Babi Na Shida

861 48 0
                                    

🤦🏾‍♀         *Rayuwar*        🤦🏾‍♀

          🙆🏾       *'Ya*    🙆🏾

🙎🏽            *Mace*              🙎🏽

Na Billy Ladan

♻ *EXCLUSIVE* *WRITERS* *FORUM*

*11*

bintladan.blogspot.com

Auren soyayya mahaifinki da ummanki sukayi duk da bamu so auren ba ganin Abbanki ya nace ya sa muka hakura muka yarje masa. Shekara biyu da aura nsu amma ko batan wata bata taba yi ba hakan yasa yan uwa aka tada hankali akan cewa lalle sai ya kara aure amma kememe yaki dole muka hkura muka barshi, a shekararsu na uku ta samu ciki, murna a wajenmu ba a cewa komai, bayan wata tara ta haifo Suwaiba. Anyi murna sosai da haihuwarta duk da munso ace namiji ta haifa.

Bayan shekara ta sake samun ciki hakan ya sa mukayi watsi da zancen kara aure, duk muka kwallafa rai muna sa ran namiji zata haifo mana, bayan wata tara ta sake haifo mace aka samata suna Saliha, an dan yi murna amma ba sosai ba.

Cikin kankanin lokaci ta sake samun ciki inda ta haifo shamsiyya nan yan uwa suka fara daga hankalin akan lallai sai ya kara aure dan ga dukkan alamu mahaifiyarki yaya mata zatayi ta haifa, ba karamin tashin hankali abbanki da ummanki suka shiga ba dan suna bala'in son junansu, kuma Anna macece mai tsananin kishin mijinta hakan ya sa gaba tsakaninta da dangin mijinta dan mu mun kasa mun tsare akan cewa lallai sai ya kara aure shi kuma yace bazaiyi aure ba dan yana sonta kuma yana gudun bacin ranta.
Ganin da gaske yake ya sa na kirasa nace lalle sai ya kara aure in ba haka ba bani ba shi, hakan ya sa ya shiga cikin tashin hankali.

Ana haka ummarki ta fara laulayin ciki. Watarana ina zaune Abbanki ya zo ya sameni, yana kuka ya rokeni akan cewa in janye zancen aurensa har zuwa sanda Anna zata haihu, in Allah yasa ta haifi namiji toh za janyen zancen auren, ganin yanda ya durkushe gabana yana kuka yasa na yarda da batunsa.

Bayan wata tara mahaifiyarki ta fara nakuda, ranan gaba daya gidan aka tafi asibiti kawai dan ganin me zata haifa, muna tsaye cirko cirko gaban dakin haihuwa wata nurse ta fito tana tambayan yan uwan Anna, duk mukayi kanta muna tambayan meh aka samu, harara nurse in ta bimu da shi tana cewa "maimakon ku tambaya koh ta sauka lafia kun tsaya kuna tambayar meh ta samu, toh kayan jariri zaku bani, tana karba ta juya ta koma ciki bayan ta sa security yayi waje damu dan munyi yawa.

Can Nurse ta sake fitowa tana tambayan mijin Anna cikin rawar jiki ya karasa wajenta, ko me ta gaya mai muka ga ya juyo cikin sanyin jiki hawaye na bin kuncinsa yazo ya zauna yana zubar kwalla, gaba daya muka yo kansa dan tambayan ba'asi dan duk a tunaninmu ko mutuwa Anna tayi, da kyar ya tsaida kukansa ya shaida mana cewa Anna mace ta haifa kuma macen da ta haifa kece, da jin haka yan uwa aka fara cewa dama ai an fada ita mata kawai ta iya haifa, kan kace meh kowa ya watse dan anji mace ta haifa aka bar Abbanki sai kanwar mahaifiyarki.

A ranar aka fara shirin bikin Abbanki ke kuwa tunda ummanki ta ji haka ta dauki karan tsana ta daura miki dan da baki fito a mace ba da ba a fara zancen auren abbanki ba, hakan ya sa ko nono taki baki.
Sam taki kulaki ko daukarki bata yi, haka zakiyi ta kuka inba ni ko goggonki munxo mun daukeki ba bazata taba kulaki ba.

Anyi maganan duniyan nan amma sam taki ji,dole aka saki a kan madara yayinda kulawarki ya dawo hannun goggonki da ni.

Ranar suna Abbanki ya sa miki sunana amma yace za ana kiranki da Sabbura, a daren ranar aka daura auren Abbanki da Saude, wannan abu ya taru ya ma Ummanki yawa ga shi yayi aure ga kuma an sa miki sunana dan ji take batada makiyi da ya wuce ni, hakan ya sa ta dauki gaba da ni da sauran yan uwa yayinda take kara jin tsanarki a ranta.

Rayuwar Ya maceWhere stories live. Discover now