12:30 na bugawa dinah suka tashi lacca tare suka fito ita da kawarta maryam.
Kai tsaye wata balcony suka nufa har suka isa dinah wata tafiya take kamar marar lakka suna zaunawa maryam ta kalleta tace ” ni yau dinah sai na ganki shiru2 kamar mai damuwa “shiru dinah tayi sannan tace ” hmm a a ni babu abunda yake damuna kawai dai yanayi ne kinsan rayuwa wata rana sai a hankali ” maryam tace ” hakane Allah ya sauwake ” Dinah tace ” amin ” ta shiga duba takardun dake hannunta
Sunyi minti 10 a haka babu wanda ya sake cewa wani abu.
ganin haka yasa maryam ta shiga danne2 a wayarta can kuma ta kalli dinah tace ” dinah bari naje na karbo abu na dawo ” kai dinah ta daga mata tare da murmushi itama ta mayar mata da murmushi ta tashi.
Kallo dinah ta bita dashi saida ta bacemata da gani sannan ta kawarda fuska tana sauke ajiyar zuciya.
Batayi minti 5 da tafiyaba wani yaro ya nufo dinah rike da leda a hannunsa daga ganinsa almajiri ne sai faman sauri yake har ya iso gurin da take.
Yanayin sallama ta jabura dan tayi nisa cikin tunaani ” wa alaikassalam ” tana amsawa ya mika mata katuwar ledar dake hannunsa yace ” wai gashi inji maryam tace komai kika gani ciki kici wai gatan nan zuwa “,
Karba tayi tana murmushi tace ” yauwa kamar tasan inajin yunwa na gode kaji ” ” tohm sai anjima ” ya juya da sauri ya tafiyarsa
Dinah ta aje takardun dake hannunta gefe ta dora ledar saman balcony,
Ta shiga kwancewa nonon ayaba ta fara fiddowa sannan ta ciro wata katuwar robar ice cream tare da pack din cake mai zagayen heart ta sake fiddo wata silver kula yar madaidaiciya mai kyau, da fork lake a gefenta an nade shi cikin tissues sai kuma bottle din ruwa.,
Shiru Dinah tayi tana kallon kayan kamar mai tunani sai kuma naga daga kafadunta alamar bata damuba tana murmushi ta shiga bude kular, farfeson kayan ciki ne romuwar tayi wani ja ga mai ya kwanta sai kanshi take,
Da sauri dinah ta warware fork ta tsoma ciki ta faraci. Sai lumshe ido take tana kasar baki tace ” uhnnn delicious ” saida taci kusan rabi sannan ta rufe kular.
ta bude ruwa tasha sannan ta yage Cardboard din cake ta fara ci sai kuma ta aje ta shiga bare ayaba.
Tana tana ci.
Dariyar classmates dinta ne ya dago hankalinta ta kalli inda suke Abdul-rashid ne da aliyu faruk sai kuma hindatu suna tsaye jikin mota sai dare2 suke.
Tsaki tayi ta kawarda fuskarta ta cigaba da cin ayabarta, jin basu daina dariyarba kuma dariyar tasu ta kara yawa yasa ta sake kallonsu taga ita suke kallo till suna dariya aliyu harda rike ciki. Murguda musu baki tayi ta jefa musu bawan ayaba, aiko kamar ita suke jira duk suka nufo.
Kusa da ita suka zauna kusa da ita aliyu da abdul-rashid suka zauna faruk da hindatu suka zauna gefenta aka taka ta tsakiya.
