10

1K 63 5
                                    


*Rayuwar*

*'Ya*

*Mace*

Na Billy Ladan

♻ *EXCLUSIVE* *WRITERS* *FORUM*

*19-25*

bintladan.blogspot.com

_Wannan shafin nakune kawayen arziki_
*Hafsat Abuja*
*Meenah Adam*
*Pherty Mamadi*
_Da kuma ma sis from anoda momma_ *Maryam Sahaz*( *Novellas lodge*) _bansan kalaman da zanyi amfani dasu wajen gode miki ba,nagode sosai da kulawarki da soyayyar da kike nuna wa littafina,Allah ya bar zumunci, *LUSVM* guys_

Sabbura na kwance dakinsu yayinda haryanxu hawaye bai daina fita daga idanunta ba, wayarta ce ta hau kara, da yake yana kusa da ita hakan yasa ta ga wata bakuwar numba da akayi saving d SA sai dai ita tasan ba ita tayi saving ba, ture wayar tayi gefe ta cigaba da kukanta har wayar ya gama ringing. Sake kira akayi a karo na biyu amma ko kallon wayar batayi ba, Shamsiyya ne ta dago ta kalleta tareda cewa "Sabbura ba kirarki ake bane? "Barshi kawai ba sanin numbar nayi ba, ta bata amsa cikin muryarta da ya dashe dan kuka. Miko hannu shamsiyya tayi ta dauki wayar, tana ganin numbar ta gane ko wayene dan ita tayi saving, dan murmushi tayi sannan ta dauka ta karawa Sabbura wayan a kunne, juyowa tayi ta kalleta tana kokarin cire wayar a kunnenta taji muryarsa ya doki kunnenta, gabanta ne yayi mugun fadiwa jin daddadar muryarsa da ya so sata manta halinda take ciki yayinda take ji kamar ta san mamallakin wannan muryar, sallamar da ya sakeyi shi ya katse mata tunani ta amsa mai can kasa kamar dole aka sata tayi maganar, gaisheta yayi da hakuri sannan duk sukayi shiru, jinsa yayi shiru yasa Sabbura katse wayar sannan ta kai dubanta ga Shamsiyya tace "Adda ke kikayi saving mun numbar ko? Wayeshi? Ta tambayeta a jere, kai ta gyada tace "wannan wanda ya biya mana kudi da mukaje shopping ne, cike da mamaki tace "toh taya ya san an mana rashi? "Ni ma ban sani ba ta bata amsa,sai dai na tabbata ko wayeshi ya damu dake dan damuwar da yayi dake ne yasa har yake bibiyar al'amuranki, yanxu dai tashi ki ci abinci dan rabonki da abinci tun safe sai kizo ki huta kukan nan ya isa haka, addu'ar mu kawai take bukata. Sata a gaba shamsiyya tayi taci abinci sannan ta sata ta haye gado ta kwanta ta fice ta barta a dakin.

A haka har aka karashi zaman makoki, bayan sati daya su shamsiyya suka koma makaranta suka bar Sabbura da kewarsu musamman ma shamsiyya da suka zamto tamkar aminai.


Sabbura ta dawo abun tausayi tun bayan rasuwar Hajia, dan yanxu an koma gidan jiya, aikin gidan duk ya sake dawowa hannunta. Tayi kewar Hajia sosai dan tasan rashinta kesa ake mata hakan.

A haka har suka zana waec wanda hakan ya tabbatar da kammala secondary da tayi. Walima aka shirya musu na gama makaranta wanda ya zo kusan lokaci daya dana saukarsu.

Ranar walimar makarantarsu ta ci ado cikin daya gown da MK ya bata ash color da aka mai ado da pink and black stone, tana cikin shiri taji muryar Shamsiyya, ba karamin dadi taji ba dan dama taso ace wani daga gida yaje mata. Ita ta mata kwalliya ta mata rolling ta fito fes abunta, wayar Sabbura taja ta fara daukanta hoto kafin sukayi selfie, sunyi bala'in kyau. Batareda sanin Sabbura ba shamsiyya ta kunna data ta zabi hotonta mai kyau a ciki ta sa a dp. A harabar gida suka hadu da Atika da ta zo dan rakata suka fice gaba daya. A bakin kofarsu suka tsaya suna jiran Shafiq dan shi zai kaisu, Atika ce ta dan matso tace "kawa nikam waye wancan da tun fitowarmu yaketa kallonki, juyowa tayi suka hada ido da MK da tun fitowarsu ya kafeta da idanu ba ko kyaftawa, sosai tayi mai kyau yayinda a ransa yaji dadin ganinta da kayan da ya bata a matsayin gift, dauke idonta tayi daga nasa tace "ban sanshi ba" dan tasan kadan daga halin Shamsiyya da Atika sai su je su rufesa da bala'i in ta gaya musu ko shi waye. Suna ganin motar Shafiq suka karasa inda yake, suna isowa yayi saurin sauka suka gaisa tareda zagaya ya budewa Sabbura yace "bismillah wifey" daria su Shamsiyya sukayi suna tafawa sukace toh mu bari mu shiga tunda ba mai bude mana, sosa keya yayi shima yana dariyar. Sai da ta shiga ya rufo kofar sannan ya zagaya shima ya jasu suka bar wajen. MK kuwa tashi yayi cikin bacin rai shima ya bar wajen.

Rayuwar Ya maceWhere stories live. Discover now