BABI NASHA SHIDA

1.9K 142 1
                                    

🤡HANJIN JIMINA.. Akwai naci akwai na zubarwa🤡

Billy Galadanchi

HASKE WRITER'S ASSO. (Home of expert & perfect writer's).

Vote me on wattpad@68billygaladanchi.

Sadaukarwa ga Aminiyata Hafsat Ilham.

16
Ana haka wayarshi ta soma ringing a daddafe ya daga wayar batar daya San me kiranshi ba,koda ya kara a kunneshi yaji muryar mahaifi Barshi

"Momy ce ki taimakeni momy gani ni kadai agidana,wlhy sam bana gani duhu nake gani komai ya dauke mun" cike da rashin fahimta tace

"Ka nutsu Baba na sanar dani me kake nufi da baka gani" Momy ki taimakeni Kizo gidana yanzu wlhy daddy ya cuceni ya gama da rayuwata ya wulakanta ni ya kaini ya baro da kuruciya ta" dafe kanta tayi ba tun Yauba take zargin me gidan nata da wasu halayen marasa kyau wanda ta barwa cikinta tun a mutuwar da y'ay'an ta naba gaira ba dalili ga aure mata suyita mutuwa da ciki,cike da dakiya tace "Babana zanzo yanzu karka damu kaji komai zezo maka da sauki da yardar Allah" haka ta kashe wayar takira yayanshi mukhtar a waya suka je gidan sunsha mamakin ganin yanda idon Mansur bakin tsakiya ya dawo fari fat duk ya fada ya rame ya lalace,kuka momy ta saka tace

"Babana menene ya sameka haka ban saniba,dan Allah sanar dani wane irin cutarwa kake cewa mahaifinku ya maka,karkaji tsoro kuma karka boye mana dukkanin abinda ya faru" Mansur kuka yakeyi har da majina yace

"Momy Karkiyi kuka duk abinda ya sameni Nina jawa kaina sabida kwadayin abin duniya,idan bazaki manta Ba,bancin yaya mukhtar kin haifi yara biyu duka maza kafinni,kuma kin sani nemansu akayi aka rasa bayan sun tasa,to hakanne Nima wani yammaci na dawo daga jami'a lokacin ina aji uku a jami'a sena hadu da Daddy a walkway na shigo wa gidannan,rike hannuna yayi yace

" Mansur kaci abincin kuwa? Kallon mamaki na masa sabida be saba mun irin wannan tambayar ba beside lokacin yashigo gidan yace "Noo daddy I haven't eating since morning, I just came back from skul" hannuna yaja yace zomuje ka rakani wani wurin me muhimmanci zan baka abinci a can..." Ban kawo komai araina ba na bi bayanshi muna shiga mota ya mikamun fanta na can yace nasha kan muje inda zamu,tunda nasha ban kara sanin me ake cikiba se budar ido na nayi naganni zagaye da mutane sun saka kaya baqi daja suna surutai akaina suna kurbar wani abu kaman jini a kwarya.....murza idona nayi ganin daddy acikinsu abin yamun tamkar mafarki nake,daddy yace dani

"Mansur ka gafarceni zan nemi duniya da jininka,zan bayarda kayan cikinka abaiwa me bani dukiya yasha farfesu Kayi hakuri kaji" zumbur na mike jin wannan maganar da daddy yayi nace murya na rawa

"Daddy mena yi maka zaka kashe ni dan Allah karkamun haka" Wata dariya naga daddy yayi yace

"Mansur ai acikin Yaya na duka mukhtar ne kadai bazan iya badawa,Kaine na goma sha hudu,gani da dukiya zan zauna talauci ya kashe ni,karkayi tunanin nafi sanka dasu na bada mahaifiyata da kanwata da kuma mijin ta balantana kuma kai kana d'ana d'an ma baka kadai bane,da daddai da daddai zan rika daukarku ina bayarwa ana shan jininku ina samun duniya bazan taba lamun cewa talauci ba,sabida banida kudi ba wulakancin daban shaba awurin yan uwana da dangi na har makaranta aka saka kowa nikuwa dakyar na hada secondary da tsufana naje jami'a ka taimakamun mana Mansur,daga kai saura mutane biyar da jini na ke yawo ajikinsu dazan bayar kaga kuwa saura kadan,abin Banso yakai canba amma dolene sabida a kungiya banida Magaji ko magajiya" zabura nayi zan gudu suka dam koni,dodon tsafinsu yazo saka wuka ya yanki hannuna kadan yabi ya lashi jinin yace

"Wannan dazakayi Magaji dashi dazaka more halinka nasan duniya kaf gareshi kuma ga alama ze kawo dukiya dakuma ci gaban al'umma" ihu na saka nace

"Bazan taba zama dan kisan kai ba wlhy,sedai ku kasheni,bani ba wannan aikin,daddy Allah ya tsine maka albarka wlhy sekayi mutuwar wulakanci" mari ya wanke ni dashi yace daya sanya naga fararen taurari yace

