BABI NA SHA DAYA

2.2K 143 2
                                    

🤡HANJIN JIMINA.. Akwai naci akwai na zubarwa🤡

Billy Galadanchi

HASKE WRITER'S ASSO. (Home of expert & perfect writer's).

Vote me on wattpad@68billygaladanchi.

Sadaukarwa ga Aminiyata Hafsat Ilham.

*Wannan shafin nakine Aunty Bilky @ Khadeeja candy novels group, tnx alot for loving me and this book I heart you irin totally dinnan*

11

Ba tare da bata lokaciba suka wuce da Hilal asibiti, cikeda gaggawa aka karbeshi a Trauma Emergency,ba wani hope akan Hilal kasancewar harbi biyu ne,dayan a gefen mararsa dayan kuma a kafada,na gefen mararsa shikeda babbar matsala,kai tsaye ICU aka kaishi bama kowa ke Shiga wurin ba,anyi nasarar shire harsashen duka biyu kawai dai chances na survival are very low.... A bangaren yaran Mansur kuwa da kyar daya daga cikinsu yayi confessing after so much torture,amma abin mamakin shine annemi Mansur sama da kasa ba'a ganshi ba yabar kasar ma gaba daya ga alama.....

Kukan sosai Jawaheer keyi kuma ba karamin tsorata tayi da wannan ciwon dake damun Hilal ba,musammm dataji kameel na sanarwa mahaifinsu komai kuma taji a media ana fadar cewan kashi ashirin ne kawai na tashi nsa acikin dari....ta kudirta aranta muddin inhar Hilal ya mutu itama seta kashe Mansur sedai itama a kasheta,da kanta ta roka mahaifiyar sa itace ke jinyarsa.

Bayan kwanaki goma sha biyar

Har zuwa wannan lokacin Hilal be motsa ba,Jawaheer kuwa kullum cikin kuka take hankalin ta atashe yake,gani take tamkar asanadin su ne ze rasa rayuwar sa,hankalinta idan yayi dubu toko ya tashi....yauma kamar kullum rike take da hannunsa tana rera uban kuka,tana fadar duk wata adua datasan ta samun sauki ce ga mara lapia,Hannunshi datake rike dashi taji ya hade da nashi sosai a hankali ta sassauta sautin kukanta ta dago kai ta kalleshi ya bude lumsassun idonshi ya sakar mata wani kayataccen Murmushi seda kumatunsa duka biyu suka lob'a tana hawaye itama ta washe baki,sake hannun shi tayi da sauri ta dubi gabas tayi sujjada sannan ta dago ta kalleshi shima din ita yake kallo,da sauri taje gareshi batasan sanda ta rungume shi ba tace murya na rawa "sannu my Hilal inane yake maka ciwo yanzu? Me kakeso ? Zakaci abinci ko ruwa zaka sha?" Murmushi yakuma yi mata yace "I'm all fine my princes sanar dani meya faru dani ?" Kallonshi tayi

"That's really not necessary now, lemme rush and call the doctor" be Musa ba ta juya da sauri zuwa kiran doctors din....Alhamdulillah dama farfadowarsa shike nuna samun nasarar aikin,kuma shakka babu yaji sauki ko wounds nashi sun fara healing nanda kwanaki kalilan akace zasuyi discharge nasu,Jawaheer kuwa washe gari tafara azumi dama tayi wa kanta alkawarin yin azumi goma na godiya wa Allah idan yasamu lapia...... Ahaka dai har Hilal ya mike ya zamto mutum me koshin lapia inda gizo ke sakr kuwa shine har yau ko labarin mansur babu shi wanda sam hankalin kowa be kwanta da rashin sanin we're about nashi.

Zuwa yanzu watannin cikin khairiyyah bakwai da kusan sati biyu, duk ta canja kullum suna tare itada kameel sosai ta saba dashi hankalinta ma baya kwanciya idan be zoba,yauma tun safe bezo gidan nasu ba har wuraren karfe 8-30 be zoba wanda duk sanda yakai irin wannan time din kowa yasan ba zuwa zeyiba...Mamie ce ta kalleta tayi jigum ta rafka uban tagumi,yarinyar na burgeta sam bata da hayaniya a daya bangaren kuwa tana masifar jin tausayin halin da baiwar Allah ke ciki ga kuruciya zuwa yanzu ta gane dan nata nasan khairiyyah kuma ta saka aranta idan har yace ze aureta bazata hana shiba, a hankali cikeda tsokana tace

"Khairiyyah Mamie menene bana hanaki wannan tunanin ba,sanar dani me kike tunani haka" dan Murmushi tasaki sannan tace "Mamie Allah ba komai bana tunanin komai wlhy" rike hannunta tayi tace "kinga idan kameel kikasan gani har kina gaba da abinci bara nayi kiranshi awaya lallai yazo kina San ganinsa" cike da mamaki da kuma kunyar abinda Mamie tace ta sadda kanta kasa "Ma bafa haka bane,bana jin yunwa ne sam" tana daga wayarta domin kiransa yana shigowa parlor din da sallamarsa,gaidata yayi ta tashi tabasu wuri tana Murmushi.... Zama yayi kusa da khairiyyah yace cikeda zolaya

Hanjin Jimina...akwai Naci Akwai Na ZubarwaOpowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz