Babi na uku

4K 159 3
                                    

🤦🏾‍♀         *Rayuwar*        🤦🏾‍♀

          🙆🏾       *'Ya*    🙆🏾

🙎🏽            *Mace*              🙎🏽

Na Billy Ladan

♻ *EXCLUSIVE* *WRITERS* *FORUM*

*3-5*

*_Am dedicating dis page to HawwaDy, Kakaya Bukar, Ashwal, Hafsat Abuja da duk sauran members na Hausa Novel Lovers, Ina Sonku sosai Allah ya bar zumunci, Amin_.



Sabbura na shiga ta hango umma zaune gefenta da yar muciya, cikin tsoro ta zo zata wuce ta gefen Baba saude dan dakinsu na gaba da nata, muryarta na rawa ta mata barka da rana ta sa kafa zata shige dakinsu ta ji a finciko hijabinta tayi baya ta fadi ganin Baba Saude tayi ta yo kanta da muciya ta hau rafka ihu tana rokonta, kaimata bugu da muciyan tayi Sabbura kuwa ta dago hannu ta kare kanta ai kuwa ta rafka mata a hanu, wani uban ihu ta saka tana "wayyo Abba kaxo ka ceceni, Abbanta kuwa tundaga zaure ya fara jiwo muryanta wanda ya sashi saurin karasawa ciki gani yayi Baba Saude ta daga muciyar tana kokarin sake rafka mata, wani uban tsawa ya daka mata da ya sata wurgar da tabaryar, karasowa yayi ya sunkuya gefen Sabbura yana " Sannu Sabbura taso kizo, ya dagota sannan ya dubi Baba Saude yace "wai ni Saude yaushe zakiyi hankaline, ace kullum aringa miki magana akan abu daya sai kace yaro,  ai ni yakamata ki daka ba ita ba tunda ni nace ta tafi krta miki aikin dan na san dalilin cin zalinta da kike knan, wlhy yau ya zamo rana ta karshe da zan miki magana akan yarinyan nan in ba haka ba zan mugun saba miki, ya juya ya dubi Sabbura yace je dakina ina zuwa, dakin Anna ya shiga dan dubo man zafi yayi mamakin ganinta kwance tana daddanna wayarta cikin kwanciyar hankali, kada kansa yayi ya dauki abunda zai dauka ya fice dan ya gaji da mata magana itama kuma bai shirya bacin rai ba dan yasan in ya fara bazasu gama ta dadi ba.

Zaune ya sami Sabbura tana ta sharar kwalla ya nemi waje ya zauna, tausayin yar tasa yake sosai, wani lokacin yakanji kawai ya aurar da ita ko ta huta da wahalar da take sha amma ya dubi karancin shekarunta ya kan gusar da wannan tunanin, matsowa yayi yace " inga inda ta ji miki ciwon, hannunta ta miko ya kuwa ga wurin har ya tashi ya shafa mata man zafi tareda murzawa, duk dauriyarta sai da hawaye ya diga mata yana gamawa ya dubeta cikin kulawa yace "Kiyi zamanki nan gefena kr ki fita ni zan koma kasuwa, a dawo lafia tace mishi ya fita zuciyarsa fal tausayin yar tasa.

Yana fita Sabbura ta fito dan zuwa canza kayanta tayi sa'a Baba Saude ta shige dakinta tayi sauri itama ta shige dakinsu, bai jimaba ta fito da ragowar karyanta ta yi sashin Abbanta ganin Anna zaune bakin kofarta ya sata karasawa ta russuna tace "Anna Sannu da hutawa, batareda ta dago ba tace " yauwa, gefenta ta zauna dan ta karasa cin abincin kawai taji an tsaya a kanta, dagowa tayi ta ga Baba Saude tsaye kanta tana ta huci "yanxu ai sai ki wuce muje tunda ubankin da ke daure miki gindi baya nan, cikin i'i'na Sabbura tace " dama Baba Saude so nake in naci abinci sai inzo in fara aikin dan yunwa nakeji kuma in na fara da yunwa nasan zan wahala wlhy, gani tayi Baba Saude ta sa kafa ta shure abincin ya zube gaba daya sannan tace "ai sai ki cin mugani, kin wuce ko sai na babbalaki, juyawa Sabbura tayi ta kalli gefen mahaifiyartata da tayi kaman bata wajen taga itama karatunta take, cikin sanyin jiki ta tashi ta shige kicin ta hura wuta cikin minti kadan ta gama dafa shinkafa dan dama tayi miya kan ta fita da safe.

Tana gamawa ta shiga toilet in Baba Saude da yayi kaca kaca ta wankesa Tas ta fito ta ganta zaune a falo itada Rahama, ta ce " Baba Saude na gama, nuni Baba Saude ta mata da hannu ta dubi inda ta nuna mata taga tulin wanki ta juyo tace "Baba Saude dan Allah abar wankin nan zuwa gobe dan hannuna ciwo yake ban dakin ma karfin hali nayi, kallon da Baba Saude ta watso mata shi ya sata yin shiru ta karasa tana hada wanki, hr ta sa kai zata fice Rahama tace Sabbura shiga dakina akwai nawa gudu uku a kan gado na aje, baki bude Sabbura ta juyo take kallonta, Rahama dai kanwartace amma jibi yanda take bata order.

Rayuwar Ya maceWhere stories live. Discover now