Part 11

656 37 1
                                    

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

    *MATAR UBA*

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀


*By Miss_ayusha*


*🌈Kainuwa writers asso🤝*

           *2⃣1⃣&2⃣2⃣*



A cikin gidan Habiba aka dire Heedaya ya Ahmad bayanan wato mijin Habiba sae ita kadai suka samu.

"Bayin Allah meya sameta haka? "

"To muma dai a takaice bamu sani ba amma gatanan tai miki bayani mukam zamu tafi"

Godiya sosai Habiba ta shiga musu kafin suka tafi.

"Heedaya yanzu dawa kukayi fad'a haka har da kona kafa"

"Wallahi Adda Habi Anty ta saka ni girki fa kawai sai ga matar Dr Amir tazo toh nikuma fitowana kenan kawai naji sun rufeni da duka muka fara toh ruwan zafin da na fito dashi shine fa suka zubamin"

"Inalillahi to gaskiya Heedaya auran Dr ya haramta a gareki bazaki je ta kashe ki a banza ba"

"Adda Habi wallahi ni kuwa yanzu ne naji karfin son Dr kuma auran gaske zamuyi ki cire komai a ranki ma"

"Heedaya ki rufa min asiri ke kadai kika ragemin baya dake bani da kowa kawai ki hakura da auran shi"

"Adda Habi" kafin ta karasa magana wayar ta ya fara kara ganin habibin tane yasa ta dauka da hanzari.

"Habibi"

"Na"am habibaty kina ina yanzu haka? "

"Ina gidan Adda Habi" kit taji ya kashe waya"

"Adda Habi kiga dai ya kashe wayan"

"To Heedaya ki jira muga ikon Allah me kuma zaeyi"

Wayar Heedayan ne ta sake daukan ruri

"Abbana"

"Na'am princess kina ina haka? "

"Abba ina gidan Adda Habi"

"Bani Habiban"

"Abba"

"Na'am mamana"

"Ya jikin nata"

"Abba da sauki sosai dan Allah ya takai ta"

"To ki kula da ita sai nazo"

"To Abba"

Gidan Abban Heedaya.

Duk iya kokarin na ganin mazan sun buge kofar sun kasa haka suka hakura suka fita.

"Baiwar Allah ki fita yanzu ki barmin gida tun kafin muyi nawa nidake"

"Kedin banza kedin wofi" tsuka Kausar tayi taja gyalenta sai waje.

Sallama ake kofan gidan Habiba mayafin ta kawai ta sako tayo waje ganin Dr ne tare da abokan sa biyu yasa tace su shiga yayi dai dai da dawowan Ahmad.

Duk tare suka shiga gidan kowa nasan yaga Heedaya

"Sister"

"Na'am ya Ahmad"

Kasa magana ma yayi tsaban bakin ciki

"Habibaty"

"Na'am habibi"

"Ya akai haka ta faru"

Nan ta shiga kora mishi jawabi

" lallai Kausar she will pay for it"

Ran Dr Amir a bace suka fita kira Ahmad yakeyi amma ina Dr yayi nisa

Shima Ya Ahmad tambayan meya faru yayi nan Habiba ta maida mishi zance Allah wadaran halin Rakiya yayi nan ya farfarda ma yan uwa tuni gida ya cika anzo gaida Heedaya yan uwan Abban suma ba'a barsu a baya ba suma kansu sunje dubiya.

Gidan Dr Amir

Sanda suka isa yayi dai dai da fitowan Kausar daga cikin d'akin ta.

Tass Dr ya dauketa da mari ji kake tass ya kara bata wani ta dayan gefen.

"Kausar ke wace irin matace wata irin annuba ce ke baki jin abinda na fadamiki ba kenan ko"

Duka kawai Dr ya fara kaiwa Kausar da kyar su Dr tsalha suka banbareshi baiyi auni ba ya shiga kitchen ruwan zafi ya fito dashi take ya watsama Kausar a yanda ta watsama Heedaya.

"Kausar  nagaji na gaji da halin ki kafin na dawo you make sure kin barmin gida na ki tafi can na miki saki daya"

Ihu Kausar ta shiga kwalawa tana kiran Amir amma ina ko ta kanta bai biba ya fita abinshi.

Mamanta kawai Kausar ta kira ta sanar da ita abinda ya faru.

"Jar uba shi Amir din ne yayi miki haka ki jiramu gamunan muna tahowa yanzu tare da yayunki"

"Toh mummy"



Toh anya za'a kwashs yar dadi kuwa ku cigaba da bina jin ya zata kaya.



Bani da charge kuyi manage da wannan dan Allah.





Miss_ayusha💋

MATAR UBAWhere stories live. Discover now