Part 19

589 24 0
                                    

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

    *MATAR UBA*

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀




*By Miss_ayusha*




*🌈Kainuwa writers asso🤝*








           *3⃣9⃣&4⃣0⃣*



B'angaran Heedaya banda amai babu abinda take shekawa har sai da Amir yayi mata allura sannan aman ya tsaya daganan kuma bacci ya sunkuceta shiko Allah Allah yake ta tashi yaji abinda yake tunani gaskiya ne ko yaya.




Suko Rakiya dasu Kausar an bazama anyi wurin boka a tsorace take dan tunda take bata taba takawa zuwa wurin wani malami ba sai a sanadiyar Rakiya da kawayen ta jeji kawai suke kutsawa harta gaji bataga an iso ba

"Wai dan Allah har yanzu ba'a kawo bane? "

"Daallah idan zaki tafi kizo muje duk badan ke ake tafiyar ba"

"Kema ai da taki bukatar gaskiya Rakiya bakida imani inhar mutum Allah ya hadashi da MATAR UBA irin ki ya shiga uku"

Wani dariyan rainin wayau Rakiya tayi

"Kausar kenan indai akan wannan 'yar iskar yarinyar ce sai yanda karfina ya kare dan sai na hanata jin dadin duniya har karshen rayuwar ta"

"Amma dan Allah me tayi miki haka da kika tsaneta? "

"Ke Kausar tambayoyin ki sun isheni haka mucigaba da tafiya kawai"

Haka suka ringa kutsuwa cikin lungu har daga karshe sukaji an saki wata irin tsawa wanda duk cikin su Kausar ce kawai ta tsorata harda yunkurin guduwa batayi auni ba sai ganin wani mummunan mutumi tagani gaban su daga ganin shi dama kasan ba zaiyi imani ba.

Kirari suka shiga yi mishi yanda daga karshe ya basu izini suka zauna

"Boka gagaraba dau munzo domin neman taimakon ne"

"Akan Heedaya ko? "

"Eh tabbas akanta ne"

"Ke MATAR UBANTA mai kikeso ai mata haka kema abokiyar zaman ta mai like so ay mata"

"Boka babu abinda nakeso ay mata face a rabata da mijina ta bar gidana ta barni da mijina yanda muke a da"

"Ke kuma MATAR UBANTA fa? "

Ai ni boka abu daya nakeso inma za'a rabata da duniya kamar yadda uwarta ta barshi to inaso"

"A'a kawai dai a rabata da 'yan uwanta ta shiga duniya tayi hauka"

Dariya ya kara kecewa da ita na rashin imani wannan aikin me sauki ne surkullan shi ya fara wanda daga bisani ya basu wani abu a hannun su

"Ke MATAR UBANTA wannan zaki samu rami a bayan dakin ta ki birneshi kuma kada kowa ya ganki, sannan ke kuma abokiyar zaman ta wannan a kofar dakin ta kawai zaki barbada data tsalaka shikenan"

Nan fa suka shiga godiya kamar me tare da zabgada mishi kirarinshi wani abu a leda suka ajiye sannan ya bace bat suka tafi.

"Ni yanzu Rakiya tayaya zan birne wannan abu"

"Ba wani abun damuwa bane yanzu mu wuce gidana in yaso da duhu ya shiga sai kije ki birne"

"Yawwa kawata ai haka nakeso shiyasa nake sonki wallahi" daga haka suka rabe Kausar da kawayen ta sukayi hanyar su sai Rakiya da falmata ma hanyar su.


"Kausar gaskiya wannan Rakiya ta gagara mata ba digon imani"

"Kedai barta ai in Allah ya hada ka da mata irin wannan ka gama yawo"

Gab sun kusa isa gidan ta suka sauka dan bazasu shigaba haka ko ta shiga cikin gidan kai tsaye sai part din ta.


