Part 4

780 30 0
                                    

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
          
        *MATAR UBA*

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀


  *Story and written by*

        *Miss_ayusha*


*🌈Kainuwa writer's asso🤝*


           7⃣&8⃣



Sanda suka kai gida a cike suka sami gidan hakan ya k'ara tabbatar musu da lallai Mamin su ta rasu yan uwan ta suka gani hakan yasa aka zaunar dasu a wurin banda kuka babu abinda sukeyi, an kammala suturta gawa yanda aka bukaci suyi mata addu'a akan gawar suka tsaya tuni suka zube k'asa suna wani mugun kuka addu'a ma kasa wa sukayi sai rungume gawar ma da sukayi suna kuka, shi kanshi baban su kukan yakeyi balle ya rarrashe su ganin zasu b'ata lokaci wani bappahn su ya janye su a wurin suka zauna dabas kamar ransu zai fita suma, da haka aka kai mamin su mak'wancin ta na gaskiya suko karban gaisuwa suka cigaba dayi duk wanda yaga Heedaya da Habiba sai ya tausaya musu bama 'ya Habiba gwanin tausayi basu ci basu sha sun zama kamar kurame ta b'angaran baban nasu shima hakan ne,

Sauran 'yan uwa basu tafi ba sai da akayi addu'an bakwai sanan gidan ya watse, yayar mamin su Hajiya Aina'u babu yadda bata yi ba ko mutum d'aya a bata amma baban su ya hana dan yadda yake jin yaran a zuciyar shi abin ba'a iya cewa komai, tunda ake karban gaisuwa Murja da 'yar ta suka kaura gidan gaba daya suka bari sai da akayi bakwai ne sanan suka dawo,

  "Alhaji Alhaji"sai da tayi kira biyu kafin ya firgita ya san da wata a kanshi "Rakiya lafiya dai ko" aifa dole ka tambaye ni lafiya ka tara yara sai kace wanda daga kanku aka fara yiwa mutuwa to ka taso ina son magana da kai" wani magana ne da baza muyi ta anan ba, indai bazaki fad'e ta anan ba to ki bace min dagani mara hankali kawai"lallai Alhaji wato tunda wanan b'aka mai bak'in aniyar ta rasu ka wani sakalo da mugun hali toh ai bazaka burge ni ba har sai sanda ka dawo da ita duniya,ire ire sunata gaba dama sun addabi jama'a,  Heedaya kallon Habiba kawai takeyi da idonta ya kad'a yayi ja ina bazata iya jure wanan mugayan maganganun ba tsaye ta mike kamar mai shirin dambe,

"Ke Rakiya kike da suna kowa toh albishirin ki in baki sani ba yau kisani, kar ki manta mamin mu ta samu kyawawan shedu kuma shedar duniya itace ta lahira, ke bakida labarin bayin Allah ne suke tafiya yanzu ai duk wani mara imani mai bak'ar zuciya sai ya jira tashi tazo muji ko za'a samu shedu kamar na mamin mu"

  "Ke Heedaya nice mai bak'ar zuciyar"zata sake magana Habiba tajawo ta "haba Heedaya yanzu har kin manta abinda mamin mu ta fad'a mana"Adda Habiba ban manta ba zan iya jure komai a cikin gidan nan amma banda abu biyu
Na farko naga ana zagin mamina ana muzan tata da mugayan kalamai,na biyu bazan taba bari a gabana wata banza tace zata zagar min babana dan nasan darajar shi watakil ita bata san nata ba" Heedaya har abin naki ya kai da zagi dago hannun ta ke da wuya zata mareta taji an rike shi gam,

  "Ke wace irin dabbar matace yanzu da har zaki daga hannun ki dake ta Rakiya maiyasa halin ki bazai canza ba maiyasa a koda yaushe kike san b'ata min rai, gaskiya da mahaifiyata tasan abinda zan tarar a auran ki da bata matsa na aure ki ba amma kowa da kaddarar shi na tawa a kanki ne, to inaso ki sani duk wani abu daza kiyi a gidan nan kada ki kuskura kice zaki dakesu dan zakiga fushi na, Habiba ku tashi mu tafi" a wurin suka barta tana ta banbamin da ruga zagi ko kala ba wanda yace mata a cikin su,

Kuka kawai takeyi yau mutuwar mamin ta sabuwa ta dawo mata,

"Mami maiyasa kika tafi kika barmu a irin wanan rayuwar maiyasa mutuwa baki had'a dani ba" haba Adda Habi yanzu dan Allah maiyasa kike haka idan mutuwar ta daukeki ni kadai zan zauna kenan a wanan kuntaciyar duniyar dan Allah ki daina fad'in haka, da kyar suka lallame ta tayi shiru daganan bacci yayi gaba da ita,

  "Babana dan allah kayi hak'urin abinda na aikata dazu" Heedaya
dole zakiji ba dadi akan maganar da take fad'a amma inaso ki dinga kai zuciyar ki nesa kinaji" eh abba "Allah ya muku albarka" amin ta amsa shi abinci kawai ta shiga daura musu dan tasan mahaifin nata bazai wuce jin yunwa ba.


 



Miss_ayusha💋

MATAR UBAWhere stories live. Discover now