14

1K 55 0
                                    

*Rayuwar*       

               *'Ya*  
          
            *Mace*            

Na Billy Ladan

♻ *EXCLUSIVE* *WRITERS* *FORUM*

*33-34*

bintladan.blogspot.com

_Wannan shafin naki ne ke kadai *Hauwa Suleiman Muhammad*( *Ma Kawa*), ina sonki sosai tawan,Allah ya bar munke_

Tun ranar MK ya fita harkar Sabbura, in kaga suna magana toh ko Rufy na nan ko kuma ana side in su Nani dan sai sannan take zagewa tayi hiranta dan yanxu sun saba sosai.

Ganin yau har wajen 10 bata fito ba ya sa shi shiga dakinta,ganinta yayi kwance sai mirginiwa take yayinda numfashinta sai sama sama yake gashi ta hado gumi, yaye bargon da take kai yayi idonsa ya kai ga jini da ya bata kan gadon cikin sauri ya fita ya kira Rufy sai gata ta shigo da katon cikinta, da sauri ta hau dubata tareda mata wasu yan tambayoyi, rubuta masa magunguna tayi tareda miko masa tace yayi maza ya kawo, da gudu ya bar dakin dan zuwa sayo maganin.

Yana dawowa ta karbi alluran ta mata, a take ta fara jin saukin ciwon, cike da tausayawa MK ya xo ya zauna ya riko hannunta yana mata sannu, dubanda Rufy tayi tace "habibi hada Mata ruwan wanka ta kimtsa jikinta sai in mata allurar bacci dan ta samu ta huta, kai ya gyada tareda tashi, kafun ya fito har Rufy ta bar dakin, bai tsaya tambayarta ko zata iya tashi ba ya dagata cak, yayi toilet da ita bai damu da bacin da jikinta yayi ba, direta yayi a toilet in tareda wanke hannunsa ya fito tareda jawo mata kofar. Kafun ta fito har ya canza bedsheet in ya sa wani sabo,cikin sauri ta karasa shiryawa ganin baya dakin taje ta haye gado, turo kofar dakin akayi ta juyo suka hada ido,plate da ke hannunsa ya zo ya aje a gabanta tareda miko mata cup da ya hada mata tea, haka ya tasata a gaba yayita dura mata abincin har sai da ta ce ta koshi sannan ya fita dan kiran Rufaida, tana zuwa ta mata allurar bai jima ba kuwa bacci mai nauyi ya dauketa.

Ba ita ta farka ba sai wajen magrib, toilet ta shiga ta sake wanka ta fito ta shirya cikin kananan kaya riga da skirt sunyi bala'in amsarta ta fito dan zuwa kitchen dan yunwa take ji sosai. Tun da ta doso kitchen in take jin wani daddadan kamshi na tashi,ba karamin mamaki tayi ba ganin MK tsaye yana girki,jin motsi ya sa shi juyowa tareda sake mata murmushi, kawar da kanta tayi ta karasa inda yake tace "sorry na barka da aiki, murmushi kawai ya mata ya cigaba da aikinsa, hannu ta sa dan ta karasa amma sam yaki sai ma ja mata kujera da yayi yace ta zauna ya ma kusa gamawa, ba musu ta zauna yayinda from time to time take satar kallonsa yande yake komansa a nitse ba karamin burgeta yayi ba. Har ya gama ya juye a flask bata sani ba sai da ya zo ya sunkuya a gabanta ya dan lakuci hancinta ta dan firgita ta dawo daga duniyar tunanin da ta shiga, ta gs har ya kimtsa wurin, hannu ya mika mata ba musu ta mika mai nata ya dagota sukayi falo inda ya jera musu abinci a falo, dining ya aje nasa yayinda ita ya aje mata a kan carpet, bata damu da dalilinsa na yin hakan ba ta zauna ta ci abincinta, dan dadi Sabbura harda sude hannu. Zama tayi sukayi kallo tare can ta fara hamma ya dubeta yace "kije ki kwanta mana, tashi tayi ta mai sai da safe, maimakon tayi dakinta sai tayi kitchen, abincin da ya rage ta sa a fridge da niyar gobe in ta tashi zats duma tayi breakfast da shi.

Washe gari kuwa ta dan makara dan sai 9 ta tashi,wanka tayi ta shirya tareda yin light make up sannan ta fito dan yin dumamenta, kan kujerar kitchen in ta sami MK yana shan tea dan dama shi bai cika cin abu mai nauyi a break ba, gaishesa tayi ta nufi fridge, da karfinta ta bude   dan dauko ajiyarta taga wayam, dagowa tayi ta dubi MK taga hankalinsa ma bai wajenta, bin kitchen in ta fara yi da kallo ta hango cooler a kwando har an wanketa, ba dai zubarwa yayi ba ta fada a ranta, juyowa tayi ta kallesa taga har yanxu hankalinsa na kan wayarsa, abun da bata sani ba shine duk yans sane da abunda take kuma ya san meh take nema amma ya dake, gyaran murya tayi batareda ta kallesa ba tace "dama..........., sai kuma tayi shiru, batareda ya bar danne dannen wayarsa da yake ba yace "uhmm ina jinki, ji tayi kamar ta hakura dan kar ya rainata amma kuma baxata iya ba, " abincin da na aje a flask nake nema, ya ji ta fada, batareda ya dago ba yayi mata nuni da hannu, inda ya nuna ta bi da ido, a hankali ta taka taje ta bude microwave in ta ciro plate da ke ciki, bata san lokacin da ta saki murmushi ba, juyowan da zatayi taga MK ya kafeta da ido shima yana murmushi ya taso ya zo ya tsaya a gabanta yace "ko baki fada ba nasan abincin ya miki dadi dan mijin naki is a good cook, d smile on ur face says it ol so i wil tk dt as a compliment" yana gama fadin haka ya fice daga kitchen in baki bude ta bi bayansa da kallo tareda tabe baki, zama tayi ta ci abincinta tayi nak sannan ta fito ta gansa zaune da Rufaida. Cikin jin kunya ta karaso ta gaidata ta amsa sannan suka zauna suna hira.

Rayuwar Ya maceWhere stories live. Discover now