Babi na biyar

1.1K 57 0
                                    

🤦🏾‍♀         *Rayuwar*        🤦🏾‍♀

          🙆🏾       *'Ya*    🙆🏾

🙎🏽            *Mace*              🙎🏽

Na Billy Ladan

♻ *EXCLUSIVE* *WRITERS*

*08*

_This page is for U Sadiya Ibrahim Gombi(Dee Dee)._
_Baby kinyi ne a rayuwa,irin totally,Allah ya kara dankon zumunci ya bar so da kauna_
*LUSVM*

Tafia take a hankali yayinda hankalinta sam bai jikinta dan tayi nisa cikin tunani bata ma ji horn da ake mata ba, cikin zafin nama da jin haushi MK ya figi motar da niyar bugeta dan ta kular da shi, ji tayi an fisgota ta koma gefe sai sannan ta dawo hankalinta,juyowa tayi dan bawa mai motar hakuri yana ganin cikin idonta ya hau surfa mata zagi dan dama da idonta yake ganeta sabida kullum cikin niqab take "Banza wawiya kawai kina tafia sai kace an toshe miki kunne, wlhy kinci sa'a da sai in takeki kuma in take banza stupid kawai, kafun ma Sabbura ta budi baki ya ja motarsa yayi gaba, juyowa tayi gun wanda ta jata taga wata yar tsohuwace ta gode mata sannan ta cigaba da tafia a zuciyanta tana shirya kalamai da zata wa MK duk sanda suka hadu dan ita ta rasa gane meh ta tare masa da kullum sai ya yaba mata maganganu, ita damuwar gidansu ma kadai ya isheta balle yace zai zo ya daura mata nasa. Ji tayi ana sake horn ta dan ja gefe dan bawa mai motar hanyar wucewa, maimakon ya wuce sai taga an ja an tsaya, ji tayi ance sabrina, sanin shafiq ne kadai ke kiranta haka ya sata tsayawa tareda juyowa, shi din kuwa ta gani, sake ma juna murmushi sukayi sannan ya bude motar ya sauko, gaishesa tayi ya amsa sannan ya kalleta cikin so da kulawa yace " wia to my wifey? "Abinci zan kaiwa Abba a kasuwa ta bashi amsa, krban basket da ke hannunta yayi ya bude bayan motarsa ya sa sannan ya dubeta yace muje toh in ajeki, sai da ya bude mata ta shiga sannan shima ya zaga ya shiga.

Zaune suka sami Abba yana karatun Alkur'ani mai girma, yana ganinsu ya rufe ya aje tareda nuna musu wajen zama, gaidasa shafiq yayi ya amsa cikin kulawa dan sosai yaron ya kwanta mai a
rai. Abinci Sabbura ta miko mai ya dubeta cikin so da kulawa yace " Sabbura biyoni da abincin kikayi, murmushi tayi kanta na kasa tace "Abba naga baka karya ba ka fita shine na kawo ma, " Nagode Sabburahna, Allah yayi miki albarka duk suka amsa da amin, hadasu yayi duka yayita musu nasiha tareda cewa shafiq ya kula mai da yarsa sosai sannan ya sallamesu suka fice.

Sai da suka tsaya a MK plaza yayi mata sayayya sannan ya ajeta a gida tareda cewa zai zo da yamma.

Sai da ta ga motarsa ya tashi sannan ta juya zata shiga gida taga Baba Saude tsaye a zauren gidan tana mata kallon tuhuma, tahowa tayi ta wuce ta gefenta tareda gaidata, tabe baki tayi ta wuce cikin gida sabbura kuwa ta wuce dakinsu dan aje ledar da ke hannunta tareda rage kayan da ke jikinta ta dan kwanta.

Har bacci ya fara daukarta taji an tsaya a kanta, bude idonta tayi a hankali taga Baba Saude ce tsaye a kanta, cikin yanayin jin bacci ta tashi ta zauna yayinda Baba Saude ke bin duk jikinta da kallo tareda cewa "ai sai ki fito, an je an gama yawon banza an dawo taya ba za ayi bacci ba, kullum cikin hijabi sai kace saliha ashe duk na munafurcine Allah kadai ya san meh kuke aikatawa, hawayene ya fara bin kuncinta jin kalamar Baba Saude ke nan a tunaninta fitarta wani abun suka aikata da Shafiq, cikin kuka tace "wlhy Baba abinci na kaiwa Abba shine ya rage mun hanya kuma in baki yadda ba ki tambayi Abba, tabe baki tayi ta karasa shiga dakin tana cewa "ke dai kika sani, wa ya san ko Abban naki ma bakinku daya ne, ledar da ta shigo da shi ta bude ta dibi abunda zata diba ta fice.

Hijabinta ta sa ta fito taga Baba Saude na zaune kan tabarma har ta bude chocolate da ta dauka a ledar tana mai cin yaushe gamo, ganin razor da ke gefenta ya sata karasawa bata ma tambayeta meh zatayi ba dan ta sani ta bude  rezar ta fara gyaran farcenta

Rayuwar Ya maceWhere stories live. Discover now