BABI NASHA HUDU

2K 149 4
                                    

🤡HANJIN JIMINA.. Akwai naci akwai na zubarwa🤡

Billy Galadanchi

HASKE WRITER'S ASSO. (Home of expert & perfect writer's).

Vote me on wattpad@68billygaladanchi.

Sadaukarwa ga Aminiyata Hafsat Ilham.

*Assalamu Alaikum, nagode sosai da adu'o inku fans nasamu sauki sosai Allah bar zumunci*

14
Ba shiri Amal tabi jirgin yamma daga kano zuwa Lagos, a gajiya ta isa gidan Baba gambo,bayan ta natsa taje ta samu shi,cikeda mutunci suka gaisa sannan tace

"Baba dama nazone akan zancen danaji wai kabada aurena awurin mahaifinsu maneman auren su khairiyyah,bayan kana sane cewar mijina ba sakina yayiba,har yanzu da akwai igiyar aurena akan sa kuma Baba ko bayan haka baka ganin idan mukayi haka munci zarafin mahaifiyar su Hilal,matar nan ta mana komai a rayuwa itace tayi dawainiya da khairiyyah har Allah ya sanya ta sauka lapia,wlhy Baba ko banida miji kusani bazan taba auren wannan mutumin ba" zare ido yayi ya Hau banbami

"Bakida hankali ne Amal? Ina ma zaki fara hada wannan shirmen? An gaya miki muna haukane dazamu bari ki komawa matsafi wlhy baki isa ba,ina sane cewar auren naki na nan,kuma yanzu haka Auwal na kano an yankawa Mansur da ubansa sammaci gobe ma zaki koma,sabida jibi za'a fara zaman kotu harni,bayanki zanbi,domin kuwa tabbas seya sakeki bazamu yadda ba kina zama da igiyar dan yankan kai a akanki" nisawa tayi tace

"Dama Nima Baba bawai so nakeyi nata Zama da igiyarsa akaina ba,kawai dai ina fada muku ne wlhy bazan taba aurar mahaifinsu kameel ba" cikeda fusata yace

"Ke baki isa ki nunamun kin isarwa kanki ba wlhy,yaushe aka haifeki? Kuma aure narigada na bada se naga yanda zakiyi" cikeda bacin rai tace

"Yanzu ni ina da aurena aka,kuma koda banida shi tunda yake ni din zawarace nice nake da haqqin tsayarwa da kaina mijin danake so na aura bawai kuba,bazan taba aminta na ruguzawa marayun Allah rayuwar suba sabida wata San duniya taku,banasan daddyn kuma bazan aureshi ba,zancen Mansur kuma dama gobe zan juya ta jirgi nazo kuma ta jirgi zan koma" tsawa ya daka mata

"Ke dan ubanki kina ganin kin isarwa kanki kenan ko? Wlhy baki isaba muje kanon araba auren idan kika ban daura miki aure da Alhj ba ban Cika sunana gambo ba" kunkuni tashigayi tasaka kuka"

*Bayan Kwana daya*

Tare suka sauka ta jirgi da baba gambo daga Lagos a kano,kai tsaye gidan ta ta wuce dashi inda ya sauka a dakin baki,basufi awowi biyu da sauka ba Hilal yakira waya yake sanarwa Amal cewan mahaifin Mansur ya kaisu kara a kotu akan sun hada baki da mahaifin su sun likawa dansa yankan kai sabida kurun mahaifinsu naso ya auri matarsa kuma sun gudu mishi da yaro,baya ga haka sun mai asiri akan duk inda yaje mutane namasa kallon mahaukaci" sosai ta girgiza dajin wannan abin.....A kotu batare da bata lokaciba aka fara gabatar da zancen sakin da akeso Mansur yayi wa Amal,inda aka tambayeta bata rage komai ba na abinda ta sani da wanda ta gani game dashi ta fada, koda akace Mansur yafito wai bayanan,ran alkali yabaci ya dage sauraren karar se gobe akan lallai ya kawo kanshi......washe gari kuwa koda Mansur ya bayyana a kotu kowa seya fara sussune kai,inda alkhali yace cikeda rudani

"Bawan Allah Yaya zamu bukaci ganin mijin wannan matar kazo mana ta mahaukaci kuma tsirarara acikin court Hall" mamakine ya kama daddyn Mansur domin kuwa harga Allah dansa sanye yake cikin Shiga ta alfarma hadda hularsa ka,kallon alkali yayi yace

"Ya me girma me shari'a tayaya d'a na yana cikin suturun sa na alfarma zakace wai bashida kaya?" Kallon takaici yayiwa daddyn Mansur yace da dandazon mutanen daketa faman sunne kai a court Hall din

"Jama'a wannan nawan Allah yana sanye da sutura ido nane yake hangomun tsiraicinsa kokuwa aa tsiraran yake?" Wasu daga cikin mutanen suka ce

