Part 5

830 48 0
                                    

🎀🎀🎀        🎀🎀🎀
               ❤❤
                  🎀

         *MATAR UBA*



*By Miss_ayusha*


*🌈Kainuwa writer's asso🤝asso🤝*


             9⃣&1⃣0⃣

Kitchen Heedaya ta shiga yanda ta daura musu cous cous da vegetable soup tana kan aikin ne Rakiya ta shigo kitchen din

  "Ke Heedaya ina fatan dai abincin harda mu kike dafawa saboda Rahina batanan"

  "Sai ki jira ta dawo idan ta dawo zata girka muku amma ba girkin Heedaya zakici ba"

  "Heedaya wa ni kike fad'awa magana saboda ubanki ya daure maki gindin yin abinda kika ga dama to wallahi ki shiga hankalin ki"bata ce komai ba ta rab'a gefenta tai wuce war ta,d'akin su ta shiga jin wayan Addan ta yana ringing ta duba nan kuwa taga Ahmad ne da hanzarin ta ta dauka.

  "Ya Ahmad" na'am Heedaya" ina yini" lafiya kalau ya k'arin hak'uri" alhamdulillahi tace" ina mutumiyar tawa" tana bacci shine amsan data bashi toh ki ce mata ina nan zuwa da yamma ko harda Maryam zamu zo nan tace Allan ya kawo su lafiya sannan ta kashe wayan.kitchen ta koma ruwan girkin ta kara dan harsu zata girka ita bazata iya wani sabon abinci ba anjima haka tayi abincin ta tsaf hankalinta kwance sai mugun ramar datayi kamar ba ita ba d'akin Abban su takai mishi nashi yanda ta ajiye a gefen shi.

  "Abba ga abincin ya sauka" to Heedaya ubangiji Allah ya miki albarka" amin tace dashi .

GIWA HOSPITAL

Tun ranar da su Heedaya suka bar asibiti Dr Amir yake bin duk yadda zaiyi ya sake ganin ta amma bai san ta ina zai fara ba abokin shi ya samu akan suyi magana.

"Aboki dan Allah shin ba wani taimakon da zaka min akan wannan yaran da maman su ta rasu"

  "Dr bansan abinyi ba amma akwai abu d'aya muje cikin file dinsu ko Allah zaisa mu sami numbern wani daga cikin su" haka ko sukayi yanda suka bi file din alhamdulillahi Dr tsalha yace sanda yayi arba da wata number.

   "Aboki ga wata number matsala bamu san numbern waye a cikin su ba"

  "Aboki ai kawai kira zamuyi idan mukaji numbern namiji ne sai mu kashe" da haka suka kira wannan numbern.

  Tana zaune ga hoton Mamin su data saka a gaba tana gani hawaye na zuba a idonta taji wayan Habiba na k'ara ganin sabon number ne yasa taki d'auka sai da akayi kira biyu sannan ta dauka shiru tayi sanda taji anyi magana tukun itama ta amsa

"Dawa nake magana"

"Kina magana da Dr Tsalha"

  "Ayya mai wayan tana bacci sai in ta tashi zan fad'a mata"

  "A'a tsaya kiji bakune wanda kuka kawo maman ku asibitin giwa ba" eh mune" so dan Allah in bazaki damu ba inason ki mana kwataccen gidan ku zamuyi wa Abban ki ta'aziya ne"

  "Gidan mu yana kinkinau wurin masallacin algark'awi"ohk to shikenan sai kinji mu kit ta kashe wayan.

  "Heedaya kedawa kike waya haka?" Hmm wai Dr Tsalha wanda suka karbi Mami a asibiti zasuyi ma Abba ta'aziya ne"Allah sarki sai sunzo.

"Heedaya yunwa nakeji kin dafa mana abinci kuwa"

"eh tun dazu ke nake jira ai ki tashi muci kuma Ya Ahmad ma ya kira ki yana zuwa anjima kinji"to ta amsa mishi.

  Toilet fa fad'a tayo brush sannan ta fito suka ci abinci kafin sukayi d'akin Abban su.

"Abba" na'am Habiba yau Ya Ahmad zai zo toh Allah ya kawo shi lafiya amin ta amsa"

"Habiba kinga lokacin bikin ku bai wuce saura 2 weeks ba dan haka ni inaganin zaki koma gidan Aina'u ko Zainabu in yaso duk abinda ya kamata kuyi kwayi a can ko"

  "Toh Abba"akwai kuma Dr da suka duba mami sanda muka kaita asibiti sunce zasu zo maka ta'aziya" a'a to dama sunada numbern kine, a'a abba inaji dai a file din mu suka dauka toh Allah ya kawo su lafiya Amin dukka suka amsa mishi.

  "Heedaya maza kije ki kiramun Rahina"da toh ta amsa yanda tayi d'akin su Rahina sanda taje Maman ta kawai ta gani da kawarta Falmata.

  "Anti Rahina tazo inji Abba"

  "Badai wani munafurcin aka sake kitsawa ba dai dan nasan hali ansha a nono"hmm kawai tace sannan tayi waje.

  "Ke Rahina ki fito Abban ku na kiran ki"daga ita said leggings red dawani blue body hug a jikin ta tayi wurin Abban nasu ko sallama batay ba balle tace dasu sannu wuri kawai ta samu ta make ba abinda yay mata zafi.

  "Abba gani"

"Rahina inaso ki bani nutsuwarki nan ki ban hankalin ki, kinsan mai nake so dake" kai kawai ta girgiza

"Kinga bikin Habiba ya matso kuma ko ba komai 'yan uwanki ne abinda nake so dake dan Allah ku hada kanku kinji uwata duk wannan fitinan ku bar yinta kinaji" eh Abba insha allah ubangiji Allah yay muku albarka amin suka amsa dukkan su.





Miss_ayusha💋

MATAR UBAWhere stories live. Discover now