Part 2

1.1K 60 2
                                    

🎀🎀🎀        🎀🎀🎀
               ❤❤ 
                  🎀

        *MATAR UBA*

     
      *By Miss_ayusha*



*🌈Kainuwa writers asso🤝*

    

            3⃣&4⃣


"Heedaya ki tashi dan Allah ki tashi kawai ki kira anty amina kinga jikin mami yana ta tsanan ta"

"Wai dan Allah adda Habi kamar baki san halin matar nan ba yanzu ko na kirata kinsan bazata zo ba"

  "Dan Allah ki jarraba watakil yau taji tausayin mu tazo tunda baba bayanan" to kawai ta amsa mata,

  "Assalamu alaikum,  ko amsa sallamar bata yi ba tace miye, mayya maiya kawoki d'aki na a wannan lokacin,
  "Anty dan Allah ki taimaka jikin mamin mu ne yayi tsanani ki taimaka mu kaita asibiti"
  "Kaji zancan banza zancan hofi da Allah fitamin a d'aki ta mutu mana miye nawa a ciki gwara ku nemo wanda zai kaita bani ba shashasha kawai"fita kawai tayi tana jin tsanar matar uban ta har cikin ranta, direct waje ta nufa auwal ta tarar a kofan shagon shi hakan yasa ta karasawa wurin shi,

  "Auwal dan Allah ka taimaka mukai mamin mu asibiti baban mu bayanan ga anty amina tak'i saurarana ma"

  "To shikenan maza ki shiga ku fito da ita" da hanzari ta karasa cikin gidan,

  "Adda habi ga Auwal a waje na jiran mu" d'agata sukayi da kyar suka fita da ita motan shi suka kalla a wurin hakan yasa su shiga da ita cikin motan Habiba na gaba sai Heedaya dake tare da mamin su basu tsaya ko ina ba sai GIWA HOSPITAL emergency akayi da ita yayin da suka zauna zaman jiran su dan likitoci sun dukufa a kanta,

   "Heedaya ga waya kira mana Baba yasan halin da ake ciki" wayan ta karba yanda tayi dialing numbern Baban su bugu biyu ya dauka, murya a rikice take magana

  "Baba muna asibiti jikin mama yayi tsanani" d'aga d'ayan b'angaran inalillahi ya shiga ambato "wani asibiti ne mamana" ya tambaya "Giwa Hospital" ganinan zuwa kawai yace kafin ya kashe waya, cikin d'akin likitoci sun bazama a kanta domin ceto rayuwar ta bugun zuciyar ta ya tsanan ta numfashin ta sama sama yake su kansu sun rasa mai zasu mata,

  "Doctor Amir bai kamata mu tsaya kuma ba kamata yayi mu sami wanda suka kawo ta dole sai an sa mata oxygen" sunyi na'am da maganar haka kuwa sukai waje yayi dai dai da isowar Baban su,

  "Doctor tsalha yan mata ina mahaifin ku?" A tare suka nuna Baban su

  "Alhaji ya zama dole sai an saka wa matar ka oxygen dan akwai matsala" Doctor kar a b'ata lokaci kuyi abinda ya kamata cikin d'akin suka koma inda suka saita komai kafin nan aka sa mata,

  "Abba dan Allah ya kace a saka mata oxygen"

  "Habiba ya zama dole tunda suka ce a saka mata hakan ya dace" suna cikin wanan maganr Dr Amir ya fito "Alhaji matar ka na bukatar ganin ka da yaran ta"da gaggawa sukayi cikin d'akin hanun ta gam suka rike,

  "Mami gamunan a gefen ki" ita din ma hannun su ta rike tare da na mijin ta,

  "Alhaji ku saurari abinda zan fad'a muku, " Habiba" na'am mami "ga Heedaya nan ki kula da ita kicigaba da hak'uri da halin ta sanan abu na biyu ina so ku cigaba da hak'urin zama da matar baban ku duk wani abinda zata muku hak'uri shine maganin shi, ke kuma Heedaya nasan halin ki na rashin hak'uri abinda nake son ki sani shine ki daure hak'urin nan shine maganin zaman duniya kinaji " mami dan girman Allah ki daina haka cuta ba mutuwa bace insha Allah zaki tashi,

  "Alhaji ga yarana nan dan Allah ka kular min dasu ka kare min mutuncin su banason wani mugun abu ya same su sanan ka cigaba da hak'urin zama da Rakiya nasan ko ba dade zata gane abinda take ba dai dai bane"

  "Murja banaso kina irin wanan maganganun da izinin Allah zaki tashi mu cigaba da rayuwar mu kamar yadda muka saba" hannuwan su tsaf ta had'e akan kirjinta ta daura su kafin kace me tuni ta fara salati nan ubangiji ya karbi abinsa iya rikice sun rikice da gudu Heedaya ta fita kiran Dr, Dr Amir ne kawai a wurin hakan yasa ta kasa magana sai jikin shi kawai data fad'a,

"Baiwar Allah" bata jira wani magana nashi ba take nuna masa kofar d'akin hakan yasa shi gane mai take nufi janyeta yayi ya rike hannun ta yanda suka nufa d'akin da hanzari ya nufa wurin mamin su nan ya tabbatar musu da cewa ta mutu wani uban ihu Habiba ta saki kafin tayi k'asa a zube da sauri nurses din suka dauke ta aka nufa wani d'akin da ita ita kuwa Heedaya sandarewa kawai tayi a wurin sai da suka zaunar da ita sanan baban su karfin hali kawai yakeyi kafin kace me yan uwa duk sun dauka Murja ta rasu tuni aka cika gidan fam da koke koke ga Habiba datake kwance, gawar aka tafi da ita domin a suturtata ya rage saura Heedaya da kanin baban ta dayake wurin Habiba, bayan mintuna Habiba ta bud'e ido a gadon asibiti sunan mami kawai take ambato nan dai uncle din nata yasa su a mota sukayi gida wanda Heedaya ko a batacewa sai dai ruwan hawaye dahaka suka kai gida.





Miss_ayusha💋

MATAR UBAWhere stories live. Discover now