🤡HANJIN JIMINA.. Akwai naci akwai na zubarwa🤡
Billy Galadanchi
HASKE WRITER'S ASSO. (Home of expert & perfect writer's).
Vote me on wattpad@68billygaladanchi.
Sadaukarwa ga Aminiyata Hafsat Ilham
03
Ba karamun karkata hankalin jawaheer yayiba akan san sanin menene ke cikin wannan dakin me kuma yake yawan kai Mansoor aciki duk daren duniya mesa daren juma'a ne kadai baya zuwa? Wannan abin na damunta tanaso ta manta da wannan amma sam ta kasa cirewa aranta,yau a school bayan sun kammala exams an tashi a school suka fito abakin gate na school suna jiran isowar driver gidan mirror wanda shine dama yake kaisu yake kuma daukarsu idan sun tashi,har after 3 be zoba gashi sun fara jin yunwa,kallon khairiyyah jawaheer tayi tace cikin kosawa
"Khairiyyah dan Adam be saba yin haka ba kuma nifa yunwa nakeji,ko naje can shop din na karbo mana cock?" Gyada mata kai kurun tayi kasancewar ta bamesan yin magana ba sam,tsallakawa tayi tashiga cikin karamin shopping mall din ta dauko chocolate cookies da cock da kuma wasu chocolate tazo domin biyan kudin bayan an gama bugawa kudin se yaron ya kalleta yace da ita
"Haj basai kin biya ba, yallabai ne yace komai tarin kayan dakika dauka kar a karbi kudinki" kallon mamaki tamasa tace
"Waye kuma yallabai kuma ce masa nayi banida kudi dazai biyamun Kokuwa yawon bara yaga alamun inayi ?" Kallonta yaron yayi "maida wukar Haj bani nakar zomonba rataya aka bani,kuma Nima Bansan shiba,Yaune kadai naganshi awannan shagon,kuma kayanki 2300 kacal dubu goma ya bayar ungo ga canjinki,danshi ya fice tuni" mamakinta ne ya kasa b'oyuwa tace dashi "bani dubu gomar da daya baka duka,da kudina zan biya wannan kayan,ungo kudin" beyi musuba ya karbi kudin yabata dubu goman da canjinta dari bakwai dayake 3000k tabashi,kallonshi tayi tace dashi muje waje koda zaka ganshi ka nuna mun" ba musu ya bita ilai kuwa koda suka fito yana jingine jikin wata mota kirar Mercedes Benz 2017 black se sheqi takeyi yasha dakakkiyar shadda fara k'al dinkin hannu da hularsa black ta kalminshi black agogon hannunshi ma black,daga inda take hango shi tana jiyo tashin kanshin turarenshi daya mamaye ilahirin wurin,waye yakeyi yana dariya ilahirin kefen kumatunsa lobawa sukeyi ga tsararriyar wushiryarsa dake bayyana a duk sanda yayi dariyar,nuna mata shi yayi da hannu yace "Gashinan ni zan koma kan aikina" godiya tamasa taje ta tsaya akanshi harya gama wayar,mayarda dubanshi yayi zuwa ga reta yace cikeda izzah
"Yan mata any problem why are starring @ me like that,how may I help?" Dayan hannunta daba komai ta saka tarike kugunta tace cikeda tsiwa"Yallabai aka ce dani kake kowa oho dai,zuwa nayi na mayar maka da kudin ka tunda ba rokar ka nayiba,Kokuma ka sanar dani idan alamun bara kagani ajikina dazaka biyamun kudin abinda na siya har dan raini zakace Abani canji" kura mata ido yayi na wasu yan dakiku,kan ya mika mata hannu,kallonshi tayi da rashin fahimta amma batayi magana ba,cikeda yanga yace "Bani kudi na malama,kin wani kafeni da ido" sosai taji haushin kalamanshi,mika masa kudin tayi a wulakance ya kalleta ya tab'e baki yace "Haka yakamata kina baiwa Babba abu bawani girmama wa?" Hawayen datake tare wane ya silalo har ranta taji zafin kalamanshi duk tsiwa irin tata se taji nauyin sake hada ido dashi gashi lokaci daya ya mata kwarjini,sadda kanta tayi k'asa ta kasa mika masa kudin,sanda yace
"Bani kudina mana?" Cikeda kasala tace tana me mika masa a ladabce "Kayi hakuri raina ne a bace" bece da ita kanzil ba ya karbi kudinsa ya shige mota ya tayar,har yabar wurin tana tsaye,a center mirror ya ke Kallonta,aranshi yana mamakin tsiwa irin tata dakuma saurin yin laushi datayi,har ranshi gwadata yayi yaga koda itama tanada mugun hali nasan abin duniya. Gwiwa a sace ta karasa wurin khairiyyah ta ajiye kayan tace da ita,Kici kawai ni cock din ta isheni, dama khairiyyah batada yawan magana,shiru tamata kurun ta soma cin cookies din,wasa wasa fa har karfe biyar dan Adam be zoba ga basa zuwa da waya school, kuma Aunty Amal sunsani yau se shida zata dawo bata masan basu koma ba balantana tazo daukarsu,ga yaa Mansur ya gargadesu akan hawa adaidaita,tsakin da jawaheer taja kuwa yafi hamsin,ganin yamma nayi yasanya ta kalli khairiyyah