"Ai sabida banida bukatar tozar tarwarku ya sanya nece zan badaku in yi kudi,kuma sekasha azaba tunda kake mun fi'ili,dodo a nuna masa yanda kake dawowa idan anyi garkuwa da jininka.....giri riri aka jashi,awurin da aka kaishi yaga abin al'a jabi,gawarwakine ke fitar da kudi ta sassa daban daban na jikinsu,sosai na tsorata hadda yayyuna guda biyu aciki,da kannen bila adadin ganin haka fa na gigice,nace idan zasu barni da raina nida yan uwana zan shiga kungiyar Nima,daddy yace wlhy mahaifiyata ze saka akawo a yankata agabana,anan na kara diriircewa na shiga ban baki,harga Allah momy kaddara ce ta afka dani a sanda nace dasu na yarda zan shiga nayi hakane kurun saboda nasamu kubuta Na manna su hannun hukuma har daddyn,Abin takaicin shine wanna cewar danayi zan Shiga domin kuwa shine silar sauyawar rayuwata,daga nan daddy ya Shiva murna,aka dauko jini akace sai nasha naqi haka suka matse ni tamau suka tuttulamun daga nan aka Hau bori akaina ana sambatu nanfa komai ya kwancemun aka zomun da wani nau'in abincin da bazan iya fassara wane iri bane aka dura mun,haka fa na dage tun daga wannan lokacin na nemi tausayi da tsoron Allah na rasa,kuma su ka dauko tsabaran kudi Billion daya suka bani, suka xanna rika samun linkin ba linkin duk ranar duniya idan zan basu hadin kai, haka na biyewa tunanin su da umarnin su,wannan lokacin ne suka bukaci jinina banida d'a bani da jika Dole suka karamun lokaci nayi auren gaggawa dakika San nayi ba shiri fa abubuwa suka canja mun ahaka na dauki matar da d'an na bayar har dangin tama Dukkansu bayan nan kuma suka mallakamun dukiya a yanzu haka danike muku zancrnnan na daina kai kudade na bank kuma basa bari ayi sadaka ke kanki shaida dace bana kyautar kudi,sabida gudun zargi na fara aikin gwamnati wanda dashine nake kyautar kudi domin nasu ba'a sadaka dashi,momy ahaka har sallah suka saka banayi duk jumu'a Nashiga tsaka ko su Amal danace dake sunmin sata sun gudu karya nake musu nine nan na cutar dasu......take ya kwashe komai ya sanar mata har kawo yau dinnan, har zancen deena be rage komaiba kuka me tsanani ta saka tafara sambatu tana yarfawa mijinta ashar da tsinuwa,dakyar suka shawo kanta tayi shiru daga nan ta kwasheshi zuwa gida.
....

Khairiyyah idan hankalinta yayi dubu tofa ya tashi domin a ganinta sam bata kyautaba gani zeyi tamkar tana Goran ta masa abinda tasani game dashi ne,wayarta ta daga tayi kiranshi amma qin dagawa yayi,koda gari ya waye sukuku take Amal ce ta kalleta sosai

"Khairin Umma wai lapia Naganki wani iri kuwa??" Dan murmushin yake tayi tace "Ba damuwan komai Adda Amal kawai dai inajin kamar kaina yana danmun ciwo" cikeda tausayi Amal tace

"Ko Zakije asibiti ne wannan ciwon kan ya sakoki a gaba wlhy" kan tayi magana se sallamar Kameel sukaji zumbur ta mike yayinda Amal tabar parlor din bayan sun gaisa,sosai khairiyyah taji sanyi ganin kameel,kurawa kyakyawar fuskarta ido yayi yana sakar mata wani lallausan Murmushi wanda yake wanzar mata da sakonni Masu yawa,matsowa tayi daf dashi tace "Yaa kameel dan Allah Kayi hakuri wlhy yarda dani bada wani manufa nayi maganar ba subutar baki ne da kishi bazan iya jurewa fushinnan dakake daniba zuciyana fashewa zeyi" hannayenta duka biyu ya hade wuri daya yace

"Dakin San wahalar danasha rashin jin muryanki na kwana d'aya kurun dakin tabbatarwa kanki cewar kaina na azabtar bake ba,dan Allah ki kula inada saurin fushi kidena batan rai akai akai kinji" langwabe kai tayi cikeda shagwaba ta dakar masa kirji cikeda kuruciya

" Allah nice na wahala yaa kameel bazan ma ci abinci ba yau" dariya ya kwashe da ita suna haka Sega Hauwa ta fado tamkar wata zautacvi

"Kar Allah yasa Kici abinci Banza munafuka dangin mayu" kan wani yayi yunkurin harta janyo speaker daya ta makawa khairiyyah akai sosai ta gigice kameel na riketa tana warcewa duk abinda ta samo kwala mata kurun takeyi seda su Amal suka ji hayaniya suka kawo dauki sosai taji jiki jini se fita yake ta goshinta,Hauwa kuwa bata bar yanko musu Ashar ba tana surfa ihu......

Mom Nuaiym

Hanjin Jimina...akwai Naci Akwai Na ZubarwaWhere stories live. Discover now