Part 9

770 33 0
                                    

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

       *MATAR UBA*

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀



*By Miss_ayusha*



*🌈Kainuwa writer's asso🤝*

              1⃣7⃣&1⃣8⃣




  Buga k'ofar d'akin ta shiga yi" ke munafukar Allah wallahi ko ki fito ko na illataki a cikin gidan tunda uban naki baya nan"jin abinda Antyn ta ke fad'a yasata fitowa.

"Gani Anty" maza miko min kudin da ubanki ya baki" make kafada tayi "zaki miko ko se ma taka ki" Allah sarki jiki na b'ari ta mika mata kudin.

  "Maza ki wuce ga kayan wanke wanke ki wanke su fita tsaf" jiki a sanyaye ta fita domin wanke wanke, haka ta wanke kwanukan tsaf sannan ta koma cikin d'aki zubewa kawai tayi tana wani irin kuka mai tsuma rai a wurin bacci yayi gaba da ita.

  Cikin bacci taji wayan ta na kara ganin Amir ne yasata dagawa.

  "Hello baby"

  "Na'am"

  "Ya kike?"

  "Ina lafiya lau"

"Ya gida dasu Abba?"

  "Lafiya lau, Abba yayi tafiya"

  "Masha Allah, pls inaso yau nazo idan har kinada time"

  "Shikenan sai kazo"

  "Yawwa baby bye"nan yayi hanging kiran, jin miryan Rahina na kiran ta yasata saurin fitowa.

   "Rahina" na'am Heedaya ya kike?" Lafiya na lau" ina kikaje ne na dawo baki nan?"

  "Gidan uwarki taje dan ubanki ke kuma shasha sauna da har kike ttambayan ta ya take mara hankali, ina damuwan ki da ita inbanda ke bakida tunani ma wuce kiban wuri a wurin" da sauri Rahina tabar wurin tana kunkunai cikin daki ta shige.

  "Ke kuma ki fito ki daura mana abinci saura na fito baki yi niya ba"

  "Anty amma fa zanyi bako"

  "Ina ruwana da bakon da zakiyi iya abinda na sani ki fito ki daura mana abinci kafin kwarton naki yazo"

  Wani bakin ciki ne ya tirnuke ta jin abinda Antyn nata ke fada kai kawai ta girgiza ta wuce kitchen tuni ta hada duk abubuwan da zata bukata ta daura girkin ta nan da nan ta gama abincin ta juye shi ta ajiye.

Wanka ta shiga ta cancada abinta yanda ta saka abayan ta tay rolling da gyalenta tayi kyau sosai dama abinka da farar mace hakan yasata kara yin kyau.

" Wai Dr ina zakaje ne da kake ta irin wannan shirin haka" Kausar na fad'a miki zani unguwa koko da wani yare nai miki ne?" Da hausa kai min amma naga shirin yaki karewa ne ai" taki akeji matsa min daga hanya"kin matsawa tayi tureta yayi yai wucewan shi wayan ta kawai ta dauka nunbern Salim tayi dialing ringing biyu ya dauka.

"Hajja ya akayi ne"

  "Salim kana inane haka"

  "ina gida ranki shi dade"

  "so akwai abinda nake son kai min yanzu Dr zai fita inaso duk inda yayi ka dinga binshi a baya har ya kai yanda zashi"

  "Angama ranki dade" tuni shima Salim ya hada machine dinshi yabi bayan shi.

  Kai tsaye gidan Dr tsalha ya fara zuwa a parlo ya tarar dashi tare da matar shi.

  "Dr ya kake?" Aboki ina lafiya lau "madam ya karfin jiki?" Alhmdllh Allah ya kara sauki amin ta amsa mishi.

  "Aboki sai ina zuwa haka ne" wurin mutumiyar mana" ahh kace lallai ka samu karbuwa "kai kam ka bari kawai amma ina tunanin ranar da Kausar zata san wannan maganar fa" karkaji komai bari lokacin yaxo toh shikenan ni bari na tafi"nan sukayi sallama ya kama hanya yayi gaba.

  Duk yanda Dr yayi sai Salim ya bishi a haka har ya iso kofar gidan su Heedaya Salim na gefe na kallon shi wayan ta ya buga batafi minti biyar ba sai gata ta fito tun daga nesa yae gifan ta da wani kallo kamar me karasowa tayi fuskarta dauke da murmushi shidin ma hakan ne.

  "Amincin Allah ya tabatta a gareka"

  "Amin babyna"
 
"Ya na sameki fatan kina lafiya"

  "Lafiya lau sai godiya" ya missing din sister
 
  "Wallahi kamar ka sani dan da yau ma zanje gidan ta"

  "Ba damuwa ai ba sai na kaiki ba"

  "Owk durling shikenan"

  Mota ya bude mata suka shiga kafin ya tada mota suka dau hanya.

  "Baby" na'am durling na tambayeki mana" inajin ka" shin zaki iya tare da matata" kaji ka da wani magana to aini zaman ka zanyi bana matar ka ba ko" hakane baby kinsan halin wasu matan ne ai, wasu kace kuma kasan halin kowa ya banbanta ko" tabbas hakane Allah ya zabar mana mafi alkhairi amin ta amsa hira suke cikin kwanciyar hankali babu abinda ya dame su.

Salim ya kwashe duk wani information ta kaima Kausar hankalinta in yayi dubu ga tashi tsoron ta daya kar Dr neman mata ya fara amma tasan me zata mishi bakomai da ita yake zance.

B'angaran su Heedaya kuwa sun kai gidan Habiba lafiya don har Dr shima sai da ya shiga cikin gidan domin gaisawa da Habiba da Mijin ta haka ko sukayi wuri Habiba da mijinta suka basu yanda suka sha soyayyar su babu abinda ya damesu Heedaya har ta manta duk wani b'acin ran dake ranta domin Dr ya mantar da ita duk wata damuwan ta.

  Sai da aka kusa magriba sannan sukayima su Habiba sallama siyayya yayi mata sosai sannan ya maida ta gida.







Miss_ayusha💋

MATAR UBAWhere stories live. Discover now