EPISODE 2️⃣3️⃣
Tana fita ta tsaya ta dauki box ta loda a boot sannan taja motan tana danna waya ta turama DIG message kan bazata iya zuwa aiki gobe ba, tunda dama gobe Friday zataje zaria wajen Sister Mom dinta batada lafiya, baidauki lokaci ba yace permission granted, agidan mai ta tsaya ta cika motanta kawai tafada titi da daddaren nan tayi zaria daga Abuja.
Wasa wasa fa Hawwa ta tafi, da farko Baba ya dauka zai iya daurewa amman ya kasa wayanshi yadaga yashiga neman number Baban Yaseer, da kyar ya gane number yayi dialing, Baban Yaseer na zaune a falo yana aiki da system dinshi Ni'ima na gefenshi tana kallo a Zee world su Yaseer kuma na wasa da IPad dinsu wayanshi yahau ringing kallon wayan yayi ganin Baba yasa yakalli Ni'ima da hankalinta ke tv yace "Baba is calling me wife" dan faduwa gabanta yayi cus ba kasafai Baba ke kiran Aliyu ba, katse wayan yayi yakira Baba da kanshi Baba yadaga yana gaishesa ma bai tsaya ya amsa ba yace "Aliyuu unnn nace ba mutuniyan taku na wajenku ne"? Yana kallon Ni'ima yace "Baba meke faruwa?" Cus baiso yace "eh ko a'a batare dayasan abinda ke faruwa ba" ahankali Ni'ima tace "sa wayan a speaker" wayan yasa a speaker yace "Baba wani abu ya faru ne?" Da dan damuwa kan muryan Baba yace "eh to kusan hakan, daman na sanar da aminina Malam Sama'ila cewa yadan sakamin sanarwa ina nemawa Hawwa miji, kowa yafito yanuna yanaso zan bayar" haderai tamau Baban Yaseer yayi Baba yashiga bada labarin har karshe, hannun Ni'ima har rawa yake ta shiga kiran Hawwa amman bata dagawa, Baba yace "kawai so nake naji inda take hankalina ya kwanta amman dai inhar bata yarda da auren Alhaji Kabiru ba kam saidai tabar gidan nawa tayi zaman kanta" adan fusace Baban Yaseer yace "Baba wai mesa kake haka? Idan kaje ka jefa Hawwa cikin wani hali fa? Ita yarinya ce dazaka mata dolen dole saita auri wanda kakeso Baba, bazaka bata dama ta kawo wanda takeso ba, Baba an gayamaka batada mai sonta ne"? Ranshi ya bala'in bacci harya nuna akan fuskanshi yakalli Ni'ima dake kallonshi still tana dialing number Hawwa yace "did she answer your call wife? I need to know inda take" daga ta dayan bangaren yace "saida safe Baba bata gidanmu zamu gwada kiranta idan mun gano intda take zamu sanar da kai" ya katse wayan ya ijiye laptop yatashi da dan zafi yasa hannu ya karbi wayan Ni'ima yayi dialing number nata da kanshi Ni'ima na kallonshi luckily Hawwa tadauka tace "Best ina driving ne, I know Baba ya kiraki don't tell me anything" dasauri Ni'ima ta tashi takarbi wayan tace "naji I don't want you to tell me anything and nima I will not tell u anything Hawwa, but just tell me kina Ina yanzu naji kina hanya, ina zaki"? Shiru tayi kaman bazatai magana ba tace "wajen Ammi zani a zaria" faduwa sosai gaban Ni'ima yayi tace "Hawwa going to zaria da daddaren nan ke kadai a mota are you okay? Kin manta yanda ake kidnapping ne a hanyan" ahankali Hawwa tace "I will be fine karki damu" cikeda damuwa Ni'ima tace "Hawwa why can't you come to me eh kika kama kik......" key mota dataga Baban Yaseer yadauka yayi kofa yasa dasauri tazare wayan daga kunnenta ta katse tace "Baby ina zaka"? Slippers yashiga sawa yace "zaria" tahowa wajen tayi dasauri tace "zaria this night"? "if anything happens to Hawwa wani abu zai iya samuna!" Yafadi da karfi dayasa chak Ni'ima ta tsaya shima ya tsaya yana kallonta jin abinda yafito daga bakinshi saikuma yadan dafe kanshi yace "just stay with the kids, text me her aunt home address" yana maganan yafice tana tsaye awajen taji ana budemai gate, hannunta da aka rike yasa tai firgigit tajuyo tab dinta Yasmeen tabata tace "Mommy I want to sleep" dan murmushi ta kakalo ta mata ta kalli Yaseer ma tace "okay muje ku kwanta" kama hannunsu tayi tawuce dakinsu dasu bayi ya kaisu sukai fitsari sannan tahau gado dasu tace "addu'an bacci" addu'a sukayi taja bargo ta rufesu tana kashe musu wuta ta rungume su, wasu hot tears taji sunabin kuncinta hannu takai ta share amman sun kasa daina fitowa jin alamun sunyi bacci yasa ta tashi tafito daga dakin tazo falon ta zauna tana kallon system nashi very important aiki yake da Oganshi yasashi yayi yaturomai by 11 na daren nan, gashi yanzu 11 saura, zama tayi tasake fuzar da ijiyan zuciya sannan tadauki wayan nata hannu tasa ta goge fuskanta tass sannan ta shiga turamai address din, kafin tai dialing number Hawwa