BABI NA SHIDA

2.2K 165 2
                                    

🤡HANJIN JIMINA.. Akwai naci akwai na zubarwa🤡

     Billy Galadanchi

HASKE WRITER'S ASSO. (Home of expert & perfect writer's).

Vote me on wattpad@68billygaladanchi.

Sadaukarwa ga Aminiyata Hafsat Ilham.

  *Wannan shafin sadaukarwa ne ga babban Aunty Mejiddah Musa,sosai nake jin dadin comments da kuma kulawarki ga wannan book din,Allah ya bar mana ke.*

     06

Murmushi ya sakar mata,ita kuwa mamakinta ya kasa b'oyuwa ta Mike tace murya na rawa " Yaa Hilal me hakan yake nufi? Dama cutar dani kake so Kayi shine kaketa bibiyata" zama yayi ya ce yana mata nuni da kujera " ki zauna magana zamuyi ta fahimta" Jada baya tayi tace cikin kuka "Kayi hakuri idan akan rashin kunyar dana makane abaya wlhy bazan kumaba" matsawa yayi daf dab da ita ya riko hannunta jikinta sai kyarma yakeyi yace cikin tausasa murya "look blacky nifa ba yanda za'ayi na cutar dake har abada mutuncinki kawai nake kariya,akwai abubuwa dayawa na had'ari dasuke tattare da rayuwar ki dana en uwanki wanda sam baku San dasuba,kuma yanz inaso kibani aron hankalinki da nutsuwar ki zamuyi magana kinji" sauke nannauyan ajiyar zuciya tayi tace "To ka sakemun hannu na zan zauna din" saketa yayi lokaci daya suka zauna a tare yayi gyaran murya yace

"Nasani kinada karancin shekaru amma lura danayi cewar kinada kaifin hankali da tunani yasanya nace bara na fito miki baro baro,a yanda na fahimta kema kinsan cewar mijin yayarki ba mutumin kirki bane kuma tabbas kinsan wani abu game dashi me girman gaske,da wannan nakesan ki saki jikinki ki saka aranki ceton en uwanki zakiyi ki sanar dani menene ainahin abinda kika sani game dashi" kasa daurewa jawaheer tayi ta saka kuka lokaci daya

"yaa Hilal nifa ban taba sanar maka nasan wani abin ba ni iyakar sani na mijin yayata mutumin kirki ne kuma bakada wani dalilin dakkoni ka kawoni nan koma nace Kayi kidnapping nawa" kura mata ido yayi na wasu yan dakiku kan yayi gyaran murya yace

"Jawaheer wannan dalilin ne ha sanya nake yabawa hankali irin naki dukda kasancewar kinada karancin shekaru, wannan kadai ya nuna mun cewar zaki iya rike sirri na na har abada,da wannan nake San ki kwantar da hankalinki muyi magana daganan da kanki zaki zabawa kanki mafita" batayi magana yasa yaci gaba

