Kai dinah ta daga mata momi tace ” amman ba ason kuka kinji kuka baida kyau ”
Momi ta kara riko fuskarta da kyau tace ” kuma in wani abu na damunki u cn fel free n tak 2 ur momi rght “?
Dinah tace ” yes momi ” , momi tace ” gud hau gado ki kwanta kamin akare hada muku break “,
kai kawai Dinah ta daga ta koma tsakiyar gadon momi ta kwanta tare da jan bargo ta rufa,
Momi ta sauke ajiyar zuciya ta tashi ta shiga bathroom,
Karfe 3:25 jidda ta shigo gidan,
saida ta fara shiga dakin momi ta gaisheta sannan ta wuce dakin dinah,
Tan tsaye jikin window dakinta tana rike curtains,
A hankali jidda ta dafata ” bestyyy “! Dinah ta juyo fuskarta dauke da murmushi ta rungume ta tace ” besty har kin iso “!
Jidda ta saketa tace ” aeh kin gama 4 ta kusa muje kawai kar muyi African time “, ta karasa maganar tana duba agogon hannunta!
Dinah tace ” owk bari na chanja kaya dan wannan tun dazu nasasu “!
Tana kaiwa nan ta nufi wadrope ta dauko wata atamfa brown mai ratsin fari, da farin gyale ta dora saman bed,
Jidda tace ” bari naje gurinsu nafisa kamin ki shirya ” kai kawai Dinah ta daga mata,
Ta tashi ta fice,
Dinah ta shiga saka kayan tana karewa ta shafa power da Lips gloss ta daura dan kwalinta ta dora gyalen saman kafadarta tana cikin sa takalmi jidda ta shigo,
Wani kallo ta mata tace ” gaskiya bestyy mijinki ya huta dube ki ba wani makeup kikayiba amman ki kin fito Mrs world duk kayan da kikasa sai sun miki kyau “,

YOU ARE READING
DEENAH
RomanceThe beginning of another life. suspicious, terrified, remorseful. DEENAH...! ®2015 NOT EDITED ⚠️