Babi na takwas

876 51 1
                                    

🤦🏾‍♀         *Rayuwar*        🤦🏾‍♀

          🙆🏾       *'Ya*    🙆🏾

🙎🏽            *Mace*              🙎🏽

Na Billy Ladan

♻ *EXCLUSIVE* *WRITERS* *FORUM*

*15*

bintladan.blogspot.com

_Ina Maryam Chiroma, ur page is here dearie, ina godia bisa kulawarki da kaunar da kike wa littafinnan, Allah ya bar so da kauna_

A hankali yake tuki duk dan kar ya tadata yayinda from tym to tym yake kai dubansa gareta a haka har suka iso kwanar da zai sadasu da gidansu Sabbura. Waje ya nema yayi parking, anguwar shiru kakeji dan duk mutane na gida kuma gari bai fara haske ba, hannu ya sa ya kai zai shafi fuskarta naga ya runtse ido tareda mayar da hannun, ya rasa taya zai tadata dan duk ya ji bazai iya tabata ba, wutar motan ya kunna a zatonshi in taga haske zata tashi,maimakon tayi hakan sai ya ga ta juyo fuskarta gefe ta cigaba da baccinta. Can dabara ta fado mai ya kama jikin hijabinta ya dan jijjigata sai gashi ta juyo ta fara bude idonta a hankali. Zaro idonta waje tayi tareda ja da baya hr ta dan bugi kanta a jikin glass, cikin nuna damuwa ya matso kusa da ita yana sannu bakiji ciwo bako, runtse idonta tayi yayinda jikinta ya hau rawa tace "dan Allah kar ka tabani ka taimaka ka maidani gidanmu" komawa mazauninsa yayi batareda ya kalleta ba yace "duba kiga a ina muke, a hankali ta bude idonta ta duba ta glass ta ga a anguwarsu take,kama mabudin motan tayi ta fara kokarin budewa ta jita a rufe, juyowa tayi ta kallesa idanunta fal hawaye, toh wai wannan bawan Allahn me yake nufi da ita ne, ji take kaman ta gaggaya mai maganganu son ranta amma tuno abunda ya kusa yi mata daren jiya ya sa ta soma yi masa magiya tana hadasa da Allah akan ya bude mata, jin yayi shiru bai tanka mata ba ya sa ta dago taga ya kura wa lips inta ido suna hada ido ya kawar da kansa yayinda ita kuwa ta sauke niqabinta, ita sam ta mnta a dage yake. Miko mata wayanta yayi ta sa hannu zata karba taji ya rike gam yaki sakewa, dagowa tayi suka hada ido tayi saurin kawar da knta tareda sake mai wayan, gyaran murya yayi yace "kiyi hakuri da abunda ya faru kuma ina fatan wannan abu da ya faru ya zamto sirrine tsakanina da ke dan na tabbata ko kin fada a gida ba mai yadda cewa nida ke ba abunda ya shiga tsakaninmu sabida haka zai fi miki in kin ja bakinki kin yi shiru, kallonsa tayi cike da tsana yayinda ta warci wayanta a hannunsa ta kauda kai tace " sai ka bude mun ai, ba musu taji karar bude motar,cikin sauri ta fita bata ko sake juyowa ba ta nufi gida da gudu dan gani take kaman zai sake biyota. MK kuwa tana fita ya jingina kansa a jikin seat in motar yana mamakin kansa "did he just tell her he's sorry? Abun da bai tabayi ba kenan wai bawa mace hakuri, ai wannan da boys nasa na nan ma sai su mai dariya, tsaki yayi tareda tada motarsa ya bar wajen.

Da gudu Sabbura ta shiga gidan garin saurin ta karasa ciki har tayi tuntube ta bugi kafarta tareda fadiwa a kasa. Tashi tayi tana dingisawa ta karasa ciki, zaune ta ga Abbanta da Hajia sun zuba tagumi, Abbane ya fara ganinta ya taso dan ganin ko wayace, yana ganinta ya dubi Hajia murya na rawa yace "Hajia Sabbura ce fa, cikin kidimewa itama ta taso ta nufo inda Sabbura ke tsaye taketa aikin kuka, rungumota tayi tace " Alhamdulillah Allah mungode maka, janta sukayi zuwa daki. Cikin kulawa Abba ya dubeta yace "baki ji ciwo ba ko, ina dai ba abunda suka miki, su waye suka daukeki Sabbura dan shari'ace kawai zata rabani da su, a jere duk ya jero mata wayanan tambayoyi ta rasa ma wanne zata amsa, samun kanta tayi da yi wa Abbanta karya, tana shesshekar kuka tace " ban san su ba Abba, kuma basu mun komi ba, hasalima wata aka sa su kamo shine aka samu matsala suka daukeni kuma tun jiya suka sakoni rashin mota yasa nayita takawa har sai yanzu da na samu na iso, ajiyar zucia duk sukayi Hajia ta dubeta tace "toh Alhamdulillah tunda basu tabakin ba, Allah ya dada kiyayewa bari in tashi in nemo ruwan dumi kiyi wanka in gasa miki kafarki dan nasan hala kin sha tafia, nan ta tashi ta wuce kitchen dan nemo ruwan yayinda Abba yabi bayanta, suna fita ta sauke numfashi yayinda ta ke mamakin karyan da ta shirga, toh me ma nata na wani karya duk dan ta kare wanda ya so ketamata haddi, ta san ko da ta fadi gaskia Abbanta zai yadda da ita kuma sai in da karfinsan ya kare amma ta san irinsu Baba Saude ba lallene ta yarda ba kuma sai ta bi anguwanni kaf ta gama yada karya da gaskia, tana cikin tunanin nan taji Abba sun dawo, Hajia da kanta ta matsa mata kafar har zuwa inda ta buge, sai da ake matsawa ta ji fa ashe lalle ta buge sosai dan daurewa kawai tayi bata saki ihu ba. Tana gama mata ta tashi tana dingisawa taje tayi wanka ta zo ta shirya ta kwanta dan rama bacci.

Rayuwar Ya maceWhere stories live. Discover now