BABI NA DAYA

7.1K 313 10
                                    

🚽HANJIN JIMINA...akwai naci akwai na zubarwa.

  Billy Galadanchi

Haske writer's Asso💡 ( home of expert & perfect writer's)

Bismillahirahmanir raheem,ina rokon Allah yabani ikon rubuta Alkhairi ya kuma sanya ku amfana da abinda zan rubuta,Allah ya kareni daga sharrin maheranta yakuma sanya na gama da iyayena da duniya lapia Ameen...

Kaunar ku agareni me yawan gaske ce amintattun haske Allah ya kara hade kawunanmu ya dauke idon maqiya akan mu.

  Wannan littafin sadaukarwa ne ga kawata Hafsat ilham.
    01

Tafiya takeyi tana faman had'a gumi iya gajiya ta gaji,tafiya tun daga agege har owodé tafiya ce me nisan gaske sabida fitane daga ckin garin lagos zuwa wani country na daban,btada kdin hawa brt tun daga agege har zuwa can,gashi tafiyar ta zame mata dole dakyar taga ta isa,tun asba ta fito daga gida amma sai karfe daya saura ta isa wurin,batare da bata lokaciba ta bude bakin buhun da tazo dashi tashiga tattare shinkafar da masu durawa a buhuhuwa ke zubar wa awurin yayin aunawa,tafi awa biyu tana tatre wa,ba laipi ta tara yafi kwano goma kasancewar ba wani wanda ya damu da wacce ta zube din kowa aikinsa yake,kwara babbiyar nokia torch light dinta ta janyo daga cikin zani tga har uku ta gota,wannnan ya sanya ta dakata tayi salah sannn taci gaba,ganin hudu ta gota yasanya tayi hanyar gida,bus tafara hawa ta sauketa wani station sanan ta hau brt ta sauketa a agege inda ta hau adaidaita zuwa zango...da salama ta shiga gidan nasu ba kowa a tsakar gidan nasu tamkar anyi shara,kai tsaye daki ta wuce ta tarar mahaifiyar ta nata kwasar kuka,da sauri ta karasa inda take ta durkusa murya na rawa ta furta

"Umma lapia me kuma ya sameki haka?" Dagowa tai ta kalli yar sannan tace

"Amal  Auwal ne shine yazo" zaro ido tayi waje ta dafe girji tace cikeda fargaba
"Kaddai wani abin ya aikata agareki Ummie?" Gyaran zamanta tayi tace cikeda d'acin rai
"Amal yamun komai ma,Auwal so yake ya kasheni ya huta sam wannan yaron bashida kirki,kaf abincin dake gidannan ya gama tattarashi ya gudu,a haka jawaheer tafice tana kukan yunwa banmasan inda ta nufa ba" dafe kai Amal tayi cikeda k'unan rai tace "Subhanallah oh ni Aisha se yaushe Auwal zeyi hankali ne wai? Kiyi hakuri Ummie bara nayi sallah nazo na gyara wannan shinkafar tunda da kasa aciki inyaso nakai gidan iyan hadi su siya se nayi cefane muci abinci  tunda inaga yafi kwano goma wannan" kwanciya Ummie tayi tana me sakawa Amal Albarka yarinyar gwanin ban tausayi akwai kokari mace sekace namiji tana mata fatan Alkhairi.. A wahalce ta mike taje ta dauro alwalan la'asar ta gabatar sannan tafara aikin ta....

  Da azama kameel ya shigo gidansa iya yunwa ya kwaso yunwa,yana shigowa parlor ya tarar tana kwance Ameer yayi kashi a saman tile se jagwalgwalashi yakeyi tana zaune tana shan rake abinta tana kundu ma masa zagi

"Tsinannen yaro me shegen kazantar tsiya ka rasa inda zaka mun kashi se'a parlor wlhy sena kammala shan rake na sannan zan kulaka ka karasa kazantar taka" to she hanci kameel yayi cikeda bacin rai yace
"Haba Hauwa wannan wane irin mugun kazantane haka,gida se wari yake yaro yayi kashi kin zauna kina faman shan rake" mikewa tayi ta gyara daurin zanin atamfarta wanda asaman bingilalliyar vest dinta ta dora shi tace tana Sosa kunne

"Kaga kameel ni karkaga laifina fa Ameer shine sarkin kazanta,banda iskanci yaro yasan yace zesha ruwa,Umma tee zansha,Amun wanka amma ya zauna ya tiqa mun kashi a kasa sannan kace laifina zaka gani?" Tsaki yaji cikeda kosawa yace

"Yaronnan fa Hauwa ko wando baki saka mishi ba,ga uban sanyi ana kwad'awa amma kibarshi tsirara ko kunya bakyaji" tsaki taja ta dauke yaron kurun tayi ciki dashi tsabar haushi kasa karasawa ciki yayi ya juya abinshi zuwa gidan maryama,besha wahalar shigaba kasancewar me gadin yasan da zamansa tun a kofar parlor din wani dadda dan kamshi ya tarbeshi,lumshe ido yayi ya sauke ajiyar zuciya sannan ya cira hannu cikeda kasala yai knocking,bude masa kofar maryama tayi a lokaci daya ta rungumoshi ya fado jikinta,Sumba ta manna masa a wuya sannan cikeda shauqi ta kirsa tace

