DESTINY LOVE
Oum yasmeen
Free book
Karku manta kuyi following ɗin channel ɗina
https://whatsapp.com/channel/0029VaLdFeg4SpkQ9xyW5c0k
EPISODE 6-11
Amma ina garin kaucewa ya bugewata mota cikin sauri ya fito ya tsaya kusa da motar me motar ne ya fito nesa ba kusaba tareek ya girme sa zallar hutu da jin dadi suka zauna mai ganin irin kallo da yake wa tareek ya haɗiye wani miyau me ɗaci yace
"Dan Allah kuyi hakuri ban luraba na buge ka,
Cikin fusata yace
"Kai wanne irin mutum ne mahaifiyar mu na ciki kana ƙoƙarin bugemu ni wallahi ban zan damuba inni naji ciwo ammafa mahaifiyar mu da yan uwana wallahi da wani abu ya same mu da bazamu taɓa yardaba sai munyi Shari'a da kai,
Rumtsai idanuwansa yayi ganin ƙaramin yaro nagasa mai magana yace
"Nima ai ba'a son raina zan bugekuba tsautsayine tun da Ubangiji ya nufa sai anyi kuyi hakuri hurin da ya lotsai zan kai a gyara muku in hakan be muku ba ku fadamin kuɗinta in siya muku wata tunda na lura sabuwa ce ,
Kallon hadarin kaji ya shiga yiwa tareek tama raina musu hankali tab ya buɗe baki zai magana yaga mahaifiyar su na kokarin fitowa ya ja bakin sa yayi shiru
ganin irin ja'injar da akeyi da ɗanta ta fito sanye da lufaya wata buɗurwa na bayanta bata tsaya ta kalli wanda yayi musu wannan ta'annatin ba tace
"Aisar shigo mu tafi kyale shi ,
Four eyes sukai da tareek yace
"Dan Allah kuyi hakuri,
Bata tsaya bashi amsa ba ta shiga mota shima ganin ta shiga aisar ya shiga ya ja su shima shiga yayi ya fara tafiya a hankali saboda ciwonsa na gab da tashi buɗe baki yayi tari ya sarke shi da sauri ya jawo tissue paper ya goge bakinsa aikuwa sai ga jini guda guda parking yayi cikin wahala ya kifa kansa a sitiyarin matarsa wayar sa ya shiga lalubowa cikin Sa'a ya ganta cikin fitar hayyaci ya shiga contact ya lalubo wata number bakinsa na sarkewa yace
"Kazo kabuga ka daukeni ya sake wayar domin ciwon yayi tsamani cikin yardar Allah sai ga jamil nan ya kiɗema da yaga halin da abokin sa ke ciki kama shi yayi ya mai dashi baya ya kwantar kai tsaye asibitin da ake duba shi ya kai shi cikin gaggawa suka rufa akansa har numfashinsa ya dai daita
____________________
Ɗurƙusawa yayi cikin ladabi yace
"Sitti gani,
Gyara zama tayi yarda zai dau maganar da mahimmanci tace
"Ubaidullah daman maganar yaron nan ne an kyelesa ba aure ina so inhada shi da yar uwarsa ta rufa mai asiri safna ta aure shi da kyar na shawo kanta ta amince ,
Da sauri abbey ya ɗago kai cikin ladabi yace
"Sitti banƙi tataki ba amma da a kƴele shi lokacin da yayi niya yayi aure duba da irin tashi ƙaddarar dake ɗawainiya da shi a gaskiya bazan iya tursasa tareek ya aure ta ba sitti har yanzu tareek be yafemin ba har yau alaƙar mu bata dawo daidai ba duk da ko a fuska baya nunamin ninasan abin da yake nufi da hakan bazan so in ƙara lefi agunsa ba ,
Tsawa ta daka mai tace
"Wato ni zaka nunawa iya kacina akan dan shegen da ka haifa uwarsa ma ta guje shi mu mun ruƙesa ya ci ace ta juyo ta waiwaye sa tun yana zanin tsunma to in kaman ta bari intuna baka da kuɗin mahaifinka aka dinga suyimai madara ana bashi har ya girma wata ranma inta ƙare kafin asiyo nonan akuya ake bashi har ya girma sannan zaka nuna min iya kacina akan sa wallahi gaji na rantsai maka zan tsine maka in yau ba a ɗaura musu aure da safna ba ai yar ɗan uwan kace duk abin da zai yi yazo yayi ai ba tsoransa nake ji ba duk taurin kansa da kafiyarsa dole mu tanƙwara shi ai bashi ya haifi kansa ba mu muka haifesa muna kuma da iko akansa tana kai wa nan ta tashi ta bar gun

STAI LEGGENDO
DESTINY LOVE
Storie d'amoredabi'ar family ne ba ruwan wani da wani tamkar bajini daya ba wata iriyar kaddararriyar rayuwa suke me ban mamaki da tsoro haka ya samo asali daga iyayen su sun nuna son ya'yansu dan uwanka be isa ya tsawatar wa da ya'yan dan uwansa ba ran kakansu a...