EPISODE 8️⃣
Mahaukacin faduwa gaban Hawwa yayi jin yanda Khaleel yariketa fuskanshi manne a kafadanta jikinshi na rawa kana gani kasan this is the first time yataba jin karan ko ganin bomb ma, da dan sauri ta tureshi yakoma baya yana kalle kalle kunnenshi sunmai dummm baiji ko kadan, yana kokarin kunnenshi yadawo daidai yaga Hawwa tai wani irin super tai wajen aguje tana shooting nasu, wow! Dabadan he knows this is real ba and he's present a live location dinba dayace action movie yake kallo, she's so fast in harbi, and wayanci he notice ba shoot to kill take ba, cus baiga wanda ta harba akai ko zuciya ko ciki ba, she mostly target legs and hands, da gudu ta shige cikin container yarinyar Hawwa tagani tana kuka sosai tana ihu ta kankame kunnenta sabida karan bomb ga wuta data gani, ahankali Hawwa ta duka gabanta tasa yatsanta akan lips nata tace "shiiiiiiu I'm fairy Angel Anty I come to rescue you from bad guys,, dena kuka" juya mata baya tayi tace "hop on my back, hau baya" takai yatsunta biyu tana taba wuyan Hayatu ganin yana numfashi yasa tashiga kiransa "Hayatu Hayatu, wake up" ahankali Noor tahau bayanta ta kankameta, dasauri Hawwa ta tashi she will come back for Hayatu, Noor first fitowa tayi ahankali goye da Noor ganinsu yasa Khaleel yatashi yataho wajen su da sauri yazo ta bayanta yana murmushi sosai looking and sounding so emotional ganin little baby shi that looks so scared and terrified a bayan Hawwa yace "Noory" dasauri yarinyar tace "Dadyyyyy" karban ta yake shirin yi daya daga cikin criminals din data harba a kafa dake wajen yadauki sandan dake wajen yadaga zai bugama Khaleel dake kokarin karbe Noor daga bayanta, karaf Hawwa tagani dawani irin sauri tai pushing Khaleel yafadi a side nata sandan ya sameta a hannu da karfi ya yagi skin nata sai jini, kafa tasa ta daki kan thug din ya sume dasauri Khaleel yatashi yana kallon hannunta da jini yabata hannun rigan already yace "you are bleeding" ahankali tace "it's fine, leave Noor help me pick Hayatu" gyadamata kai yayi tawuce dajin goye da Noor neman Abraham taganshi a sume akasa, dagashi tayi sukai mota tasashi abaya tasauke Noor ta sata a baya itama daidai Khaleel na zuwa da Hayatu a sheme ya ijiyesa abaya yasa hannu ya dauki Noor ya kankame ajikinshi yarufe kofan baya yadawo gaba yashiga ya zauna Hawwa taja motan da mugun gudu tana calling DIG office waya for backup. "I repeat my team are down, goons are also down seriously injured calling for backup, code 22028IV" Khaleel ya kankame Noor data kankameshi dukansu suna kallon Hawwa dake tuki around 11 nadare tana magana har saida DIG yadaga wayan dan da farko voicemail ne, ahankali Khaleel yakalli hannunta dudda baya ganin ciwon but hannun riganta was bloody.
Kusan around 1:13AM na tsakar dare sukakai gidan sharp sharp aka bude musu gate cus DIG yarıga ya sanar da zuwansu, tun kafin su karasa tsakar compound din Excellency da Momy da mutanensu ke tsaitsaye suna jiransu, tun kafin tai parking Excellency da Momy suka shiga gudu suna tahowa wajen motan, tana parking mota Excellency yabude gaba Mommy tafashe da kuka tana kallon Noor datai bacci yarinyar ta rame tace "look at my Noor oh no no" takai hannunta tana karban Noor daga hannun Khaleel, shikuma Excellency yasa hannu yana fito dashi Khaleel yasauko yace "Dad did you call her Dr"? Dasauri yace "yes yes everything is set, yana clinic" Mommy tashiga shafa Khaleel da hannu daya tace "hope babu abinda yasameka Khaleely na welcome Alhamdulillah, babu abinda yasame ka"? girgiza mata kai yayi ahankali, Hawwa tadan matso taja kofan motan duk suka juyo suka kalleta takoma driving sit, Excellency yace "you guys did a great job Miss Hawwa welldone, dare yayi kuzauna anan zuwa safiya" calmly and politely tace "my team are down zan kaisu clinic dinmu" dasauri Excellency yace "ai da kin bari Dr ya gansu anan we have clinic anan" anatse tace "DIG yariga yace na kaisu clinic dinmu" dan ijiyan zuciya Excellency yace "okay but drive safe, bari nakara muku mopol su biku for extra security is night" dan gyadamai kai tayi cus batason ta kara gardama tai reverse da motan sannan tai kwana hakanan Khaleel samin kanshi da kallonta yayi daidai tana figar motan da gudu Excellency yace "ayi gudu a sannu" Khaleel yajuya ahankali yayi ciki.
YOU ARE READING
GARGADAN SO
RomanceStory of a police woman in her 30s da maza sukaki aure sabida they feel intimated by her career🔥😂 READ AND ENJOY