BABI NA TAKWAS

2.1K 145 5
                                    

🤡HANJIN JIMINA.. Akwai naci akwai na zubarwa🤡

     Billy Galadanchi

HASKE WRITER'S ASSO. (Home of expert & perfect writer's).

Vote me on wattpad@68billygaladanchi.plss dnt forget to vote and comment.

Sadaukarwa ga Aminiyata Hafsat Ilham.

   *Wannan shafin na sadaukar dashi ne ga reku Hanjin jimina's Fan's, wlhy inajin dadin comment naku sosai sosai,ina kaunarku sosai kuma ana tare irin totally dinnan*

        08

Sosai Hankalin Amal yatashi ganin cewar bil haqqi Mansur ita yake bi,ana cikin haka wayarshi yasoma ringin,yana dagawa me gadinsa yace masa "Yallabai da matsala fa da kazo gida wlhy kaga yanzunnan muka fara jiyo kukan mutane daban daban daga cikin gidan kuma nayi kokarin Shiga naga ko lapia amma kofar gidan taki budewa gashi naga madam tafita aguje kuma ka dafa mata" rikicewa Mansur yayi wannan kadai alamace dake nuna cewar Amal tabar wannan durowowin data bude a bude wanda ba karamin masifa taja masa ba ak'aida ma ba'a bude dakin da rana kuma duk kofar da aka bari a bude gawarwakin ciki zasu dena bada dukiya,gashi me gadin ya sanar masa cewa kukane daban daban,hakan ya nuna cewar ba daya tabari a bude,ba idan me producing dalar amurkane ta gama dashi wlhy,da sauri suna zuwa kan u turn ta mike shi kuwa ya juya zuwa gida......

   Ganin ya dena Binta be saka hankalinta ya kwanta ba,waya takira number dinda jawaheer tamata sending Hauwa ce ta daga dayake tasan komai, "Hello Juju ganifa kuma Mansur harya biyoni baya yakuma komawa wlhy yau nagano wa kaina masifa,inane unguwar kuma inane gidan" misali Hauwa tamata sannan ta kashe wayarta gaba d'aya takama hanya gashi Ziya'ul haq se kuka yake ko saman car sitter bata daura saba,a haka ta isa gidan batasha wahalar ganeshiba kasancewar ba wani boye yake ba a unguwar Jan bulo,koda tayi horn me gadin bude mata kurun yayi ta shige,jawaheer da gudu tazo ta bude mata gidan ta rungumeta suka saka kuka,kasa sanar wa jawaheer tayi meta gani kurun ta barwa ranta akan se Hilal yazo..... "Ko kadan Hilal hankalin sa be kwanta ba ta jin cewar ba labarin khairiyyah har wannan lokacin,idan hankalinsa yayi dubu toya tashi,yasani Mansur bashida imani ko kadan,koda Amal ta sanar masa meta gani yaji sanyi har ransa cewar sunada evidence me kwari against him,da wannan ya ce zasu koma gidanshi garsu taku rawa Hauwa,shikuma ze koma cikin bq wannan shine umarnin mahaifiyar sa domin tasan komai,Amal godiya tamasa tace

" yanzu Hilal to da motana zamu tafi ko Yaya?" Dan rausayar da kanshi yayi yace "Bazaki tafi da motar kiba hasalima bazaki kara hawan taba bakida labarin cewar motar babban identity ce idan ana amfani da ita zeyi tracing naku,yanzu you have to be very careful kuma ku yi hakuri akan zancen khairiyyah indai tana Raye da yardar Allah sena nemo muku ita,kuma shi Mansur yanzu haka na nemo komai na samo number dinsa nakai Mtn office nakuma kai dayar Airtel office daganan har zuwa lokacin dazamu kammala binci kenmu zasu bamu information na dukkanin calls dayake yi" dan nisawa Amal tayi tace cikin kuka "mun gode mun gode sosai Brr Allah ya saka maka da Alkhairi yakuma daukaka ka ya kare da dukkanin wani abin qi" sosai sukaji  dadin adu'arta shida dan uwansa kameel.

*Bayan watanni hudu*

   Iya kokarin daya kamata Barr yayi yanayi amma har yanzu shiru gashi alamomi sun fara nuna cewar tabbas Mansur yafara shinshino wani abin game dashi,gashi dama ka'idane a kungiyarsu duk wani yaga mahakar dukiyarka seka samu wani matsala a yanzu haka bayaji da kunne daya,gashi kullum fatanshi yaga Amal Allah ya dora masa kaunar ta fiye da tunanin me karatu,ita da yaronta yana San ziya'u ba kadan ba,yayi neman duniyar nan babu su ba labarin su,yauma kamar kullum mahadarsu ta tsafi inda suke ganawa da dodon su na makuba,Mansur na durkushe yana rokonsa

"Ka taimakeni me bayarda dukiya,ka taimakeni me wanka da jini,ka taimakeni mecin yayan cikin dan Adam,ka bude mun littafinka na tsafi ka sanar dani inda Amal da ziya suka shige" wata mahaukaci yar dariya dodon ya sake yace

Hanjin Jimina...akwai Naci Akwai Na ZubarwaTempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang