MENENE ILLA TA 12

25 5 0
                                    

MENENE ILLA TA ?

012

Duƙushewa tayi a ƙasan ledar ɗakin idanunta na zubar da hawaye akan hukuncin da Mai babban Allo ya zartar a kanta. Tunda ta Aureshi yau kimanin shekaru Ashirin da bakwai bata taɓa yaji ba balle akai ga maganar saki, yau sai gashi ta janyowa kanta faruwar abunda ke barazanar tarwatsa mata zuciya.
Kuka sosai Takeyi tamkar ƙaramar yarinya, yayinda kalmar mai babban Allo ta ƙarshe ke kai komo a tsakanin kunnuwanta!

Nadama ce fal cikin ranta yayinda wani sashi na zuciyarta ke bata shawarar ta nemi gafarar mai babban Allo. wataƙila ta samu damar da zata gyara kuskurenta a karo na biyu, Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta kai hannu ta share hawayen daya wanke mata fuska still bata miƙe daga inda take durƙushe ba. Daga can ƙasan ranta takejin abinda tayi dedai ne, becouse babu abinda ya zarta farin cikin d'anta a rayuwarta. ta sani dole nan gaba mai babban allo zai sauko domin bashida wanda ya wuce idrissa a duniya.

Duk wannan abinda ya faru hajiya yaya bata bari idrissa ya sani ba. haka ma Aminatu, Baba Sama'ila ne kaɗai ya sani shida Sahura, suma kuma ta roƙesu akan su rufe maganar sakin da akai mata har lokacin da bintu zata tare a cikin gida. sannan bata so Aminatu ta sani don har ga Allah tana jin tsoron damuwar da yarinyar zata shiga. Dika suka amince da muradinta sannan ta samu ƙarfin gwiwar sanar da mai babban Allo cewar zata zauna tayi idda a ɗakinta kafin ta tafi, bai mata musu ba ya amince domin abinda addini ya umurta kenan.

A daren baba sama'ila ya samu idrissa ya sanar mishi da aurensa da suka d'auro da bintu, tsabar murna idrissa har d'afe baba sama'ila yayi godiya kuwa ya yita tafi cikin carbi yana yi yana hawaye, Aminatu tana jin yanda yake godiya ga baba sama'ila tareda mi'ka godiyarsa ga Allah hakan yasa ta fita cikin azamarta domin tambayarsa meke faruwa.

"Ya Idrisa lafiya naji kana ta murna ko hajji aka biya maka?" Ta furta hakan fuskarta d'auke da murmushi tana gyara hijabin jikinta, dariya yayi yace "zan iya cewa farin cikin da nake ciki yafi na zuwa hajji Aminatu, alhamdulillah kawai zance sabida burina na duniya ya gama cika alhamdulillah na mallaki...... Uhmmm dama dama Uhmmm"

shiru yayi da ya tuna baba sama'ila yace mishi kar ya sanar da ita, murmushi ya sakar mata cikin daburcewa da alamu ma rashin gaskiya yace "saidai mu gode Allah kawai Aminatu amfanin gonar dana shuka ne ya fito yayi kyau sosai, wannan yasa naji nake farin ciki da murna. amma karki damu jeki ciki kinji? Da safe zan fad'a miki sauran". Yayi firta hakan yana ƙoƙarin raba ƙwayar idanunsa da nata wanda yake jin tasirinsu na huda gabaɗaya ilahirin jikinsa

Bata ko amsa mishi ba ta koma d'aki jikinta a sanyaye domin tun wayewar gari ta fahimci akwai muhimmin abu dake faruwa, ta lura duk mutanen gidan na cikin wata irin damuwa marar misaltuwa amma sai gashi idrissa na murna, "ko dai abinda zuciyarta ke saƙa mata ne ya faru?" Cikin sauri ta kawar da wannan tunanin tace "idan haka ne ai wani zai fad'a min dole!" ta firta hakan a fili zuciyarta na mata wani irin ɗaci wanda kai tsaye barata iya fassara girman lamarin ba.

Tashi tayi ta nufi d'akin hajiya yaya suka sha hirarsu amma da zarar ta ɗauko maganar abinda ke faruwa a gidan sai hajiya yaya ta kauce, hakan ya tabbatar mata dole akwai abinda aƙe ɓoye mata. A haka aka d'auki kwanaki biyu ko gaisuwa bata shiga tsakanin hajiya yaya da mai babban Allo sabida yanda ya ɗauki abin da zafi. A can ɓangaren idrissa kusa sosai ya maida hankali wurin 'karasa gyaran sashin da aka bashi a cikin gidan wanda zai zauna da matarsa.

A safiyar rana ta biyun ne aka sanarwa Aminatu batun auren idrissa, sannan baaba sahura ta sanar da ita ranar da za'a kawo amarya. duk wanda yaga Aminatu a wannan ranar sai ya tausaya mata, domin tsananin firgici da tashin hankalin data shiga yasa ta kasa kuka.
Daga cikin tsokar zuciyarta take cin raɗaɗin abin wanda ya haifar mata da wata irin rama ta lokaci guda, kasan motsin kirki tayi sai kawai ta janye idanunta daga kan Baba Sahura ta ƙurawa bango idanu.

MENENE ILLA TA?Where stories live. Discover now