BABI NASHA BIYAR

2K 144 3
                                    

🤡HANJIN JIMINA.. Akwai naci akwai na zubarwa🤡

Billy Galadanchi

HASKE WRITER'S ASSO. (Home of expert & perfect writer's).

Vote me on wattpad@68billygaladanchi.

Sadaukarwa ga Aminiyata Hafsat Ilham.

*Ko kadan banji dadin comment dinku Ba,musamman Masu aikamun saqonni ta private, tun farko babu wanda ya tsaramun yanda Zan rubuta littafina idan kaga bazaka iya karanta wa Ba,karka takura kanka tunda Ba dole,amma ku sani I'm not happy with you ko kadan*

15

Sosai Mansur ya Saka karfin sa wurin ganin ya wulakanta Jawaheer, amma ga mamakin sa ji yayi an lankwashe masa abar da karfi,take ya kwallah kara ya saketa,jikinshi yabi da kallo yaga ta karye ta juye gefe daya tamkar karyayyar kafa,wata iriyar razananniyar kara ya sake yayi cikin daki da gudu,Aljana yar tsito ce ta fito masa a siffarta ta yara tace tana me kwashewa da dariya

"Nabaka dukkanin dama ka wofintar da damar dana baka namaka lamuni akan wulakanta mutane da kake,bakasan darajar rayuwar dan Adam ba kisa awurinka Ba komai bane har kananun yara kake yankawa sabida kurun ka samu duniya,zan Barka da duniyar Mansur amma zan rabaka da abubuwa guda hudu masu muhimmanci arayuwar ka,zan rabaka dasu daya bayan daya yanzu wannan abin dakake takamar lahanta rayuwar Yaya mata da ita ka rasata kenan har abada,bazaka kara moruwa da itaba har abada,kuma kasani ban gama dakai ba" cikin tsananin rudu da gigita yace "Dan Allah kiyi hakuri yar tsito wlhy kisani dukkanin abinda kikeso dani zan aikata agareki ki rufamun asiri karki mun haka" wata razananniyar murya yaji tace

"Baka San Allah ba sanda moruwa da ni'imomin yayan mutane,bakasan Allah ba sanda kake moruwa da ni'imomin jikina ina maka ihu ina magiya ina hadaka da Allah baka saurareni ba,wlhy Mansur bazan taba saurara maka ba arayuwa,na dinga rabaka da abubuwa Masu muhimmanci kenan arayuwar ka daga nan harka koma ga Allah" daganan ta bacewa ganinsa anan ya durkushe yanata faman kuka,su kuwa wayannan kartin se fitowa tayi da Shiga irin na Mansur tace dasu

"Ku mayar dasu gida yanzunnan ba se anjima ba,kuma ku basu kudaden dake cikin wannan jakar gaba dayan su" Kansu Amal ya kwance suka susuce,a haka aka kamasu aka mayar dasu Gidan salun alun.....

Kamar daga sama suka jiyo muryan Daddy yana cewa "Ke Mariya baki isa ki hanawa yara jin dadin su ba,idan dai akan zancen Amal ne ni wlhy na janye,banida masaniyar akwai aure akanta,hankali na sam beje canba, sa'anna Alhj sammani ya lurar dani rashin dacewar hakan,yace wannan kwamacalar beyi ba, kuma na fahimceshi,na kuma fahimci cewar wlhy naci zarafinki da wannan sabida haka kiyi hakuri,a yanzu haka mun yanke sha'awar shi Alhj sammani ya nemi aurenta tunda yake tun bayan mutuwar Haj karime be sake aure ba,kuma yaran na bukatar tallafi,dan Allah na rokeki ki janye wannan kudirin ki barsu suyi aurenki sabida wanna zullumin dana sakaki na miki Alkawari Allah ne shaida na dakuma yaranki,bazan taba miki kishiya ba koba Amal ba" sadda kanta kasa tayi sannan tace

"Amma Alhj kasan cewar anci zarafina da yawa ko,tayaya ma zan rike yaranna da Amana sannan daga bisani kace zaka hadani da yar Cikina kishi,wlhy sam banji dadiba kuma yaran sun munafunceni suna sane sabida kwadayi suka nunnuke Kansu" dafa kafadarta yayi yace "Haj Mariya ki yarda dani wlhy tallahi billahi banda gaisuwa wata magana me kamada wannan bata taba Shiga tsakanina da Amal ba,ita kanta batada masan iya akan abin da na aikata,sa'annan kuma Babanta ya sanar mun cewar har can Lagos ta sameshi ta sanar masa bazata taba aure naba,duk dan tana ganin tamkar anci zarafinki idan akayi hakan" nisawa tayi tace

"Dan Allah ku gafarceni ina rokon Allah yasanya Alkhairi da albarka a rayuwar auren nan da Zakuyi,ya kuma kareku daga Sharrin masheranta" da murnarsu suka amsa da

"Ameen ya Allah,mun gode sosai Mamie ,mun gode Daddy Allah yabar kauna ya kara girma" kallonsu daddy yayi yace

