11

951 59 0
                                    

Rayuwar*       

               *'Ya*  
          
            *Mace*            

Na Billy Ladan

♻ *EXCLUSIVE* *WRITERS* *FORUM*

*26-28*

bintladan.blogspot.com

_Wannan shafin nakune manyan matan *EXCLUSIVE*_
_My aminiyas_ *UmmuKhady*
*HumyLuv*
*Ermeenart*&
*Queen Bee Marafa*
_Allah ya bar zumunci, ya dada hada kan yan *EXCLUSIVE*,ina muku fatan alkhairi a duk inda kuke_

Kallon da Shafiq ke binsu da shi ba karamin tsoratata yayi ba, cikin sanyin jiki ta karasa wajensa, juyawa yayi ya shiga mota ya zauna itama ta bisa ta bude daya gefen ta shiga ta zauna. Kife kansa yayi a jikin steering yayinda zuciyarsa ke tafarfasa saboda tsananin kishin ganin hannun MK akan na Sabbura, dagowa yayi yana mata kallon tuhuma yaga itama shi take kallo, kawar da kansa yayi yace "waye wancan da na ganku tare? Kawar da kanta itama tayi zata basa amsa taga MK ya tashi daga tsugunnen da yake hannunsa dafe akan kirginsa da ke bugawa da karfi kaman zai paso ya fito, a hankali taga yake jan kafarsa har ya iso gun motarsa ya shiga, sai da ya dan jima sannan taga ya tada motar ya bar wajen.
Juyo da kanta tayi da fuskantar Shafiq taga ya kura mata ido, zatayi magana ya daga mata hannu " ban son ji Sabbura, my eyes have seen enough sabida haka ban bukatar wani jawabi daga gareki, ba yau na fara ganinki da shi ba kuma a duk sanda na ganku nakan fahimci hankalinki na gushewa har sai ya bar inda kike, ko magana ake miki a wannan lokacin ba sauraro kike ba, na tabbata yanxu maganar da nake ma baki jini ba, na taba miki tambayar ko shi wanene a wajenki amma kin nuna mun baki sansa ba amma yau idanuna sun tabbatarmun da ko shi wayene a gareki sai dai nayi mamakin da har zaki iya hada soyayyata da wani har kina barinsa ya tabaki, dagowa tayi da idanunta da suka fara jikewa da hawaye tace "Shafiq ka san meh kake fada kuwa, zargina kake kome, taya ma zakayi tunanin cewa zan so wani bayan kai har in bari ya kusanceni ta fada cikin tsananin bacin rai, cikin bacin rai shima ya dubeta yace " ba zarginkine nake ba Sabbura akan idona naga hannunsa akan naki kuma tsayuwar da nake da kuma ganinki yanxu a gabana na hango wani abu a idonki gameda wannan yaron sai dai in boye mun zakiyi, hannu ta daga masa tareda cewa "Ya isa Shafiq, kalamanka na bata mun rai idan kuma ka cigaba zamu iya samun matsala nida kai, ban taba tsammanin zakayi questioning soyayyar da nake ma ba har ma kayi tunanin zan iya hada soyayyarka dana wani waninma mashayi, mazinaci wanda bai dauki sabon Allah abakin komai ba,a kullum ina gayama Sabbura taka ce kai kadai, mutuwa ce kawai zata rabamu, ajiyar zucia yayi tareda bata hakuri sannan suka dan taba hira ya fice.

A daren ranar iyayen wanda ke neman shamsiyya suka zo sukayi gaisuwa suna tafia Abba ya kira Sabbura ya shaida mata akan cewa ta gayawa Shafiq shima ya turo iyayensa, da murnarta ta koma daki ta dauki waya ta kira shi inda shima murnar yayi ya ce mata gobe Abbansa zai taso yana isowa zasuyi maganar, cike da jin dadin cewa sun kusa zama mallakin juna suka aje wayar. Sabbura na katse wayar ta kira Shamsiyya ta shafa mata komai, sun jima suna hira sannan suka aje wayar. Wanka tayi tayi alwala sannan ta haye gado ta kwanta, tana rufo idonta fuskar MK ta hango dafe da kirginsa, tashi tayi tana mai tunanin ko a wani hali yake yanxun, ganin tunanin na neman wuce misali ya sa ta tashi ta tada sallah.

MK kuwa da kyar ya iso gida, mai gadi na bude masa kofa ya koma ya zauna, ganin har kusan minti goma MK bai fito daga motar ba ya sashi tashi dan duba ko lafia, ganinsa yayi ya daura kansa a jikin steering yayinda hannayensa ke sake kai kace babu rai a jikinsa, kwankwasa mai yayi yaji bai amsa ba yayi yunkurin bude motar ya jita a rufe, da gudu yayi cikin gida dan shaidawa su Nani. A falo ya samesy suna cin abinci, yanda su ka gansa a firgice ya sasu tashi suna tambayarsa ko lafia, hannunsa na rawa ya nuna hanyar waje,da kyar bakinsa ya furta "alhaji karamine gashi can a mota kamar ba rai jikinsa" cikin Abba da Nani ban san wanne ya riga fita ba, gaba daya gun motar MK suka nufa suka fara yunkurin budewa amma taki buduwa dan ya rufeta ta ciki, ji sukayi mai gadi yace "Alhaji ku dan gyara", ganin abunda ke hannunsa ya sa suka basa hanya, da karfinsa ya kai wa glass in bugu sai gashi ya pashe ya sa hannu ya bude motar ya fara kokarin fiddoshi waje, tayasa abba sukayi suka kwantar da shi a wajen suka fara mai fifita, ruwa Nani ta debo ta shafe mai fuskansa amma ko motsawa baiyi ba, Nani ta dubi Abba da duk shima ya fita hayyacinsa ganin tilon dansa a kwance tace "Alhaji gwara muje asibiti" bai musa ba ya dubeta yace "shiga ki sa mayafinki kai kuma idi taso driver maza ya kaimu.

Rayuwar Ya maceWhere stories live. Discover now