  "Kamar yanda kika sani ni sunana Barr Hilal Muhammad Auwal,sannan kuma d'an haifaffen garin yola ne Adamawa,mahaifina da mahaifiyata dukkansu rikakkun yan boko ne kazalika aiki ne ya kawosu garin kano,na taso na ganni da mahaifana mu biyar kacal mahaifina mahaifiyata se kuma kannena guda biyu Wato kameel da Fatima, mahaifina sosai yakeda arziqi ba kadan kasancewar sa dan na gada ba take haye ba koda ya taso gidansu akwai yalwar arziqi sannan kuma shidinma da kafar dama yafara aikin gashi kuma dan kasuwa sana'ar motoci yakeyi da kuma noma, ya rike mukamai daban daban a cikin gwamnati kanya afkawa siyasa a yanzu haka shine Babba a kamfanin NNPC duk fadin Nigeria wanda ni kaina bansan iyakar sana'oinsa ba Yanzu,na taso ina sha'awar karatun law wanda hakan yasa mahaifina ya tallafamin harna cinma burina na karanci law a nan Nigeria a degree na na farko sannan kuma naje London nayi Dr.degree acan na dawo nafara aiki a kasata,idan da kin wayi garin Kano sosai tabbas zakiji ana labarin Brr.Hilal ba yabawa kaina nakeyiba kawai dai ina sanar miki ba wanda yataba case dani yayi wining,kanina kameel ma kama yayi aurensa kuma da matarsa Hauwa har sunada yaro sunansa Ameer,nidinnan daine Banyi aure sabida wasu han dalilai....tun kafin nasan cewar a gidan Mansoor mirror kike rayuwa nasan mirror,sa annan kuma Kune family na shida da kuka rayu acikin gidan....Mansoor mirror a hasashen mutane sabida basuda tabbas dan cult ne sam bashida Sana'a daya kwakwara shida iyayensa, matarsa ta farko me suna zinatu yar wata almajira ce dake bara a tashar dake kabuga basuda kowa se mahaifi yarta da kaninta lukman,a  haka Mansur ya aure zinatu ya kwashe har mahaifiyarta  da kanenta zuwa gidan mirror, basuyi watanni biyar ba aka nemi mahaifiyarta makauniya ce bata zuwa ko ina aka rasa a haka suka hakura kasancewar basuda gata,a k'aidar gidan mirror ba'a fita Konan da can kuma kinsani koda makota ba'a zuwa bare ma a aiki wani waje indai ba ma'aikatan gidan ba wanda sanin kanki ne a yanzu ma kun nemi yan aiki Amma idan kukace dasu gidan mirror basa zuwa,to a Hakane ya aiki kanin matarsa inda yaron na fita ya bi bayanshi,yakasance se gawar yaron aka tsinta ba private part nashi ba kunne ko daya ba ido ko daya ba harshe,ahaka akayita bincike ba'a gano komai ba,haka yayar ta hakura ta barwa Allah lamuranta,ranar data haihu a asibiti itada jinjinrin duk akanemi su aka rasa se cewa yayi asibitin ne suka sace masa matarsa da jinjiri haka itama maganar tasha ruwa haryau ba labarin su, mace tabiyu kuwa susu biyu ne suma awurin mahaifiyarsu mahaifinsu icce yake faskare basu gatan yau ba na gobe sunanta sailuba ahaka uban ya badata takanshi akafara, rana daya aka tsince gawarshi an cire masa zuciya da yan ciki,a haka itama kanwar matar ya aiketa haryau bata dawoba ita ko gawarta ma babu ita,matarma iyakar abinda gari suka sani shine tana tsohon ciki ba labarin dan ba dalilin sa bare uwar, haka ta ukun yar uwace agareni sedai bana kasar akayi auren shine dai be sannu ba, a yola ya aurota itama din haka tazo da kanwarta Aiken kanwar kurun yayi gidansu se gawarta aka tsinta ba breast ko daya ko ido ko daya,yar uwar tawa ma haka iyakar sanin mu cikine da ita bamu sake sanin inda akayi da itaba,bana kasar yace wai tagudu yawon karuwanci haka mahaifina ya manna shi kotu amma haka Shari'a r ta watse sabida ba shaidu har daukaka kara yayi wai ammasa Sharrin yankan kai dandai mahaifina nada dukiya ne kuma shimadin yana fad'a aji,koda na dawo kasar naso tada fitinar mahaifi nane ya hanani, A kauyen danbatta yakuma zuwa ya auro wata baiwar Allah itama haka ya kasheta alokacin tanada tsohon ciki domin kuwa ita mahaifinta kara yakai kotu,shima din yana hanyar tahowa nan Kano aka nemeshi aka rasa haryau a ranar d'a za'ayi zaman farko,se na biyar daya auro abarsa daga garin Kaduna yarinya yar fillo tana sayarda furarta mahaifinsu mutumin ruga ne ya mutu tun suna yara ya barta da kannen ta uku itace ta hudu,a haka ya yayibosu har uwar,duk wanda ya aika sedai gawarsa basa dawowa sam,hankalin uwar yayi mugun tashi musamman da yar tace da ita taganshi da idonta yana yanka mutum,tsohuwar dai guduwa tayi amma ya kamota ya kashe itama yar daga ciki bamu kuma jin tarihintaba......sanar dani my blacky tayaya zan samu nutsuwa kin kirani kince ya aikeki? Wlhy bazan iyaba bazan boye mikiba sam ni ban yadda da mijin yayar kiba koda kikace ta sauka lapia nasha mamaki sabida nasan duka matansa daga haihuwa suke mutuwa,Nayi Niyar taimaka miki wlhy bazan iya kyale Mansoor ba idan har ya taba daya daga cikinku,da information naki kadai zan taimakeku dan Allah ki sanarmun me Nene kika sani game da Mansoor " share kwallah tayi tace "Tabbas yaa Hilal biri yayi kama da mutum......." Take ta kwashe komai from  a to z ta sanar masa tana kuka tace "waye ma yasani koshine ya kashe mana umman mu? Kuma nasani yanzu haushina yakeji tunda nice na zuga muka masa dabara muka kai Aunty Amal asibiti harta sauka lapia" cikeda tausaya wa yace "Allah yafishi kuma inajin ajikina lokacin tonuwar asirinsa yazo bazan taba kyaleshi ba yana cutar da bayin Allah kullum wayanda basuda gata yake cutarwa tsabar mugunta,wlhy se inda karfina ya kare" shiru tamasa tanata kuka tana adua ya taso yazo ya mikar da ita tsantsar tausayi tabasa rungumeta yayi yana bubbuga bayanta a hankali,bata wani yi yunkurin kwace jikinta ba domin tana bukatar hakan,kwanciya tayi lamo ajikinsa tana sauke ajiyar zuciya a hankali........... Duk Mansoor ya wani birkice jin cewar yaransa basu hadu sa jawaheer ba sam Kodai ta fitane ba'a wannan lokacin ba,parlor yazo yace da khairiyyah "khairii yaushe jawaheer tafita ne ina nuffin karfe nawa tabar gidan?"