"Bazanso kuja lokaci me tsawo ba,zan baku kudade kuje ku had'o lefe nanda watanni biyu nake San ayi auren,ita kuwa Amal bazamuyi maganar Alhj sammani ba seta gama iddah" murna da godiya suka masa ska bar gidan cikeda d'oki kai tsaye gidan Amal suka wuce,Labarin da suka tarar ne ya rikitar dasu matuka,sam basuji dadin abinda yafaruba kasancewar yaran zasu kasance cikin zullumi, Hilal ne yakira Ummie ya sanar da ita yanda ake ciki,ita kuwa takira daddy ta sanar masa,dama a ranar zeyi tafiya yayi umarni da akai kudaden bank batare da an taba ko kwandala ba sannan kuma tunda akwai sojojin dake tsaron gate na gidanshi su dawo dayan part din baki,bayasan wani abin ya kuma tasowa,Allah sarki Mamie mace me karamci take ta sanarwa su Hilal.....hakan kuwa akayi suka dawo gidansu Hilal din, khairiyyah ce ta kalli kameel tace

"Kameel kunada kirki sosai Allah ne kadai zai saka muku da Alkhairi" murmushin dake karawa fuskarsa kyau ya sakar mata yace "Ameen yar lukuta ta kameel" zumburo baki tayi tace dashi

"Wai nikam bazaka dena kirana da wanna sunan ba ko tam Allah Nima daga yanzu ba ruwana dakai" cikeda rarrashi yace

"Haba Amarsu,kiyi hakuri mana keda kameel dinki ne fa" hannayenta ta saka ta rufe fuskarta kan wani yayi magana call yashigo wayar shi dagowa yayi yaja tsaki ya mayar a aljihunshi maraimaricewa tayi tace "My kameel Deenah ko" Murmushi ya sakar mata yace "Bakya so take kirana ko other half" tsuke baki tayi ta zumburo shi batayi magana ba, Murmushi yaku mayi akaro na Barka tai yace

"Amma other half kema kinsan bana kulata ai ko" Banza ta masa nan ma yace "Haba mana Habibty" kara tsuke bakin tayi tace tamkar zatayi kuka

"Allah ni yaa kameel ka sanyata a black list na tsaneta ita ke sanyawa kana kwasar zunubi gwaramun ka aureta da wannan abin" dan bata fuska yayi yace

"Tun yaushe nake sanar dake cewar hadu wata dake Alkhairi ne? Wlhy aure bazaya taba yin kyauba inhar da zargi aciki,ina murna kin aminta dani zaki zomun da wannan maganar" sosai fa kameel ya fusata dama badai zuciya ba,shiru ta masa kurun shikuwa ya mike da zummar barin parlor din ,mikewa tayi itama ta cafko hannunshi ya waigo yana Kallonta har idonshi ya kada,sosai ta tsorata da lamarin shi bata taba ganin irin wannan yanayin atare dashiba kasa magana tayi suka kurawa juna ido kurun,zare hannunshi yayi yabar gidan gaba d'aya, anan ta zauna tana kuka sam bataji dadin abinda ta masaba,kar yaga kamar danya sanar mata siirn sane...... Juju kuwa a motar Hilal se zuba takeyi

"Yaa Hilal kalli kalar wannan dinkin,dress din ta hadu totally,irin ta zanyi a ranar dinner shi zan saka" dan waigowa yayi ya kalli dinkin yace yana me mayar da hankalinshi ga tukin da yake "Blacky Kefa kin iya iyayi kota Yaya zaki fito acikin wannan jar rigar wayaga black in red,mugun ta kurun zakiwa kanki wlhy nazo nafiki kyau ace bamu dace ba dama mana blacky and yellow" zumburo baki tayi

"Ea din ace kafini kyau na ji,ina Kaine da kanka ka zaba bakar" Murmushi yayi yace

"Kece dai kika nace,banda haka mutum ya maka kyauta yayi tafiyarsa meyey na biyosa,salon a nanukamun black skin,Aini nasan zansha managy kuma kowa yasani farar mace itace ta sakawa agaban mota,Allah idan natashi karo aure yellow girl zan dakko,kinsamu ta shanawa" hawayen kurun Jawaheer tafara dama akwai aukin kuka,parking yayi ya janyota jikinshi yace "subhanallah my wife menene abin kuka" turesa tayi

"Toba kai bane kullum seka zagi halittana kuma sekace wai zaka mun kishiya" harga Allah dariya tabashi yace "kinga maida wukar,nifa wlhy banasan farar mace wasa kurun nake miki harga Allah wannan fentin naki da ba'ayi da man kanyi shiyaja hankalina akanki @ first so ki nutsu nidake ba kishiya..." Dukda wannan dad'in bakin daya mata bata sakko ba....

Mansur ya sanarwa mahaifinsu komai hankalinsa ya tashi yarasa yakeyi,dodon makuba ma yace ba abinda ze iyayi.......yau koda Mansur yatashi bacci ga idonshi bude amma baya ganin komai,se duhu gashi shi kadai ko waya yakasa operating balantana yakira wani se ihu yakeyi,muryan yar tsito yaji

"Ban sanar maka cewar zaka rasa abubuwa Masu muhimmanci guda huduba acikin sassan jikinka,karasa biyu kenan saura biyu" daganan yaji shiru haukace wa yayi yafara sambatu.....

Mom Nuaiym

Hanjin Jimina...akwai Naci Akwai Na ZubarwaDonde viven las historias. Descúbrelo ahora