BABI NA GOMA

2.2K 157 7
                                    

🤡HANJIN JIMINA.. Akwai naci akwai na zubarwa🤡

     Billy Galadanchi

HASKE WRITER'S ASSO. (Home of expert & perfect writer's).

Vote me on wattpad@68billygaladanchi.

Sadaukarwa ga Aminiyata Hafsat Ilham.

  *Wannan shafin na sadaukar dashine kyauta agareku yan Taskar billy Galadanchi,Allah yabar kauna*

      10

Kameel yakira dadynsu ya sanar masa komai acikin daren,inda daddyn yace dashi karya damu inshaa Allah kan nan da kwanaki uku komai ze daidaita sabida ze dauki kwakwaran mataki akanshi,kuma yasani komai daren dad'ewa asirinsa ze tonu. A dakin da khairiyyah tayi zama anan aka kai Hilal,amma shi ansaka karti tsaronshi sabida kasancewar sa namiji,a waje suke gadinsa kofar shigowa cikin gidan.... Jin tsit ya sanya ya tashi ya danna wa dakin key ya shige toilet,katin dubu biyar ya loda a wayarshi daga bank ya kira Jawaheer a tsorace ta daga wayar ta a zatonta Mansur ne,batai magana ba yace

"Jawaheer ya gidan" murya na rawa tace "Yaa Hilal kana ina yanzu ina ka hadu da Mansur meya hadaka dashi? A ina nasamu waya?" Ajere ta rattabo masa wayannan tambayoyin ba shiri

"Ki kwantar da Hankalinki Jawaheer, a yanzu haka ina gidan da naji Mansur yakira da gidan mirror sabo,kuma inaga komai zezo da sauki kasancewar khairiyyah anan tayi zama tasan gidan sosai,ni bansan komaiba banmasan ya wajen gidan yakeba fuska a rufe suka zo dani,amma ita khairiyyah tasani kuma besan wannan wayar tana hannunaba zannan rika kiranku amma zan kasheta banaso abugo a cikin kuskure ya kasance suna gun ko haske suka gani zasu fahimta,zan shedawa Al'ameen komai da kameel abinda nakeso daku ku kasance indoor kowane lokaci kuma lallai gidanku a kulleshi tundaga gate inaga ai ba wani da kuke nema da babu shi ko kuwa?"

"Ba komu yaa Hilal ina rokon Allah ya kubutar mun dakai daga hannun wayanan azzaluman mutanen" godiya ya mata sannan sukayi sallama......

  Kameel yadan  samu relief tunda yayi waya da Hilal,yaji cewan komai normal yake,faduwar gabansa daya kar agane yanada waya su masa wata illar yana wa dan uwanshi fatar fitowa lapia daga wannan mugun hannun,sosai ya kurawa khairiyyah ido dukda besan ainahin meya faru da itaba amma yana matukar tausayinta duba da yanda takeda ciki, gashi asibitin sun tabbatar masa da cewar jininta ne ya Hau,hawan jini kuwa ga mai ciki bababbr illah ne,gashi tunda sukazo bata motsaba,har yaje meeting dinshi ya dawo tanata bacci,dan motsi tayi sannan ta bude idonta a hankali,saukesu tayi akansa da mamaki dauke a fuskarta,da sauri ya taso yazo wurinta ya rike mata hannu yace "sannu khairiyyah Yaya jikinki?" Mamakin tane ya kasa boyuwa musamman dataji ya ambaci sunanta,batayi magana ba kawai dai taci gaba da kallonshi,cikeda karfin hali yace

"Sunana kameel kuma ni kanin yayan kine Hilal idan baki mantaba an sanar miki Idan nazo skt zamu koma Kano tare,kasancewar bakida lapiya yasanya nakawoki nan,dafatar kin fahimta" Dan Murmushi tamasa sanan a ahankali tace "Nagane sosai yaa kameel kuma nagode da kulawar ka,Allah bar zumunci" sosai kameel kejin tausayin khairiyyah shi tunda yake be taba ganin mutumin daya bashi tausayin da khairiyyah ke bashiba sam hankalin sa ya tashi ganinta da ciki. Kwanansu daya aka sallameta da gargadin akula da abubuwan datakeci dakuma wata damuwar dazata daga mata hankali,haka dai suka koma hotel din a dakinta ya sauketa da dare yakawo mata abinci amma takasaci damuwa fal aranta wannan cikin dake jikinta ji take tamkar ta kashe kanta tsabar tsanar datake masa,Nasiha yashiga yi mata harya samu taci abincin,daganan ya nemi sanin labarinta bata rage komaiba ta kwashe tsaf ta sanar masa takara sa cewar cikin kuka me tsani

"Yaa kameel Mansir ya cuceni ina zankai wannan abin kunyar arayuwa? Ina zan samu mijin aure bayan wannan mugun abin dana aikata? Rayu wata ta rigada ruguje yaa kameel banida wani buri arayuwa daya wuce mutuwa ta" kameel besan sanda ya taso ya rungume khairiyyah ba shidinma kuka ya saka ji yake tamkar kanwar sace uwa daya uba d'aya aka yiwa wannan cin zarafin da wulakancin,take ya kudiri niyyan ganin karshen Mansur kota halin Yaya,dan bubbuga bayanta yashigayi a hankali a haka ta dena kukan se sauke ajiyar zuciya take lokaci zuwa lokaci hawaye na tsiyaya daga idonta,dagota yayi daga rungumar daya mata ya sanya hannu ga dago habarta ya girgiza mata kai a hankali alamun ta daina kuka hannunsa ya saka ya share mata hawayenta yace cikin tausayi

Hanjin Jimina...akwai Naci Akwai Na ZubarwaOnde histórias criam vida. Descubra agora