25

404 12 0
                                    

EPISODE 2️⃣5️⃣

Ni'ima kuka kawai take bana wasaba, tana ganin tunda aka haifeta bata taba feeling wannan kalan zafin da zuciyanta kemata yauba, for years sunyi aure itada Baban Yaseer basu taba having issues ba like babban issue haka, batada wani complain akanshi but yau yayi hurting nata kwarai, kalan soyayyan datagani a idanun Aliyu ko ita baitaba mata shi ba, duk soyayyan dazaisa kafara stalking mace kana bibiyan hotunanta harda na kusan tsiraici ma dan kayan bacci ne ba karaman soyayya bane, soyayya ce ma dakana bukatan kaga therapist, he is sickly in love with Hawwa that's idan akwai word din, ciwon son Hawwa yake, yanzu Hawwan ta Baban Yaseer zaiso? They've been through so much together with Hawwa, Hawwa is her biggest support bazata taba manta sanda Hawwa tasayo mata form na school of Nursing takawo mata ba, sabida lokacin Babanta baida lpy basuda kudin daza'a saimata form agida haka Hawwa tadinga dinki tahada kudin tasayo mata form 5k takawo mata that day was the happiest day of her life, Hawwa tarakata taje tai entrance exam na shiga school of nursing din, dataci Hawwa was happier than her ma datai jarabawan, bayan 2days aka kirata zuwa interview still Hawwa tabita sukaje tajirata awajen tayi tafito suka tafi gida dagabaya aka saki admission taci an bata admission, babu kudin registration Hawwa tadinga dinki day and night, tasaida babban wayanta alokacin tasa sim nata akaramin waya takawo mata 30k itama Maman Ni'ima tasaida sarkanta da dankunne aka hada 20k daga wajenta aka hada mata taje tai registration da 50k, the first ever book da pen datai rubutu dashi a school of nursing Hawwa ta siyamata su, hawaye ta share tana tuna rayuwansu da Hawwa duk yanda mutum zaiyi tunanin friendship, kawancenta dana Hawwa yawuce haka, sabida kawance ne mai asalin amana, Hawwa harda Maman Ni'ima take fada akanta just like yanda take fada da Baba akan Hawwa tanajin haushinsa kan Hawwa haka sukema junansu wajen iyayensu, they supported each other like better half, kawance su babu ha'inci, babu kyashi ko rowa, babu bakinciki, they're always happy for each other, dudda tayi aure Hawwa bata taba mata bakincikin wani abuba, datana da ciki wlh wlh ko Baban Yaseer mai cikin baikai Hawwa kula da ita ba, idan tana craving wani abu Hawwa zata iya barin aiki taje ta nemo takawo mata, yanzu haka yaranta su Yaseer sun fison Hawwa kan mahaifiyarta grandmother su sabida aminci da kaunan dake tsakaninsu, she's just crying bitterly bamatasan ina zata saka kanta ba, kawai taji ta bama kanta tausayi bamatasan inda zatasa kanta ba wannan wani irin intertwine situation ne haka? Wani irin kaddara ne wannan? Ita da Hawwa started friendship ana maganan tun suna around 6yrs old cus primary one suka hadu, yanzu suna 30yrs, 20yrs plus friendship kifa kanta tayi akafanta tana shesheka tajiyoshi an budemai gate yafita tasan mosque zashi yau juma'a.

**
Har yamma na rannan Friday din nan shiru ba kiran Ni'ima which is so unlike her, dudda su Ramla dake damunta da labarai but still binibini Hawwa na duba wayanta ko Ni'ima tamata watsapp message ko kira ko wani abun amman shiru, tasake kira but still ba amsa dan damunta abin yafarayi sosai.
Bayan sallan magrib suna zaune sunacin abinci duka tare harda Hamza wayan Ammi yahau ringing wayan ta kalla taga Baba ne hakan yasa tadauki wayan tafito daga dakin dan bataso yaran especially su Ramla susan maisa Hawwa tazo tawuce ta shiga side nasu Hamza zama tayi kan katifarsu tayi dialing number Baban ringing daya yadaga ya buga mata sallama yace "ya wajen naku Rukayya" Ammi tace "Alhamdulillah" ijiyan zuciya Baba yasauke yace "Baban Yaseer ya sanar dani Hawwa na wajenki kice mata ni ban koreta ba ta tattaro tadawo gidan nan" anatse Ammi tace "sabida kacigaba da tallatata a masallaci kana neman kai da ita" dan shiru Baba yayi saikuma chan yace "kinga Rukayya ni ba kira nayi fada dake nayi ba, tun fadanmu na farko bayan rasuwan mahaifiyan yarinyar nan kikaso tafiya da ita nace a'a kika dinga bala'i dani nasan ba kaunata kikeba da akwai yanda zakiyi ma da rabani zakiyi da yarinyar, ni duk wannan ba itace matsalata ba kawaidai kice mata tadawo gida kar fushina yabita" dan sauke ijiyan zuciya Ammi tayi tace "yarinyar nan kawai sabida kaine mahaifinta saisa muka barmaka, wlh na sanar da Baffan ta saidai duk abinda zai faru yafaru, aure na Allah ne ba nakaba, da iyaye ke aurar da yara da tuni kowa yayi, Allah shine komi ke hannunsa, kaida yakamata ka godema Allah dayabaka irin wannan yarinya a'a sai tsalle tsalle kake" katse wayan Baba yayi danshi dama da Ammi basa jituwa kona sakan daya.