"A tsirara yake ranka ya dade" ran me shari'a ya baci yace afice masa da Mansur,zuwa office dinshi,acan sukaje da Amal yace ya saketa tunda bataso, dakyar da sid'in goshi ya saketan,inda alkalin ya shaida wa Amal basuda hurumin damke shi da laifin yankan kai,tunda basuda wata kwakwaran hujja ko kuma shaida" A haka dai aka dawo court halla alkalin yayi watsi da karar mahaifin Mansur, Mansur kuma ya nemi a bashi danshi take alkali yace a musulunce ma se yaron ya shekara bakwai a hannun uwarshi,sabida haka ya dena ma wannan mafarki........

Baba gambo dai ya kafe akan auren Amal da Alhj Muhammad Auwal,acewarsa daga zaran tayi iddah ze daura musu aure.

Zaune Mamie take ita da kawarta Hajja gana da kuma kanwarta mansura tace

"Hajja gana nifa wlhy bazan taba lamunta da wannan mugun kwad'an ba bata yanda za'ayi na bari yarana su auri wayannan mayun mutanen,banda maita ina dalilin wannan jarabar da masifar wlhy ba daniba" nisawa mansura tayi tace

"Dan Allah Aunty ki kwantar da hankalinki ni banga laifin yaran nan ba wlhy,ki barsu suyi aurensu inyaso shi daddyn su fatsima a sanar masa baze yiyu ba" hara ta wurga mata hajja gana tace

"Mansura ki rabu da ita ta dauki hukuncin daidai laifin da aka mata,ai basu kadai bane yaran aure agarin ina" dan mata rai mansura tayi

"Sabida Allah aunty Hajja wannan wane irin gurguwar shawara kike bata? Wlhy wannan sam ba soyayya bace,gaskia da sake wai an baiwa me kaza kafa,bata yanda za'ayi atakura yara,tun yaushe muke ta fatan Hilal yayi aure yanzu Allah yayi zakizo kina zigata" harzuqa itama Hajja tayi

"Wlhy komai sanmu da farin cikinsa bazamu bari ya auri dangin mayuba,dan zagaye dangin ma yara biyu har ubansu,wlhy baze yiyu ba,yaje ga ga yakura can ya aura ai yar uwarsa ce shi kuwa kameel dududu yaushe yayi auren?" Zaro ido waje mansura tayi ta dafe kirji

"Haba Aunty gana,wlhy wannan ba adalci bane tun yaushe Hilal din yake ganin yakurar daya na Santa aida yaje tuni ya nemeta" mamie ce ta wace

"Wlhy kobaya santa se dole ya aureta,matukar indai ina numfashi wlhy bazasu auri wayannan yaranba haba akan me" fusata mansura tayi ta zari key na motarta ta bar gidan gabaki daya....kameel da Hilal durkushe agaban Mamie yayinda take zaune akan kujera ta daura kafa daya akan daya tana girgiza su tace

"Idan dai nice na haifeku wlhy Dukkaninku ku janye zancen auren wayannan yaran yanzunnan kai kameel baka wani dade dayin aurenba sabida haka ba zancen karin aure agareka kai kuma Hilal kaje ka samu yakura ku daidaita kanku,narigada na gama magana ta,kuma duk cikinku wanda ya kafe yaje na sallamawa duniya shi,yazama koni ko soyayyarsa ga mayya!" Dukkaninsu gigicewa sukayi suka dimauce,an rasa wanda zaice wani abin.....

Cikin dare su Amal ji kawai sukayi ana tashinsu koda suka farka ga karti nan sunfi su bakwai akansu Bame alamun imani aranshi suka tasasu agaba zuwa mota har jaririn Amal,rufe musu fuska akayi,sanda aka Shiga dasu wani gidan sannan aka bude musu fuska,Mansur suka gani tsaye a tsirara ya kallesu ya kwace da dariya yace

"Amal kin zaci zaki guje mun ne? Wlhy Kunyi kadan sanadin ku nake yawo tsirara duniya namun kallon mahaukaci,kuma tunda kuka shigo rayuwata nake ta asarori iri iri,wlhy Sekun gane kuranku,kuma karku zata da akwai uban daze kawo muku doki,wlhy babu shi dukkaninku zan rika amfana da ni'imomin jikinku musamman ke Jawaheer takanki zan fara...gadan gadan ya yo kanta ya wanka mata mari,dama kayan bacci ne ajikinta iya karfinsa yasaka ya farka mata riga,Amal nata kokarin kwace kanta amma sam ta kasa kasancewar karti sun riketa...ahaka tana kallo Mansur ya afkawa jawaheer....

Mom Nuaiym

Hanjin Jimina...akwai Naci Akwai Na ZubarwaOnde histórias criam vida. Descubra agora