Wani mugun hade rai tayi ta kwashe kayan ciyeciyenta ta maidasu gabanta. Abdul-rashid ya kalleta yana murmushi yace ” tun dazu nake ta nemanki in tusa miki karatunki ” harara ta watsa masa tace ” to ce maka akayi ban gane ba hala mtsss ”
Abdul-rashid yayi dariya yace ” to ai nasan ba ganewa kike ba kuma ina laifina dan zan miki rihazal ” aliyu yasa hannu ya dauki ayaba yana fadin ” nidai kinsan basai kin taya minba ” harararsa tayi ” bafa tawa bace ta maryam ce kuma komai bata ciba “, hannu faruk yasa ya dauka yace ” kice abun namu ne maryam ai tawace ” ta dan sha mur tace ” kaifa faruk yayana ne kuma wanda nake ji dashi dan haka inajin kunyarka ” hindatu tace ” ai dama dole kice kina jin kun yarshi tunda an kawo ga ci ” abdul-rashid yasa hannu ya dauka ya mikawa hindatu ya sake daukar wata yana shirin farewa yace ” ae wai wasa tare ci banban yar hadama kawai ji kanta ” duk suka sa mata dariya aliyu yace ” gaskiya kan dinah akwai rowa kuma fa bama ita ta sayaba na maryam dinmu ne qundaruwa kawai ” hindatu ta kalleta tayi fuskar tausayi tace ” ayyah dinah har kinban tausayi kowa ya raina ki dan Allah friends ku raga mata mana “
Dinah ta harareta tace munafuka kawai ai harda ke ” ta kalli Abdul-rashid ” wai miya kawo ku nan dan Allah ki ku tashi ku tafi ” abdul-rashid yana kokarin daukar cake yace ” to ai sai ki dauke mu ki mayar wannan cake dinma na masoyana kike ci mata abu kida bakima part din masoya fitinanniya kawai ” cije baki tayi tana harararsa tace ” waikai Abdul ba munyi fadaba kuma har muna gaba miyasa kayi min magana “? Ya kalleta yana dariya yace ” nima ban saniba wai ko wani abun kika minne dan sonki yana min yawa har fa kasa bachi nake ” duk suka kwashe da dariya.
Suna haka suka hango maryam tafe faruk yace ” yauwa gama sweetie nan zuwa muci abun sai mun koshi babu zancen rowa ” tabe baki dinah tayi ” kaidai kasani nidai inajin kunyarka tohm ” hindatu tace ” hmmm in fa kaji an kunya2 to akwai so aciki “.
Abdul-rashid yace ” haba to nifa kinsan fa ina sonta da yawa ” ? Dinah tayi murmushi tana girgixa kai tace ” kudai kuka sani wickeds din makaranta ” duk suka kwashe da dariya., daidai nan maryam ta iso fuskarta dauke da murmushi tace ” yau kuma liyafa ake mana a makaranta duk waya kashe mana kudi haka koda yake naga abdul kila masoyiyarsa ya sayo ma “?
Wani irin sannan jikikin dinah yayi jin abunda maryam tace duk da tasan ta saba yi mata wasa murmushi karfin hali tayi tace ” hmm kaji maryam bake kika aiko min dashi ba kike zolayata “?
Faruk yace ” sweetie zo nan ki zauna tun dazu wannan dinah take mana tsiya ” ta zauna saman wani dutsi tana fadin ” tsiyar mie sweetie “? Aliyu yace ” tun dazu da mun dan taba wani abu cikin kayan ciye2 sai tace naki ne tayi ta mana matsifa ” hindatu tace ” kinga fa harda cake dinki na soyayya ta ci ita da abdul ” maryam tace ” nifa ban gane abunda kuke nufi ba ” aliyu yace ” ke dan Allah mai kwakwalwar kifi ai duk daya kuke babu abunda kuke ganewa ”
Maryam ta bude ledar awarar da take hannunta tana fadin ” kai ai kana ganewa computer kawai nidai ga gala in zakuci ” duk suka sa hannu suka dauka banda dinah da tun dazu jikinta a sanyaye yake a hankali ta kalli maryam tace ” dan Allah maryam bake kika aiko da kayan nan ba"?

YOU ARE READING
DEENAH
RomanceThe beginning of another life. suspicious, terrified, remorseful. DEENAH...! ®2015 NOT EDITED ⚠️