Part 7

830 44 0
                                    

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
            
           *MATAR UBA*

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

*By Miss_ayusha*


*🌈Kainuwa writer's asso🤝*


            1⃣3⃣&1⃣4⃣



Cikin gidan suka koma zama sukayi dukkan su yanda suka hau hira

  "Adda Habiba ina Ya Ahmad ne" cewar Nabila

  "Ah kaji min yarinya bakina da wayan shi ba sai ki kira shi ai" dariya dukkan su suka saka.

  "Adda Heedaya yakamata muje gidan su Jalila mu kai musu invitation card fa ko baza ayi komai ba ai za ayi walima dai kam"

  "Hakane"cewar Heedaya

Da gudo ya shigo d'akin yana kiran Adda Habiba.

  "Khalil ya akayi ne haka"

  "Kizo Ammi na kiran ki" tare suka tafi wurin Ammin nasu.

  "Anti gani" yawwa Habiba zauna kinji zaman kuwa tayi kusa da ita.

  "Habiba babu abinda zakiyi na bikin ne" eh Anti ni banason yin komai"

  "To shikenan ki shirya anjima Batula mai gyara jiki zata zo zaku fara kinji"eh ta amsa mata zaki iya tafiya wurin su Munnira ta koma banda shewa babu abinda ke tashi a cikin d'akin.

Bayan sallah isha'i duk suna zaune a parlo banda Habiba da take d'aki tana waya Batula ta iso gidan nan suka gaisa da Ammin su Khalil kiran Habiba ta aika ayi sanda sukaje ta gama wayar kenan tare suka fito.

"Habiba ga Batula nan tazo duk abinda ya kamata tai miki zatayi kinji toh ta amsa mata dahaka dai suka shige d'aki.

Washe gari aka fara gyaran Habiba inda su Munnira da Heedaya sun bazama gidan kawaye don kai musu invitation card suna hanya wayan Heedaya ya shiga k'ara bata bi ta kan wayar ba saboda ba suna sai number haka kawai ta barshi da niyar idan sun sauka zata kira.

  Sanda suka kai gidan su Jalila basu wani dade ba sukayi gidan su Adama da Bilki sauran catin suka bar musu akan su bawa sauran kawayen nasu da haka sukayi sallama sai gida dan suna da abinyi dayawa.

A gajiye likis suka koma gida ko minti batayi da zama ba sai ga kiran Abban su da azamanta ta dauka.

  "Abbana" na'am Mamana ya kuke?" Abbana muna lafiya ya gida yasu Anti da Rahina" duk suna lafiya Mamana ina fatan bakuda wata matsala ko eh Abba bamu da komai,yayi kyau bani"Habiba da gudu ta ruga ta kai mata.

  "Abba"na'am Habiba ya kike?" Abba ina lafiya ya kowa na gida duk suna lafiya" bakuda matsala ko eh ta bashi amsa to Allah ya muku albarka amin ta amsa nan sukayi sallama.

Wani kiran ne ya sake shigowa wayan ta tana b'ata fuska ta d'auka dan tuntuni ake kiran ta.

"Hello"

"Hi ya kike?"

"Ina lafiya lau"

"Kina magana da Dr Amir"

  "Allah sarki ya gida ya aiki?" Lafiya sai godiya to masha Allah.

  "Heedaya pls inason zamuyi wata magana"

"To amma kaga yanzu bana gida muna gidan Antin mu"

  "Bazaki iya mun kwatancan ba"

  "Unguwan sunusi Prp"owk idan nazo zan kira ki to shikenan da haka sukayi sallama.

Gida fa ya taru makil kannan Ahmad duk sun dawo gidan Aina'u 'yan uwa dadi Heedaya da Habiba dukwani b'acin ransu ya kau da fitinar Matar Ubansu.

B'angaran amarya idan kaga Habiba masha Allah abin sai wanda ya gani babu yadda Ahmad baiyi akan a bari yaga Habiba amma ankj sai dai waya harta Maman Ahmad ta dawo gidan Yayar tata ga 'yan uwan Abban su da ba'a barsu a baya ba su kansu sun bada gudu mawa dan duk abinda akeyi tare dasu ake.

  Yau takama Alhamis tunda suka tashi ake gyaran gidan basu da wani lokacin hutu masu yin lalle nayi masu kitso nayi kowa da abinda yakeyi.

Misalin karfe 4 na yamma Dr Amir ya kira Heedaya akan yazo unguwar hijabin ta kawai ta zura tayi waje da sallama a bakin ta ta karasa wurin shi.

  "Ina yini"

  "Lafiya klau Heedaya ya kike ya gidan?" Lafiya lau ina yayar taki?" Tana cikin gida ohh bazata fito mu gaisa ba" kasan amarya ce ba lallai su barta ta fito ba"au kice hidima kukeyi" wallahi fa shine ko gayyata babu"hmm kawai ta iya ce mishi.

  "To ubangiji Allah ya b'ada zaman lafiya"amin ta amsa mishi.

  "Heedaya in bazaki damu ba akwai wani important magana da nake so muyi dake pls"

  "Ehen inajin ka"

  Nan fa ya fara suburbuda zance ta inda yake shiga ba nan yake fita ba har ya kai aya.

  "To fa" pls Heedaya karkiyi rejecting d'ina hannun shi biyu ya hada wuri d'aya alamun yana rokon ta"

  "Kar ka damu bakomai Allah ya sa tarraya ta dakai alkhairi ne"

  "Alhamdulillahi gaskiya na gode sosai bani da bakin godiya a gareki"

  "Bakomai" tace dashi nan dai yayi mata sallama ya tafi itama ta koma gida.

Washe gari takama friday ranar walima kenan amarya ta hadu iya haduwa gown ta saka na wani pink material mai ratsin ash a jiki idan kaga Habiba bazaka gane itace ba.

  Arewa house angama decorating dukka wurin walima komai dasu tanada sun ajiye shi nan kuma fa 'yan kaisu walima aka tartafi yanda Malama Juwairiya tafara wa'azi mai ratsa jiki dan ya shiga mutane kusan magriba aka watse a wurin walimar.

   "Washe gari ta kama Asabar ranar bata k'arya yau ne ranar da za'a dauran auran Habiba Hamza da angonta Ahmad Hussaini yanda dunbin mutane suka hallarci wannan bikin bakin uban amarya yak'i rufowa kamar gonar auduga 'yan san barka sai zuwa masa akeyi haka dai aka gama taron daurin aure lafiya.

  B'angaran Habiba tunda taji an daura aure ta saki kuka ga Heedaya ma data mara mata baya kuka sukeyi kamar wanda mutuwa zata d'auki d'ayan su da kyar dai aka lallaba su sukayi shiru.

  Misalin karfe 5 'yan daukan amarya suka hallaro ga Abban amarya na jiran har cikin d'akin da Abban nata yake aka rakasu sosai yayi mata nasiha mai ratsa jiki sai kuka har taso ta saka shi kukan shima da kyar aka rabata da mahaifin nata suma b'angaran mata both yan uwan Mamin ta da Abban ta sun mata fad'a sosai ita haka dai suka sakata a mota yanda aka nufi gidan ta dake unguwar rimi.






Miss_ayusha💋

MATAR UBAWhere stories live. Discover now