"My kameel kamar kasa ina wanka ina tunanin ka jiya bakazominba dukna damu" kura mata ido yayi ba komai ajikinta se towel wanka tafito jikinta duk ruwa,amma se tashin kamshi takeyi tamkar wacce tayi wanka da shagon turaruka,kurawa fuskarta ido yayi cikeda kauna,gashin girarta yacika da  ruwa ya kwanta lufluf ba karamin kwanciya gashin yayi ba kuma ya mar kyau matuka,janyota yakumayi jikinshi ya  saka harshe ya lashe mata ruwan na duka giran biyu yace

"So much miss yhu Deena na,Kinyi kyau se tashin kamshi kike,gidanma sekace kamfanin sarrafa tuararuka" Murmushi tayi tace dashi tana tafiya tana jujjuya duwawuka "My honey bara nasaka kaya nabaka abinci I'm sure kanajin yunwa" wuri ya nema ya zauna a daya daga kujerun parlor din har takai kofar dazata sadata da walkway dashima ze leading nata zuwa dakin ta juyo a shagwabe tace

"Honey ni bazaka tayani saka kayan ba?" Murmushi yayi ya mike ya karaso kusa da ita dagata yayi gaba daya yana fadar "Baby dee mezai hana nashirya abata" wani narkewa tayi a jikinshi tace "Honey kona tayaka wankane mu shirya dukkanmu" direta yayi yace "sure mana baby dee ragemun kayan nauyinnan" matsawa tayi daf dashi ta Shiga balle botiran rigarsa cikeda shagwaba da salo irinna  bariki,ahaka tamai zigidir itama kuma ta cillar da towel na jikinta da fada jikinshi sungumarta yayi ya direta a cikin ruwan me kanshin da ke cikeda bahon wankan shima ya fada aciki...wal iyazu billah Allah ya shiryi zuri'a.

    Kallon Mansoor Amal tayi tace dashi "Mansoor kana ganin lokacin dazamuyi auren yayi dududu fa watanin mu hudu da haduwa,ina ma mukayi zaman da muka fahimci juna da har zamu fara zancen aure?" Kallonta yayi damuwa dauke a fuskar sa yace
"Haba my Amal? Tayaya zancen aure yashafi watanni nawa mukayi atare fata daya ne munasan junan mu" langwabar da kanta tayi sannan cikeda shagwaba daya zame mata dabi'a tace

"To ai ni banasan rabuwa da Ummie na da khairiyyah kuma kace wai Kano zaka ajiyeni" rike hannunta yayi  yace "zan kular miki dasu my Amal,kisani bayanda zanyi ne daba yanda za'ayi nayi nesa dake,kumama daddy yace zai mayarda ni kampaninsa dake Kano so kinga bata yanda za'ayi na ajiyeki anan"  Murmushi tamasa cikin dabara ta zare hannunta domin sam batasan yake tabata kuma ta kula hakan d'abi'a ce agareshi

"Ba damuwa yaa Mansoor Allah ya sanya shine mafi Alkhairi zanwa Ummie maganar inyaso tasanarwa da baba gambo sena maka waya" block compartment nashi ya bude ya janyo wata waya kirar tecno cs ya mika mata,kin karba tayi ta tsaya kallonshi sanda ya daura kan cinyarta "yaa Mansoor me haka kuma"
"Waya na siya miki mana kalli Nokia dinki Amal duk roba aiba girma na bane Matana na rike wannan wayar" langwabe kai tayi kamar zatayi kuka tace "amma yaa Mansur abin beyi yawaba kalli fa dawainiyar daka gama dani yanzu" lakuce mata hanci yayi

"Kinga malama Bafa ruwanki da abinda nayiwa Matana ehee" Murmushi tayi me sanyi

"Allah ya saka da Alkhairi yaa Mansur Allah kuma yabar kauna"....har ran Amal tana kaunar Mansoor tarasa dalilin daya sanya wasu lokutan takan ji faduwar gaba duk sanda ta tuna da zancen auren su.

  Sosai kameel da Deena suka barje ayarsu a gidan Deena,sai wuraren karfe goma na dare yayi shirin tafiya gida,har sunzo kofa  ta wani narke " Honey wai yanzu zaka tafi bazaka kwanamun ba" Sumba yafara manna mata yace "kiyi hakuri my Deena gobe zanzo kinji" kuka tasaka dakyar yalallab'ata ya tafi....Koda yazo gidanshi Hauwa na zaune a parlor tana cin farfesun kazarta me karnin gaske kota damu da ficewarsa dayayi dazu ce cewa tayi dashi

"Kameel dazu kanna fito wanke wa Ameer kashi harka juya,nace wata sabga ta samu kenan" Kallonta yayi da muguwar shigarta kitson kanta yafi one month yace "E" a takaice ya shige abinshi.

Mom nuaiym

Hanjin Jimina...akwai Naci Akwai Na ZubarwaWhere stories live. Discover now