13

922 53 1
                                    

Rayuwar*       

               *'Ya*  
          
            *Mace*            

Na Billy Ladan

♻ *EXCLUSIVE* *WRITERS* *FORUM*

*31-32*

bintladan.blogspot.com

_Masoyana ina alfahari da ku a duk inda kuke musamman yan facebook group ina,sosai nake jin dadin comments naku,ina sonku sosai wlhy,ur comments,kols and messages shi ke kara mun karfin gwiwa,shi yasa ma yanxu haka duk da bn jin dadin jikina na daure na rubuto muku yar gajeriyar shafin nan,ina godia sosai,Allah ya bar so da kauna_


Tafiya kadan sukayi taji sun tsaya dan a nan gidansu MK da ke cikin anguwan zasu zauna, cikin dabara ta dago dan ganin ko lafia suka tsaya, gani tayi ana bude wani makeken gate, mamakine ya kamata ganin girma da haduwan gidan, suna shiga ta ga gidan ya kunshi sides da yawa, daya daga cikin flat na gidan taga an yi parking mutane suka fara fitowa, Nani ce ta bude side nata tareda riko hannunta tace "amarya mun iso, ki sauko da kafar dama, a hankali ta fito da kafarta Nani ta mata jagora har zuwa dakinta ita aka barta daga ita sai yan uwanta biyu, tunda suka shigo bata yaye mayafinta ba haka ta zauna da shi abinta. Wata yar uwar Nani ne ta shigo ta ma yan uwan Sabbura magana tana fita suka juyo gun Sabbura suka ce "Toh Sabbura sunce mu fito a maida mu gida sabida haka zamu wuce sai zuwa gobe idan munzo yini, dago idanunta tayi yayinda a take taji hawaye, ganin dagaske tafia zasuyi ya sata dirowa daga kan gadon ta zo ta rike hijabin daya daga cikinsu tace "Goggo dan Allah kar ku tafi ku barni in kuka barni binku zanyi wlhy tsoro nakeji, kamo hannunta tayi ta maidata kan gadon ta fara kwantar mata da hankali tareda cewa za turo mata mai tayata kwana, sai sannan hankalinta ya kwanta ta barsu suka tafi, sai sannan ta lura da irin daular da ta shigo, tashi tayi ta shiga toilet inda ta sake baki tana kallo dan shima ba karamin kudi aka kashe ba. Mamaki bai gama cikata ba sai da ta fito parlor, fadin haduwarsa ma bata lokaci, jikin kujerar ta je ta zauna a takure dan tsoron dakin take ji, har bacci ya fara daukarta taji kaman ana shafa fuskarta, bude idonta tayi a hankali ta saukesu kan kyakkyawar fuskar MK, tsuke fuska tayi tareda gyara zamanta, ledan da ya shigo da shi ya aje mata yace "ga kayan motsa baki nan, ga kitchen can sai ki dauko plate ki zuba, tashi tayi ta nufi inda ya nuna a matsayin kitchen, sai da ta gama kalle kallenta ta dauko plate da cup ta fito ta gansa yana kokarin hada TV, kazan ta zuba kadan a plate sannan ta kwararo mai fresh milk in a cup kafun ta dau sauran ta kai cikin fridge ta koma dakinta. Juyawar da zaiyi yaga bata wajen gashi alamar wa shi kadai ta zubawa, tashi yayi ya nufi dakinta ya ji kofar a kulle take, knocking ya fara yi ko zata bude amma shiru, dawowa parlor yayi ya zauna ya ci kazarsa, sai wajen karfe 12 ya kashe TV ya nufi dakinsa, wanka yayi kafun ya sa kayan bacci ya dauki wani key ya fito, dakin Sabbura naga ya nufa ya sa key dake hannunsa ya bude, hangota yayi tayi dai dai tana ta tirkan baccinta, a hankali ya tako ya zo ya zauna bakin gadon nata, shafa fuskarta yayi ta dan yi motsi tareda gyara kwanciyarta ta cigaba da baccinta, idanunsa na ya sauka kan lips inta yaji duk hankalinsa ya fara tashi, tashi naga yayi batareda ya sake kallonta ba ya fice ya bar dakin.

Kiran Sallar asubane ya tashesa, ya tashi ya fada toilet yayi wanka tareda dauro alwala sannan ya fito, dakinta ya nufa ya jiyo muryarta tana karatu, murmushi kawai yayi ya fita dan zuwa masallaci.

Tana zaune a falo taji an bude kofar ta juyo dan ganin wayene, MK ta gani yana kokarin rufo kofar hannunsa dauke da carbi da alama daga masallaci yake, suna hada ido ta kawar da kanta. Karasowa yayi ya zauna kan kujerar da take yaga ta dan ja gefe, batareda ta kallesa ba tace "ina kwana" "lafia ya amsa mata" sai kuma duk sukayi shiru, wayarsace ta hau kara ya cirota daga aljihun sa tareda daukar kol in da sauri ganin Nani ce ke kira,gaisheta yayi sannan naji yace "toh Nani mun gode, tashi yayi yaje ya bude kofar ya karbi abincin da ta aiko musu ya aje kan dining, dan daga muryansa yayi yace "ki zo ki samun abinci pls, tabe baki tayi tareda tashi a zuciyanta tana mutum ba kuturu ba amma komai sai ya sa an mishi,  chips da pepper soup in kayan ciki ta zuba mai sai kuma kunun madara, tana gama aje mai ta juyo zatayi daki yace "ke fa? "a koshe nake" ta basa amsa sannan ta wuce dakinta. Wanka tayi ta shirya tareda yin light mkup ta fito fes abunta, kimtsa dakin tayi sannan ta fito ta dan kimtsa palon, dining in ta nufa dan kwashe abunda yayi amfani da su taga ba komai sai flasks in, kitchen ta nufa ta ga har ya wanke kwanukan, cup ta dauko ta fito ta zuba kunun ta zauna tana sha dan ta fara jin yar gusau, kamshin turaren da ya bugi hancintane ya sata juyowa taga MK tsaye yana kokarin buttoning hannun rigarsa, bata ma san ta kura masa ido ba sai da ya dago suka hada ido ya sauke mata murmushi sannan tayi saurin dauke kanta tareda tsuke fuska, dining in ya nufo yace "Dear kinyi kyau sosai,wish i can spend d whole day with you bt i hav to go out dan nasan yanxu yan zuwa yini zasu fara zuwa, tk care of urslf for me ko ya fada tareda shafa gefen fuskarta sannan ya fice, baki bude ta bi bayansa da kallo, yana fita taja wani uban tsaki tareda jin takaicin kalamansa da kuma shafata da yayi.

Rayuwar Ya maceWhere stories live. Discover now