"Sha biyu ta gota sanda tayi wanka sannan ta fice" komawa yayi dakinshi yakira yaran "ku barta Kunyi sabanine tun goma nace tafita Ashe ban saniba se shabiyu tabar gidan idan zata dawo da dare sai ku kaita gidan ginin mirror na sama,zan sanar muku idan zata fita". Koda yaje gidan da dare aka sanar masa bata nan batama zoba,hankalinshi yatashi matuka Dodon makuba yamasa alkawarin yau dinnan ze aikata abin akan daya daga cikinsu,yanzu besan yanda zeyi dashiba,komawa yayi gidan yace " khairiyyah akwai kayan dazan siyo Kizo muje tare bazan iya zuwa nayi shirmeba kaya se mata" harga Allah khairiyyah bataso hakanba yasanya tayi shiru seda yayarta tayi magana sannan ta mike tamkar wacce kwai ya fashewa aciki taje d'akin su tana shiryawa ahaka jiki ba kwari ta fito suka tafi a hanya se adua take zubawa ba k'akakutawa wacce duk tazo bakinta,wayanta ne yashiga ruri ta d'aga ganin bakuwar lamba yasanya tayi sallama kurun cikin sanyi,a d'aya bangaren kuwa muryar yar uwarta tajiyo tana cewa

"Khairiyyah jawaheer ce kuma idan kina cikin mutane kada ki kira sunana,koda Yaya Mansur ya ce ze aikeki karki fita yau darane kawa wlhy yankake zeyi,dan Allah idan kin samu hanya ku gudu keda Adda Amal Nima nafice wlhy bazan dawoba zan rika kiranki da wannan number din" murya na rawa cikin son boye damuwar ta tace "Eyyah Ummul bana gida kije kawai kiyi barkar nafita da Yaya Mansur siyayyar kayan yara" dan juyowa yayi ya kalleta be kawo komai aranshi ba,jawaheer tace "Innalillahi wa inna ilaihirraj'un,yanzu kina nufin harkun fita kuna inane yanzu?" Dan satar kallonshi tayi tace tamkar zatayi kuka "Idan muka sauka shagon zan kiraki nakara miki kwatancen gidan kinji?" Kan tace wani abu ya watsa mata wata powder take ta sume awurin daukar wayar kurun yayi ya disconnecting call din ya dauki hanyar sabon gidan mirror da ita, khairiyyah farkawa kurun tayi taganta kace kace acikin jini gashi batama iya motsa jikinta Konan dacan kuma ita kadai adaki ihun data saka yayi daidai da fitowar Mansoor daga toilet yana tsane ruwan kanshi da towel, kuka sosai tasaka tashi mishi magiya "Yaa Mansur dan Allah ka taimakeni karka kashe ni wlhy bawanda zan taba fadawa kai dan yankan Kaine karu fawa rayu wata asiri karka cutar dani wlhy banaso inmutu" mamaki da zallar mugunta ta hango a kwayar idonshi yana nufo inda take cizgota yayi da sauri ya shaqo wuyanta ahaka ya mikar da ita tsaye "Ubanwa da wa kika San kin sanar abinda kika gani?" Tanaso tayi magana amma yabshaqeta dakyar ya saketa ya manna ta a bango "sanar dani wa kika gayawa abinda kikaji kuma kika gani?" Tana kuka tace "Wlhy yaa Mansoor banida niyyan tonama asiri ba wanda na sanarwa nikadai nasani" dariya ya kwashe dashi "kin taimaki yan uwanki dabaki sanar musu ba,daduk na hallakar dasu,kekuma kisani idannkin samu ciki wannan tarawa damuyi to ranar dazaki haihu ranar zan kashe ki don ni ko uwa tace taga sirrina sena kasheta wannan gidan dakika shigo sedai afice da gawarki sannan kuma bake ba ganin waje har abada.." Yana gama fadar hakan yayi waje abinshi ya kulleta ta ciki.

Mom nuaiym

Hanjin Jimina...akwai Naci Akwai Na ZubarwaWhere stories live. Discover now