Ta wurin su Heedaya kuwa ta farka yanda Amir yay mata wanka tsaf ya gyarata sannan suka zauna

"Habibaty meya sameki haka kiketa amai"

"Habibi nima bansani ba kawai yaune na tashi da ciwon zuciya komai bansan abu mai kamshi da yawa"

"Yaushe rabo da kiyi period"

"Last month ne ai kuma bana fadamaka ba"

Fita yayi ya siyo Pt akan ya gwada fitsarinta bai jimaba ya dawo kuwa

"Habibaty kije ki kawo fitsarin ki a zan gwada abu"

Ba gardama tayo ta dawo ta kawo mishi nan kuwa ya gwada ya tabbatar da ciki gareta tsam ya rungumeta a jikin shi

"Habibaty kin gama min komai a rayuwata ubangiji Allah ya miki albarka na kusa zama daddy"

"Habibi me kace? " ta tambayeshi cikin mamaki

"Yes you are pregnant"

Ajiyan zuciya ta sauke wanda tai hamdala tay godiya wa ubangiji

"Habibaty daga yau kin daina aikin komai me aiki za'a nemo miki duk wani aiki kin daina yin shi"

"Kai Habibi"sai kace wanda cikin yazo haihuwa"

"Koma miye habibaty kin gama duk wani aiki a gidan nan" yanzu tashi zakiyi ki gyara muje wurin Umma"

"Amma dai in mukaje ba cewa zakayi inada ciki ba ko"

"Kedai kawai ki tashi ki shirya" shirin mikewa takeyi wayarta ya hau kara  Addan ta tagani haka ta dauka da hanzarin ta

"Addana"

"Na'am Heedaya na sauka "

"Me kikace ta sake tambaya"

"Na sauka an sami namiji"

Ihu ta shiga kurmawa a wayan ashe bata sani ba har Habiba ta kashe wayar ta

"Habibaty meyafaru"

"Adda Habiba ta haihu namiji kaga sai mun fara zuwa gidan ko"

Eh ta bashi amsa ai da sauri ta shirya tsabar murna zataga baby ma ta manta bata rufe kofar taba suka tafi iyakacin na ciki kawai ta rufe nan suka tafi.

Tana kwance a daki ai tanajin motsin fitar shi dan ta dau shi kadai ya fita yasa tayi part din Heedaya aiko ganin batanan yasa ta barbade dukkan kofan da maganin nan kuma ta kira Rakiya akan yakamata suzo dan basunan sun fita

Ba'a jimaba kuwa suka iso nan ta birne abu batare da kowa ya ganta ba ta bar wurin sai suka tafi zuciyan ta na cike da farin ciki.

B'angaran su kuwa sun isa gidan Habiba yanda sukaga baby boy dinta tsaf mai kama da Ya Ahmad sosai suka mata barka sannan suka tafi sai gidan Abban Heedaya nan ma gaishe sa sukayi yanda yayi musu albarka haka shima suka tafi suna tafe suna hira irin ta masoya har suka kai gidan su Amir din a parlo suka tarar da Umma da Abba har kasa suka kai nan suka gaishe su wanda duk Heedaya takasa sakewa ganin haka Umman Amir tajata sukai daki.

"Ki saki ranki kinji ko ai nan ma gidan kune karkiji komai"

Suna cikin haka Amir ya shigo

"Umma Albishirin ki"

"Goro"

"Kin kusa ganin jikan ki"

Kunyar duniya rufe Heedaya tayi kusan ta Umman nashi ta koma

" yarinya ta wai hakane"

Kasa daga kanta tayi tsabar kunya haka Umman shi ta shiga nan nan da ita harta Abban Amir saida suka fada mishi sosai fa shima ya shiga murna haka Umman Amir ta hada mata komai da zai mata amfani sannan suka tafi.

Cikin motan ma sai hira da shewa sukye abinsu har suka iso gida

"Habibaty bari naje na siyo wani abu kinji"

Haka ta fita kawai sai cikin dakin ta dukkan maganin nan sai da ta tsallake su kanta ne yayi wani mummunan sarawa kawai zaman dabas tayi a zaune kafin kace me har tafara juye juye kamar an tsikareta ta tsala ihu nan kuma ta zabura sai waje tana tafe tana sushe sushe.



Wayyo Heedaya ta fada tarkon MATAR UBANTA da abokiyar zaman ta hmm muje dai zuwa *ALLAH ya raba mutum da mata irin su Rakiya*











Miss_ayusha💋

MATAR UBAWhere stories live. Discover now