Around 8 nadare Hawwa taga Ni'ima na online ta karanta duka messeges nata amman bata kulata ba, watsapp call ta danna mata but harya katse bata dauka ba abin ya bala'in damunta voice note ta danna tace "Ni'imyyyyy sorry please kidena fushi, wlh I know kema na sanar dake abinda yafaru ni da Baba you will not be happy with abinda yayi, banson na tadamiki da hankali koki hanani zuwa wajen Ammi saisa ban sanar dake ba sorry, ina Yass dina da  Meen" ta aika mata voice note din tarike wayan tana kallo ganin yaje but still ba asaurara ba kuma tana online abin yafara damun Hawwa sosai bahaka Ni'ima ke fushi da ita ba saidai tai masifa dukansu basu iya gababa saidai suyi fada ayi zage zage da baki a shirya, dukji tayi ba dadi haka ta tasa wayan agaba tana kallo kusan 20min kuma tana online chan saita sauka ijiye wayan Hawwa tayi ta kwanta kan gadon Ammi tana sauke ijiyan zuciya.

Yau Saturday Baffa (mijin Ammi) na gidan tun goma dayazo baibarta tahuta ba da labarai da surutai dan yana mutuwan son Hawwa, tana yawan turamai kudi akai akai kaman yanda takema Ammi ta, surutunsa yasa tadan manta da damuwanta sai dare kuma tashiga kiran Ni'ima harsaida Ammi talura tace "banji kinyi waya da Ni'ima tunda kikazo ba da tuni tace abani waya tai magana dani, Ni'ima dana sani da saita kawo karinki kin shiga hanya da daddare" dan murmushi Hawwa tayi tace "tana hospital ne Ammi shift take covering, chatting mukafiyi this days Ammi" dan murmushi kawai Ammi tayi bata sake magana ba tace "bari nakaima Baffan ku shayi" tafice.

Washegari Sunday around 11 tafito su Hamza na samata komi a booth, Baffa yace "Hawwa ayi tuki ahankali kinjini" murmushi tayi tace "toh Baffa na" Ammi tace "Allah kiyaye hanya, dan Allah banda gudu" Gyadamata kai Hawwa tayi su Ramla suka rungumeta tamusu sallama tafito, text tama Ni'ima tace "gani nashiga hanya zan dawo office gobe".

Karfe biyu dawani abu anadai neman karfe uku Hawwa ta shigo Abuja hanyan hospital din su Ni'ima tawuce direct ta shiga tai parking ta kashe motan, wayanta tadauka tafito abayane ajikinta baki tawuce ciki office din Ni'ima tawuce tareda knocking tana budewa wata nurse ce aciki tana ganin Hawwa tai murmushi tace "wajen Ni'ima kikezo? Bakuyi wayaba ai batanan yau is her off" amutunce Hawwa tace "okay okay nagode" tajuyo tafito motanta tashiga tafita daga hospital din wlh she's so worried rabon datai magana da Ni'ima tun Friday wani irin fushi Ni'ima keyi da ita haka, hanyar gidansu Ni'ima tayi har zuwa layinsu mai kyau, gaban gidansu ta tsaya tai horn maidaidaicin gidane mai kyau ga babban bakin gate nasu, lekowa mai gadin yayi Hawwa tadanmai murmushi tana jiran taga yabude gate saitaga yabude karamin gate da fara'a kan fuskanshi yace "Hajiya barka da yamma" gyadamai kai tayi tace "ya kuke" yace "Alhamdulillah" saikuma ya tsaya sakaka yana kallonta Hawwa tace "budemin gate ko basanan ne"? Bazai taba iya maimaita abinda Ni'ima tacemai ma hakan yasa dasauri yace "eh basanan tun safe suka fita" danjimm Hawwa tayi kaman daga sama sukaji muryan Yasmeen ta tsandala ihu tana kuka wayyo kafanta dasauri maigadin yakalli gate saikuma yajuyo yasauke kanshi kasa, Hawwa dake juyo muryan yaran tace "kace basanan ba muryan Mims naji na kuka ba" dan sosa kai yayi da hannu kanshi na kasa yakasa kallonta yace "ahhhmm Madam tacemini duk randa nakara barinki kika shiga gidan abakin aikina kiyakuri Hajiya" dasauri da kunya yajuya ya shiga gidan tareda maida gate din yarufe Hawwa tai shiru tana wajen she don't even know wat to think, her mind just went blank wlh takai minti ashirin awajen kafin tadan fuzar da iska taja motan tabar wajen.

GARGADAN SOWhere stories live. Discover now