Part 14

667 31 0
                                    

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

   *MATAR UBA*

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

  *By Miss_ayusha*


*🌈Kainuwa writers asso🤝*

          *2⃣9⃣&3⃣0⃣*



          
B'angaran Kausar abin duniya ya isheta ga bakin cikin auran da Amir zaiyi ga kuma har yau baizo ya dubata ba haka yasa ta saka wa Mamin ta kuka akan Amir yak'i zuwa.

"Kiyi shiru hakan nan yanzu zan kirashi yazo dama akwai maganar da zamuyi"

"Mami dan Allah yanzu kema so kike yayi auran"

"Kausar shifa mijin mace hudu ne so miye na d'aga hankalin ki kowa zaman ta zatayi ki nutsu kisan me kikeyi fa kinaji ko"

"Yanzu shikenan duk an daina sona a gidan nan amma har ake goyon bayan shi"

"Banda abinki Amir bafa shi ya ganki yake so ba ke kike sonshi kuma sai da na fada miki zaki fuskanci abubuwa da dama amma kika ki to yanzu me kuma zan miki abu daya ne ki kwantar d hankalin ki kuyi zaman ku lafiya"

" wallahi bazata sabu ba har ga Allah"

"Ke kika sani wannan ya rage naki idan kikayi abu ya sakoki gabadaya damuwar ki tunda bakijin magana"

Wayarta kawai Mamin Kausar ta dauka tai kiran shi take yace mata yana zuwa aiko ba'a fi minti shabiyar ba sai gashi a parlon suka zauna dan Kausar tana daki ita.

"Ina yini Mami" lafiya lau Amir ya aikin dai? " alhamdulillah"to masha Allah kasan mesa nai kiran ka" a'a

"Amir so nake ka fadamin duk damuwan ka da Kausar wani irin zama kukeyi"

"Mami lafiya lau muke zaune"

"Kaga bansan shashanci maza inajin ka"

"To gaskiya dai Kausar bata daukeni a bakin komai ba magana ma wannan nayi mata baji takeyi ba hasalima wannan girki batayin shi sai lokaci zuwa lokaci duk dai irin haka"

" ka tabbata irin abubuwan da takeyi kenan" eh Mami to Allah yay maka albarka da har irin zaman da kukeyi kenan baka taba kawo kukan ta gidan ba ita kuma zan sameta"

"To Mami" zaka iya tafiya" saboda kunyar ido yasa shi tambayar ina Kausar din take tana daki shine answer ta Mami ta bashi kai kawai ya saka a cikin dakin.

Tana kwance tana waya da kawarta akan lallaifa tana bukatar taimako suyi gaggawan zuwa ya shigo nan kuma ta katse wayan.

"Amir" tayi kiranshi

"Ya kike ya jiki" bansani ba ai baka damu da sanin ya nake ba sanda Mami tai kiran ka da wancan shegiyar ce ai ka iya nan nakan kafa ka bita aikin banza kawai"

"Kausar ubangiji Allah ya shiryeki Allah ya baki lafiya ni zan wuce" kudi ya ciro ya ajiye mata nan yasa kai yayi waje take ya tafi

"Kausar yanzu dan ubanki har yana tambayar ki ya jiki kina masa gatsali kome yayi miki ai ke kika gawa kanki banza sauna kawai"

"Lallai ma ai zamu hadu ne bari su shafa suzo zasuyi bayani daga shi har ita dan ta kuduri komai zata iya aikatawa akan wannan yarinyar kuma abinma sai an hada da Matar Ubanta fadar Kausar.

Bayan wasu lokaci sai ga su Shafa sun bayyano itada karimatu bayan gaida Mamin Kausar sukayi dakin da take.

"Subhanallahi Kausar meya sameki haka"

MATAR UBAWhere stories live. Discover now