Part 21

568 25 0
                                    

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

   *MATAR UBA*

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀




*By Miss_ayusha*



*🌈Kainuwa writers asso🤝*




         *4⃣1⃣&4⃣2⃣*


*Wannan shafin nakune duk masoyan wannan littafin MATAR UBA ina jin dadin addu'oin ku Allah ya bar kauna*



Haka take tafiya tana sushe sushe alamun sabon kamun mahaukaciyar nan sai dariya take yi gashi dai sai dariya kuma takeyi tana tafiya.

B'angaran Amir yana zaune ji yayi gaban shi na faduwa haka dai hankalin shi bai kwanta ba kawai mota ya dauka sai gida wani irin gudu yakeyi kamar zae tashi sama kitt yaji ya buge mutum inalillahi ya shiga ambato babu shiri ya diro daga motan gashi duhu ya shiga hasken wayar shi ya kunna dan ganin wanda ya bugi

"Habibaty" ya fada da wata irin  murya

Baiyi wata wata ba ya sunkuceta sai cikin motan shi gidan shi ya nufa yadda ya bude part dinta amma me ganin wani gari gari yasa shi shan jinin jikin shi kwantar da ita kawai yayi tare da kulle kofan bansan mai zai yi ba kawai naga ya nufi part din Kausar.

"Kausar ina Heedaya take"

"Bangane ina Heedaya ba ka bani ajiyarta ne" ta fada a irin ko ohon ta

"Kausar inhar kinma Heedaya wani abu toh wallahi zaki fuskanci fushi na ba dan kadan ba"

"Amir pls ya isheni haka ka tafi can kanemi Heedaya a yanda ka ajiyeta aikin banza kawai" wani wawan tsuka taja sannan ta juya masa kai

Fita yayi ya bar wurin amma me ba tafiya yayi ba yana labe yana jin abinda take fada

Aiko Amir na fita Kausar ta dau waya ta kira Rakiya nan ta shaida mata komai da komai duk abinda ta fada kuwa yana kunnen Amir abin karshe dayaji shine dariyan da ta sheke dashi.

Lallai Kausar bazai dau wani mataki yanzu ba dan bashi da evidence din abinda yaji ta fada jiki a sanyaye ya koma part din ta sukutum ya dauketa ya dire ta a mota sai gidan Umman shi duk anan Kausar tana jin fitan shi murna ya gama cikata.

Har sun rufe gidan Amir ya shiga horn haka mai gadi yana tangadin bacci ya fito ganin motan Amir yasa shi budewa da gaggawa bai tsaya sanya ba ya figeta sai cikin gidan a parlo ya direta dan karma tace zata fita ya rufe kofar yana ajiyeta ta tsala uban ihu wanda ya tashi Umman Amir da Abban shi.

"Alhaji mai nakeji kaman ihun mace"

"Hajiya nima kaina naji mu fita mu gani"

"A'a alhaji karfa wani mugun abun ne kuma"

"Insha Allahu ba komai muje"

Haka suka fita duk jikin ta a dadare yake ganin sunyi tozali da Amir yasata karasawa da sauri

"Amir" idonshi wanda ya kada yayi jazur ya dago ya kallesu ga Heedaya da sai shirin yaga kayan ta takeyi dabara kawai da yayi mata ya daure mata hannu.

"Amir magana akeyi bakaji ne maiyasa meta ba dazunan kuka bar gidan nan ba"

"Umma sun haukatar min da ita sunsu ta shiga duniya Allah bai amince ba sunzo rabani da ita amman Allah baiyi ba yanzu gashi Heedaya ta zama wata iri" wani kuka ya yanke da shi wanda sai da yaba iyayan nashi tausayi

"Amir suwaye sukai haka kai mana bayani ka bar kukan hakan"

"Abba Kausar ne tare da MATAR UBAN Heedaya Antyn ta kenan sune da kunne na naji Kausar tana waya suka shaidawa junan su mugun abun da suka aikata.

"Inalillahi wa ina illaihir raji'un yanzu Kausar har rashin imanin ta ya kai tabi boka"

"Umma Abba dan Allah ku taimaka kar kausar ta susuce gabadaya a kira Malam Ayuba ya hada mata magani "

"Amir karka samu damuwa gobe in Allah ya kaimu zan kirashi kai kuma kayi daki da ita dan kar a samu matsala "

Haka Amir ya sunkuceta da cizo da mitsinin da take mishi amman duk a banza dan kwata kwata baji yakeyi ba daureta gam yayi a jikin gadon sannan ya rufe kofar gefenta ya koma yanda take barbaza gashin ta tana kokarin kwance daurin da yayi mata amma ta kasa.

"Habibaty dan Allah hankalin ki ya dawo gareki kar ki barni a irin wannan rayuwar ya Allah nagode maka da batayi wani hannun ba" haka yayi ta surutai daga karshe ya tashi ya dauro alwala sallah ya shiga yi ya dade yana kai kukan shi wurin Ubangiji daga bisani ya shiga tofa addu'a a kofi da ruwa yana zuba mata har ruwan ya kare ya koma tofa mata da baki a haka ranar Amir ya kwana ido a bude abin tausayi.

Da misalin karfe 9 Abban shi ya kira Malan Ayuba nan yayi mishi bayanin komai

"Alhaji insha Allah zata samu sauki bari naje gida sai na hado mata magunguna "

Da haka yayi musu sallama ya tafi can ba'a dade ba ya dawo dauke da galoli a hannun shi

Bayani duk yanda zasuyi amfani dashi yayi musu harda wanda zasu dinga mata hayaki sosai suka mishi godiya wanda suka bashi kudi mai yawan gaske ya tafi.

Amir da kanshi yay mata wanka duk da cizo da dukan da take mishi nan ya bata dukkan wasu magani da yakamata a bata a lokacin duk da da kyar ya bata haka yazo zai saka hayakin tayo kanshi sai da taimakon Umman shi sannan ya saka hayakin a daki har ya gama.

Wayar shine take kara dubawan da zaiyi sai sunan Kausar wani wawan tsaki yaja sannan ya ajiye wayan bayan ta yanke ne Habiba ta kirashi.

"Amir idan kuna tare da Heedaya ka bata wayan na kira nata bata dauka ba gashi tace yau da sassafe zata zo "

"Wallahi Heedaya bata da lafiya wanda a halin yanzu ma bata gane komai sai sun batu ihu da dariya"

"Amir kana nufin Heedaya tayi hauka kenan"

"Kusan haka"

Kuka kawai Habiba ta barke dashi wanda a halin yanzu tana da tabbacin abokiyar zaman ta ne tai mata haka tana kukan ne ta sanar da Abban su iya tashin hankali sun shiga    kafin kace me dukka dangi fa ta dauka Heedaya ba lafiya amma duk abinda akeyi bai sanar da Rakiya ba iyakacin shi yace akan gidan Heedaya ba lafiya haka ta jajanta ya tafi harta Habiba da danyan jegonta suka dunguma sai gidan su Amir.











Miss_ayusha💋

MATAR UBAWhere stories live. Discover now