amman harya katse bata dagaba message ta shiga ta turamata. "Be safe Hawwa, I'm worried about you, Allah tsare hanya" kusan 2min saiga reply na Hawwa tace "I know you are worried, don't be nakai zan kiraki, love you Best" love you best din takalla sai taji wasu hawaye masu zafi sun sake zubomata tashi kawai tayi tafada dakinta iPad dinshi dake saman drawer side nashi na bed ta kalla yawanci yana daukanshi da daddare yadanyi karence karance, samin kanta tayi da dauka, hoton family portrait nasune ne as wall paper, tadade tana kallon Baban Yaseer a hoton sannan tai kokarin duba wayan taga password shiru tayi tana tunani sai kawai tasaka birthday na su Yaseer taga yabude tashiga cikin wayan, tana dube dube chan ta shiga gallery wayan, hotunan Hawwa taci karo dasu a gallery, dasauri ta shiga ciki hotunan duka na wayanta ne wanda ko Hawwa batadasu dan ita ke snapping nata, tun hotunan su na primary and secondary school, da hotunan datake mata occasionally, da hotuna datama Hawwa adakinta tana sanye da rigan bacci mai kyau ga boobs nata da sukai showing dasauri takai hannu tai deleting wannan, saikuma hotunan datagani wayanda Hawwa nafitowa daga gidansu da hotunanta in different places kaman stalking dinta ma yake yana bibiyanta batare data sani bama ita Hawwan, ganin zuciyanta zai buga yasa tashiga marking pictures din tai deleting everything ta maida iPad din ta ijiye tana sauke ijiyan zuciya saikuma tafashe da kuka sosai na tausayin kanta.
Sosai Hawwa ke gudu akan titi da daddaren nan zuciyanta gabaki daya yazo mata wuya, bini bini take goge hawaye, she can't even explain d kind of pain datake ciki today has been a bad day for her, daidai ta shigo kaduna around 12 tayanta ya faci gangarawa gefen hanya tayi kawai tai parking tadaura hannayenta asaman fuskanta tafashe da kuka sosai tace "Ya Allah maisa ban sami mijiba? Nayi imani da kaddara mai kyau da mara kyau, I accept whatever you choose for me Ya Allah, ina salla, ina azumi, ina nafilfilu, ina karatun Al Qur'ani, bantaba fasikanci ba, bantaba shan giya ko wani abu na maye ba, inama iyayena biyayi, ina taimakon mutane, daidai gwargwado ina bautamaka Allah" cikin murya mai rauni sosai tace "Ya Allah kaji tausayina kaji Ya Allah, Ya Allah kabani mijina nima, Ya Allah ka kawomin mijina nima, Ya Allah ka aurar dani da gaggawa banson yanda hankalin Babana yake atashe sabida ni, nazaman mishi abin kunya, dani ake kwatancen shi, Ya Allah ka tausaya mini kaji" tafashe da kuka sosai she missed mamanta she missed her, kusan 1hr ita kadai a motan nan babu tsoro ko fargaba aranta koma yatakama takama din kawai, idanunta a lumshe bawai bacci takeba but jikinta duk ya saki taji ana bubbuga marfin motanta "Hawwa Hawwa, Hawwa talk to me, Hawwa" kaman ana kiranta daga nesa hakan yasa tadan bude idanunta kadan, ganin hasken flash na haskota yasa gently tajuyo da rinannun idanunta ta kallo glass na motan shima ganin haka yasa Baban Yaseer ya haska mata fuskanshi sabida taga shine, wani irin kafeshi da idanu Hawwa tayi batun yauba taga soyayyanta a idanun Baban Yaseer but koda mistake bata taba saran zamata bashi chance ba saisa bata cika zuwa gidansu ba saidai ta sami kawarta awajen aiki kosuyi outing tare, She will never ever betray her friend koda baban Yaseer ne d last man aduniya, but yau for the first time ganinshi cikin tsakiyan daren nan yazo yabi wannan hanyan tundaga Abuja yazo nemanta bayan he came to her rescue earlier today yasa ta tsareshi da idanu tana tambayan zuciyanta could Baban Yaseer be the man she just finished asking God for? Is Allah testing her? Mijin best friend dinta? She rather hakura da auren gabaki daya aduniya tayi alahira, sosai take kallonshi hankalinshi amugun tashe yake buga kofan ganin yanda take kallonshi yana Hawwa open, kusan 2min tadauka tana kallonshi kafin gently ta danna lock motan yayi unlocking kanshi yabude motan da sauri yaduko yana kawo fuskanshi daidai nata cikeda tsantsan so da kulawa da damuwa yace "Hauwa'u! Are you okay?" Tsare shi da idanu tayi sai kawai hawaye ya gangaro daga idanunta dasauri yashiga ciro handky daga aljihunshi jikinsa har rawa yake yace "don't cry and don't be afraid I'm right here, Aliyu is here".
YOU ARE READING
GARGADAN SO
RomanceStory of a police woman in her 30s da maza sukaki aure sabida they feel intimated by her career🔥😂 READ AND ENJOY