ta nufi ƙofa ba tareda ta ƙara Cewa komai akan maganar ba
Sarai Baba ta lura da sauyawar yanayinta, wanda koda bata buɗe baki tayi magana akai ba ta san haushitaji. Don haka tayi murmushi mai sauti ta ce,"Allah ya bada sa'a da nasara Aminatu."
"Amin" ta faɗa ba tareda ta juyo ba, lokacin data bar ɗakin Baba sahura kai tsaye ɗakin Hajiya yaya ta nufa, ganin ƙofar a rufe yasa ta fahimci bata tashi ba don haka ta nufi ƙofar fita ahanzarce tana kallon agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunta.
Tun kafin ta isa zauren gidan ƙamshin turarenta ya game gurin, wannan ƙamshin shine babbar alamar data alamtawa Idrisa fitowarta.
Sai dai kafin ya yunƙura ya fito daga ɗakinsa tuni Aminatu ta fice daga zauren zuwa inda mai babban allo ke zaune yana lazimi.
Har ƙasa ta rusuna ta gaisheshi sannan ta ƙasa da kanta ta ce,"Abbah zan tafi office." tayi maganar tana mirza chain ɗin jikin jakar data rataya.
Ajiyar zuciya ya sauke kana ya dubeta cikin alfaharin kasancewarsa uba a gareta ya ce,"Ubangiji ya kaiki lafiya Aminatu."
Sosai Addu'ar ta huda zuciyarta, don haka ta miƙe cikin natsuwa ta ce,"ngde Abbah." ta faɗi hakan tana barin gurin zuwa inda motarta ke ajiye. Seda taja motar sannan mai babban Allo ya janye idanunsa daga kanta yana mai binta da kyakkyawar addu'a.
A nitse take tuƙa matar tanayi tana bin karatun alƙur'anin da Shaik Abdullahi Abbah Zaria ke rerawa, har cikin ranta zagin muryarsa ke hudawa wanda hakan ya saukar mata da nutsuwa sosai.
Ƙarfe 7:30 ta isa General hospital ɗin dake cikin garin Kankia. A nitse ta nemi guri tai paking ɗin motar a inda aka tanada don hakan, sannan ta buɗe murfin motar ta fito bayana ta gyara rolling ɗin dake kanta. Hand bang ɗinta da ta ajiye a sit ɗin dake kusa da nata ta ɗauka sannan ta rufe motar ta tasrma hanyar da zai kaita ofishinta kaitsaye, tun kafin ta isa inda take son zuwa ta fara gaisawa da mutane. Wannan sauƙin kan na Aminatu shine ya janyo mata soyayyar ma'aikatan Asibitin da dama.
Da sallama ta shiga cikin ofishin, hand bag ɗinta ta fara ajiyewa a kan table ɗin daya ƙawata ofishin sannan ta kai hannu ta ɗauki lapcord ɗinta wadda ke ɗauke da hatimin sunanta a jiki ta sanya, sai da tayi bisimillah sannan ta zauna akan kujerar tana kallon tarin file ɗin dake zube bisa table ɗin. Nimfasawa tayi don tabbas tasan yau akai tarin aiki a gabanta, ajiyar zuciya ta sauke mai gajeran nauyi sannan ta fito da glashinta na ƙara ƙarfin gani ta saka bisa idanunta.
Cikin nutsuwa ta janyo file ɗin farko ta buɗe wanda ke ɗauke da Suna Farouq Sulaiman a jiki, nan ta fara duba bayanan dake cikin file ɗin tsaf sannan ta miƙe tsaye. Kafin ta motsa taji an turo ƙofar da sallama.
Idanunta ne ya sauka cikin nasa idon kimanin wucewar sakwanni,
A hankali tayi ƙasa da kanta cikin sanyin Murya ta ce,"Iam sorry sir, I wasted a lot of time before I arrived, now I will prepare for the surgery in sha Allah."
Jinjina kai yayi ba tareda ya ce komai ba ya juya ya bar ofishin
Ajiyar zuciya Aminatu ta sauke mai nauyin gaske, sannan ta koma jiɓir ta zauna akan kujera tana maida numfashi. Gaɓaɗaya ta rasa dalilin da yasa take rikicewa idan tai Arba da Doctor Saif Alƙali, ganin zata ɓatawa kanta lokaci da tunanin banza ne yasa ta miƙe ta fara shirin shiga tiyatar dake gabansu........
![](https://img.wattpad.com/cover/342810273-288-k243458.jpg)
YOU ARE READING
MENENE ILLA TA?
Non-Fiction"Idan kina ganin hakan shine dai-dai a zuciyarki to kiyi hakan BINTOU. ni kuma nayi alƙawarin cewa bazan taɓa dakatar dake ba, sai dai kafin ki zartar da hukuncin da kike ƙokarin zartarwa ina so kiyi tunani Akan ƴaƴan dake tsakanina dake...." cewar...