Babi Na Hudu

1.1K 61 0
                                    

🤦🏾‍♀         *Rayuwar*        🤦🏾‍♀

          🙆🏾       *'Ya*    🙆🏾

🙎🏽            *Mace*              🙎🏽

Na B.A. Ladan

♻ *EXCLUSIVE* *WRITERS* *FORUM*

*07*

Firgigit ya tashi, ba karamin bugawa zuciyarsa tayi ba ganin Rufaida tsaye a bakin kofarsa, juyawa yayi gun Nicky da tayi zuru zuru da ido ya mata wani banzan kallo sannan ya tashi dan sa kayansa ficewa Rufaida tayi idonta na zubar hawaye.

Da sauri ya gama sa kayansa ya bi bayanta, hr ya kusa kofa ya juyo yace "I always tell u to liv as early as possible amma baki ji so dnt b here wen i cm bk n kr ki sake zuwa sai na nemeki, yana ficewa itama ta tattara kayanta ta fice.

A hnkali ya turo kofarta ya shigo tareda sallama, can kan gado ya gnta rakube fuskarta na kallon gefe amma hakan bai hanashi gano hawayen da ke bin kuncinta ba, cikin sanyin jiki ya karaso ya zauna gefenta tareda kwantar da kansa a cinyarta shima ya fara kuka haka sukayi tayi hr kusan minti biyar ba wanda ya budi baki, can MK ya dago ya share hawayensa sannan ya kai hannunsa kan na yayartasa ya rike "am sorry sis, pls kar kice zaki tafi ki barni wlhy sharrin shaidan ne, i promise u wnt eva see dt again but pls dnt liv me ya fada yana hawaye, juyowa tayi ta kallesa da jajayen idanunta tace "MK tafiya dole inyi but abu daya zan gayama wannan sabon rayuwa da ka dauka ba rayuwa bace n if ka ce zaka cigaba a haka toh ka sani ka fada hanyar halaka, da kasan girman wannan zunubi da kake aikatawa da baka yi ko mafarkin aikatasa ba, ina mai baka shawara ka yarda wannan rayuwa tun wuri in kuma ka ki wlhy ba ni ba kai kuma in na sa kafa na fice a gidannan bazaka sake gani ba ko daddy sai dai muna gaisawa ta waya, indai rayuwar da ka zaba kenan toh ka sani bani ba kai mantawa zanyi inada wani kani tana gama fadin haka ta juya mai baya tayi kwanciyarta tace " ka fita bacci zanyi, cikin sanyin jiki ya fice ya bar dakin dan tunda suke bai taba ganin bacin ranta ba sai yau kuma sanin shi ya ja ba karamin damunsa yayi ba, yau ma tsautsayi ya sa ya kawo nicky gida if not can gidanta suke haduwa su gama abunda zasuyi ya dawo kuma ba wanda ya san wannan rayuwar da ya dau wa kansa. Dakinsa ya wuce ya dauki key ya fice.

Gefen gidansu Sabbura naga yayi parking ya fito ya nufi shagon da ke kallon gidansu, samarin da ke wajen suna hangoshi suka fara "MK!!!! har ya karaso basu bar ihun sunansa ba, daya daga cikinsu ne ya tashi ya ja mai kujera ya zauna tareda mika musu hannu suka gaisa, daya daga cikinsu yace " ya dai MK naganka wani sukuku haka hop lafia, ajiyar zuciya yayi sannan yace "my guy bari kawai ina cikin wata yar damuwa ne but komai wl b normal soon, miko masa taban da yake sha yayi tareda cewa "zuka daya ya isa ya tarwatsa duk wata damuwarka, dariya MK yayi tareda kawar da kansa yace " ai wannan sai ku, ka san bn wannan harkar taku,ni kunga tafiyata ma kr ku cutar da ni da hayakin sigarin naku, ya tashi yana mika musu hannu daidai lokacin Sabbura ta shigo shagon da sallamarta cikin shirinta na islamia, ko kallon gefensu batayi ba ta siya abunda zata siya ta zo zata fice ta kusa cin karo da MK da ke kokarin fita, ja da baya tayi dan ya wuce shikuwa hararanta yayi tareda jan wani tsaki sannan ya fice, tabe baki tayi dan ta ganesa kuma shima ya ganeta dukda nikabin da ke jikinta, a zuciyanta tana tunanin irin wannan halin na MK, yau dai yaci darajar shigar da ke jikinta if not da sai ta gaya mai magana dan ta tsani tsaki a rayuwarta, har ta fito bai bar wajen ba yana tsaye jikin motarsa yana waya yayinda hannunsa ke kan kofar motar, kallo daya ta mai ta kau da kai ta cigaba da tafiyarta yayinda shikuwa yabi bayanta da kallo yana mamakinta ace mutum kullum kana wani lullube kanka, sai da ya daina ganinta ya shige motarsa yana mamakin tsayawa da ya yi yana kallonta.

*WANENE MK*?

*Muhammad Kabir Mansur* shine asalin sunansa  'da na biyu ga Alhaji Mansur Bilyamin, kyakkyawa ne ajin farko yanada tsayi sosai ga kuma haske da Allah ya mishi wane balarabe, su biyu iyayensu suka haifa shida Yarsa Rufaida, bayan su iyayensu ba su sake haifuwa ba, aiki ya kai Abbansu Korea inda suma a can suka yi yawancin rayuwarsu dan MK ma a can aka haifesa.

MK na da shekara goma mahaifiyarsu ta bar gidan, haka kawai suka wayi gari suka ga bata nan, dalilin haka Abbansu ya tattarosu suka dawo gida Nigeria.

Rayuwar Ya maceWhere stories live. Discover now