BABI NASHA UKU

1.9K 154 2
                                    

🤡HANJIN JIMINA.. Akwai naci akwai na zubarwa🤡

     Billy Galadanchi

HASKE WRITER'S ASSO. (Home of expert & perfect writer's).

Vote me on wattpad@68billygaladanchi.

Sadaukarwa ga Aminiyata Hafsat Ilham.

                    13
*Bayan watanni biyu*

     Mansur ya Shiga cikin tsaka me wuya,domin kuwa yar tsito sam bata barinsa ya huta,kullum abu daya yakeyi awanni goma sha takwas dake cikin awowi ashirin da hudu da muke dasu a rana,yayi baki ya rame,kai baka ganshi kace shi bane,sannan kuma ta daure masa baki sam duk yanda yafita yaso yaga yawa wani seyaji bakinsa ya masa nauyi ya kasa,hankalin mahaifinsa ya tashi amma duk sanda ya tambayeshi seyace ba komai da haka daddyn yaje wurin dodon tsafi....

"Mansoor ya janyowa kanshi masifa ba abinda zan iyayi masa yanzu,ni kaina wannan tarawar danayi da yarinyar Aljana yar tsito ta fusata dani takuma sanar dani seta dauki fansa akanmu,shine ta fara akan Mansur kuma yaronka yana shan wahala sosai yaje ya nemi yafi yarta shikadaine abinda zance" yana gama fadar haka ya bacewa ganin daddy,jiki na rawa yabar jejin zuwa gida,kai tsaye gidan mirror dake Jan bulo ya yaje ,besha wahala ba sabida me gadin yasanshi shida kanshi ma ya nemoshi,a parlor ya tadda Mansur yanata kuka kai,sanar masa yayi cewar yaje wurin dodon makuba ya sanar masa menene damuwar,kasa fada yayi dakyar mahaifin Nasa yashawo kanshi yamasa bayanin komai da komai,gidimewa yayi yafara neman mafita koda mahaifin sa yabar gidan Sega yar tsito ta bayyana agareshi
Tace cikeda razananniyar murya
"Kayi kuskuren sanar da mahaifin ka wannan maganar, zan azabtar dakai azaba mafi muni,zan baka wahalar dabazaka iya dauka ba,zan tozartar dakai tozartarwa mafi zubar da mutunci,zan mayar dakai me suturu a tsirara" kan yace wani abu ta bacewa ganinshi,ga mamakin shi ranar be fitaba amma sam bata zo masa ba amma  beji azabar dayakeji ba idan lokacin kusantarta yayi beyiba,har washe gari shiru,da wanan ya shirya yafita,shago ya fara zuwa domin siyan ruwa da drinks na gidanshi sun kare amma ga mamakinshi mutane se kallonshi sukeyi suna kwasar dariya,sannan  mata sesu rika rufe idonsu duk inda ya dosa sesu watse,kanshi fa ba karamin daurewa yayiba,da wannan ya nufi gidansu yana mamakin meya sanya mutane ke masa dariya mata kuma na gudu,har wani yaji yana cewa "Allah sarki inaga wanan sabon kamu ne,Allah ya bashi lapiya" mamakin kalaman mutumin ne suka kara rikitar dashi,koda ya isa gidansu matan dake musu aiki yaga sun kwasa aguje suna kauda fuskarsu yayinda me gadin gidan tun a gate yake kallon sa baki a sake yau ko gaidashi beyiba, mahaifiyar Deenah yafara cin karo da ita babban parlor itama din kallo daya ta masa ta kwasa aguje ba shiri hakafa acikin gidan ko ina yaje se kowa ya watse har mahaifiyar sa gashi daddyn sa baya nan,a haka yabar gidan cikeda alhinin abinda yasanya ake gudunshi,shawara yayi na zuwa gidansu abakin shi bashir inda tun a gate me gadin ya eba a 360 yana waigowa cikeda tsoro,wasa wasa fa kowa yaga Mansur seya gudu,aikuwa gidanshi ya koma yanata faman kuka na sosai da sosai.....

