CHAPTER 43-44

55 1 0
                                        

DESTINY LOVE

OUM YASMEEN


43-44

A gigice ta farka tana wai waye da sauri ta kunna lamp ɗin datake kusa da gadonta haske ne ya mamaye dakin zuciyar ta na wani irin bugu yawa ta waɗo zuru kafafuwan ta tayi kasa domin wallahi baza ta ci gaba da kwana a dakin nan ba haba wannan masifar har ina ta yau daban ta gobe da ban wayar ta ce tayi ƙara da sauri ta dauka ganin me kiran dafe kirji tayi tace

"Innalillahi bily ta mutu ,

Wayar ce ta sulale a hannunta tabbas mun taɓowa kan mu a bin da ba'za mu iya ba na shiga uku sauran ni

kuka take yawa ranta zai fita bata san safiya tayi ba sai ganin haske ta window ɗinta tayi ya shigo yawa wata mahaukaciya ta tashi ta shiga toilet a gurguje tayi wanka shafshaf tayi sallah ta ɗauki key ɗin motarta ta fita a ji tayi an bigeyta juyowa tayi ta dauke nasreen da mari ai bata dure hannun ta ba ta shararara mata mari cikin mamaki tace

"Nasreen Ni kika mara...?,

kallon tara sauran kwata nasreen tayi mata tace

"Au tantama kike ko in ƙara miki..?,

Wani kallo tayi mata na zamu gaura ya tayi gaba tace

"Bani da lokacin ki amma kin ɗauki bashi,

Dariya Nasreen tayi tayi gaba tana yar waka

shiga motar ta yi cikin sauri take tuƙi sai kotu road a bakin kofar gidan su bily ta faka da sauri ta fito ta shiga gidan gwuiwoyin ta kasa ɗaukar ta sukai lokacin da taga bily a shinfiɗe ko wanka ba aimata ba

sa hannu tayi ta buɗe gawar zaro ido tayi ganin irin kisan da akai mata

shaƙe ta akai har ta mutu zubewa tayi tana kuka har haka hada ta bata dena kuka ba

ga su nucy suna zo har da tafida ko kallon safna basuyi ba ganin mutane sun fara raguwa safna ta fito sa'a taci garo da nucy da tafida suna tare kusa da su ta tsaya tace

"Yanzu shawara daya ta rage mana ko ku ɗauka ko karku ɗauka amma ita ce mafitar halin da muke ci inba haka ba to lashakka za'ai tayi mana zari dadde kuma kunsan baza mu iya tsare mai ba bubuwan nan sun isheni haba yau ba bayijjah ba bily jibi fa.....,

Kallon hadarin kaji tace

"Ci gaba muna sauraran ki...,

yar ƙaramar dariya tayi tace

"NUCY TAFIDA hmmm ku naga har yau bakuyi nadama ba to wallahi kuna gamai mai aiki kashe ku zaiyi kamar yarda ya..... Sai tayi shiru bata ƙarasa ba saka maƙon ganin NAZEER da tayi sallama NAZEER yayi musu tafida ya  meƙo mai hannu suka gaisa yace

"A'a kaga dan jarida duk inda aka ji anyi wani abun sai kunzo ,

dariya yayi yace

"Wannan shine aikin mu kuma hanyar samin abincin mu ,

NUCY tace

"Hakane Allah yasa ba da wata a kasa ba ake bibiyar rayuwar mu,

DESTINY LOVEWhere stories live. Discover now