   Khairiyyah zaune itada kameel a gidan Adda Amal suna hira ya kalleta yace

"Wainikam my khairiyyah jegonne har yanzu ina kusan watanni nki biyu da aihuwa amma kin kama kinqi sakin jiki dani muyi zancen aurennan daga zaran na dakko maganar seki kauce nifa sosai na fahimceki bakya sona" kura masa ido tayi cikeda kauna har ranta takeji tsananin kaunar kameel tace cikin sanyi

"Yaa kameel bawai bana sanka bane Wlhy ko kadan abinda kake tunani baikai canba,kawai dai me kazanta irina bata cancanci zama matar tsaftataccen mutum irin kaba,bata yanda za'ayi na gauraya tsaftacciyar rayuwarka da tawa me cike da tarin kazanta da tulin abin kunya,kana fa sane Kaine kadai na sanarwa wulakancin da Mansur da yan kungiyar asirinsu sukamin,dan Allah yaa kameel Kayi hakuri da zancen aurennan" rike hannayenta yayi duka biyu yace

"Haba mana khairiyyah, kisani ni awurina kin ma fini tsafta kinfi ni cancanta khairiyyah, bakya ganin dukkanin abinda yafaru dake bada San ranki bane,nikuwa fa? Ina sane nake sabon  ubangijina da gangan,ki yarda dani haduwar mu khaddarace kuma ta Alkhairi kasancewar ke dinnan kece silar shiryuwana na har abada,jar naji kokuma naga kin fadawa wani wannan maganar tamu data faru dake wannan dakike gani sirri ne tsakanin miji da matarsa" da haka dai ta amince masa akan zancen auren

Jawaheer na zaune agaban motar Hilal tana ta faman kuka ido duk ya wani mata jajir se rarrashinta yake yi taqi ta hakura yace

"Haba blacky ke kincika rakin tsiya wlhy,tayaya ma za'ayi sabida ciwon hakwara ki zauna kina mana ihu na sanar miki ki bari kurun acireshi yafiye miki sauki" maqe kafada tayi cikeda shagwaba

"Allah ni dai bazan yadda acire mun haure naba baka ganin sanda Mamana bata rasu ba damuke labari ta sanarmun nasha wahalar kashin hakori da amai da zazzabi,idan fa haure d'aya ze fito sena fi wata ina ciwo,shine yanzu tsabar mugunta abinda nasha wahala kanna samu zaka wani ce nacire Allah ni dai karabu dani d'an biyuty" dariya sosai yayi dajin wannan kuru ciyar ta juju harta fusata tafara wani kukan dakyar ya rarrasheta akan ze siya mata abin dadi.

   Shirin sosai daddy yayi yaje Lagos wurin kanin mahaifin su Amal baba gambo akan zancen auren yaran,inda atake aka  badasu sabida dama Auwal yaje ya bincika komai da komai,daddynsu su Hilal beyi kasa a gwiwaba wurin nemawa kanshi auren Amal,inda baba gambo tsabar kwadayi batare da wani tunani ba yace yabashi auren Amal!!!!!tirkashi

Daddy ne zaune a parlor shida su Hilal da mahaifi yarsu bayan ya dawo daga tafiyar dayayi zuwa lagos,gyaran zamanshi yayi sannan yayi gyaran murya yace

"Ina mai farin cikin shaida muku cewar anbaku auren yaran,sannan kuma zan sanar muku wata magana sedai inaso ku kalli maganr tawa da idon Basira wlhy bawani abin yasanya na aikata hakanba sedon tausayawa yarannan,dafarko dai ke Haj Salaha kezan bawa hakuri,kuma nasanki macece me fahimta inaso ki fahimci manufata ta Alkhairi, Bayan naga yayarsu jawaheer se tausayinta ya kamani ganin gata da yaro karami amma tsautsayi ya afka mata,wannan dalilin ne yasanya nayi sha'awar kyauta ta mata,yasanya danaje Lagos bayan na nemawa yarannan auren kaninta nikuma sena nemawa kaina auren ita Amal d'in" atare suka mike dukkansu uku suka kuma kurawa daddy ido,Haj Mamie kam murya na rawa na soma hauka tana yarfo ashar

"Kan abun ubancan wlhy Alhj idan ka isa nidin shegiyace Wato wayannan yaran da gayya suka shigo domin su mallake Yaya na da mijina,wlhy ba Amal har kannenta anfasa aurensu kuma ko bayan raina ban yadda ku auri wayannan mayun ba dangin matsafa,wlhy Alhj Kayi kadan,muna fukai suma suna sane suka nanike mama tsintacciyar mage,

Shiyasa ranar naga kana nacin kallon ta sekace wani maye,idan kun isa Allah ya tsinen" dakyar yayanta suka zaunar da ita suna lallai da ban baki...

Deena kam shiryawa tayita koma gidansu azuwan Jordan datake karatu sunyi withdrawing nata sabida bata karatu,inda mamanta tayita masifa akan hakan.

   sosai Amal ta rikice akan zancen da Hilal ya sanar mata,kuka Sosa takeyi,ahaka tace zataje Lagos wurin baba gambo.

Mom Nuaiym

Hanjin Jimina...akwai Naci Akwai Na ZubarwaWhere stories live. Discover now