Part 15

627 28 0
                                    

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

    *MATAR UBA*

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀



*By Miss_ayusha*




*🌈Kainuwa writers asso🤝*




             *3⃣1⃣&3⃣2⃣*





Tsakanin masoya biyu fa abin sai cigaba ake samu soyayya suke ba kama hannun yaro yayinda Amir ya fara gyaran gida bil hakki da gaskiya hatta part din Kausar shima gyaran shi ake ita kuwa tana can tana shirin dawowa.

Alhamdulillahi Heedaya  ta warke tas abinta hakan yasa ta bar gidan Addan ta ta koma gida tunda Abban ta ya dawo sosai yake kula da ita dan baya son wani abu ya sake samun princess dinshi.

B'angaran Rakiya kuwa tunda Heedaya ta dawo bata shiga harkarta gudun kar ta sami matsala daga wurin Abban su gashi tunda ya dawo baiyi tozali da Rahina ba hakan yasa yau ya tashi da banbami alla dole sai ta dawo itadai Rakiya har ya gama batace uffan ba ta shige daki wayar ta kawai ta dauka dan kiran Rahina.

"Ke dan ubanki zaki jamin masifa ki dawo Abban ku na neman ki"

" gaskiya Mami yanzu bana kusa amma zan dawo" tsabar takaici kashe wayar tayi nan kuma ta kira falmata.

"Hajjaju ikon Allah"

"Kawata akwai damuwa dan yanzu harta kai Abban su yana neman Rahina kinga fadan da yayi tamin kuwa"

"Karki damu yanzu zan biya na karbo miki wannan maganin ki barbade shi da abinci zakiga aiki da cikawa" godiya Rakiya ta shiga yiwa falmata kaman abin arziki tai mata da haka sukayi sallama.

Wai waye falmata.

Irin 'yan barikin nan ne wanda sun sha bariki har sun gaji bata da yaro ko daya tun bayan 'yar ta data rasu sanadin accident din da sukayi da mijin ta tsabar fitina irin na falmata har mahaifiyar ta ta bar duniya bata daina fushi da ita ba wanda ala dole bakin mahaifiyar tane yake binta a halin yanzu bata da miji sai dai kawayen banza mata da kuma maza wanda suke sheke ayar su tare a ciki kuwa harda Rahina wanda falmata ke bala'in so a rayuwar ta dan tafi kwana ma a gidan falmatan akan wasu wuraren nata wannan kenan.

Batare da bata lokaci ba falmata tayi wurin malamin ta yanda ta karbo ma kawar tata magani domin rufe bakin shi akan Rahina tunda ko ba komai itama tana biyan bukatar ta da Rahina har gidan ta kaiwa Rakiya maganin yadda ta fada mishi a cikin abinci zata zuba mishi dayaci shikenan angama magana.

"Kai kawata gaskiya nagode miki amma yanzu ya batun wannan yarinyar ya za'ayi da ita"

" kedai ki bari so nake sai anyi bikin tukuna tunda yanzu ko me ya faru da ita za a zarge ki gwara idan ta tsallake tabar gidan yawwa kinga ba dan banzan da zai zarge ki kin gane ko" eh ta amsa mata.

Haka Rakiya ta barbade abincin mijinta da magani sannan ta kai mishi bai kawo komai a ransa ba kowa yaci wannan abincin.

Kausar fa tas angama shiri jira kawai take Amir yazo ya dauketa bashi ya tashi zuwa ba sai da akayi sallar magriba sanda yaje ta cika tayi fam kamar zata fashe.

Bata parlon Mamin ta ne kawai a parlon hakan yasa ya duga ya gaisheta sannan ta kira Kausar din gaba dayan su ta hade taiwa fada akan su zauna lafiya daga haka suka tafi.

"Yanzu Amir fisabilillahi muyi da kai tun la'asar zakazo amma sai yanzu saboda baka daukeni a bakin komai ba"

" sae kuma akace miki kar kiyi ma mutum uzuri ko"

"Wani uzuri zan maka wanda ba wurin wacce kaje sai 'yar iskan ka"

"Kausar kisan irin maganr da zaina fita a bakin ki banason iskanci kinaji ko" mtsww kawai tayi ayi dai mugani in tusa zata hura wuta" ko ci kanki bai sake ce mata ba har suka isa gida.

Kwanci tashi ba wuya ranaku nata tafiya lokacin biki na kara karotowa irin kayan da Amir yayi ma Heedaya abin azo a gani ne kowa sai san barka yake mata haka zalika kayan da yayi ma Kausar ma ba laifi sai dai ita da kawaye ke hure mata kunne.

B'angaran su Heedaya ta tattare ta koma gidan yayar Umman su acan ake gyarata wanda take shan gyara iri iri kullum cikin tsokana take wurin su Munnira sune masu raba I.V wa kawayen su dan Heedaya ba fita kuma ga Habiba itama cikin ta ya fito sosai sai san barka

Su kadai suka rage a daki daga Munnira Heedaya sai sauran yaran tare da gyaran jiki wayar ta ya dau kara ganin sunan shi yasata dauka.

"Habibi"

"Na'am habibaty pls ki fito wallahi yau inason ganin ki"

" kasan dai baza'a barni bako"

"Dan Allah kisan yadda zakiyi" to bani minti biyu

Haka Heedaya tai ta rokon Amina mai gyaran jiki ta barta ta fita amma bada sanin Antyn ta ba kawai ganin ta yayi.

"Masha Allah amincin Allah ya tabbata a gareki ma'abociyar kyau da kwarjini"

"Amin abin kaunata sanyi mai sanyaya zuciyar Heedaya fatan kana lafiya"

"Lafiya lau nake sarauniyar yan mata sai kewar ki data min yawa"

"Allah sarki angon Heedaya kwana nawa ne ya rage karka wani damu kanka na kusa zama mallakin ka har abada"

"To amaryar Amir Allah nuna mana ranar da alkhairi" amin ta amsa

"Angon Heedaya ina fatan kagama ganin Amaryar kar aje ana nemanta a gida"

"Ita kanta tasan bazan gaji da ganin ta ba sai dan kawai kar a nemen ta ne zan barta"

" to shikenan yanzu sai munyi magana kenan"

"Eh ya bata answer "

"Love you"

"Love yo too baby" daga haka ta shiga shima ya shiga cikin mota.

"Kai mutumin gaskiya kayi dacen mata inama nice na sami mata mai sona haka"fadar kamis wanda duk abinda suke akan idon shi

"Abokina kenan kaima insha Allah zaka zamu wacce tafi tawa ma kaji" Allah yasa abokina amin ya amsa.

"Yanzu ina zamu nufa? "

" wurin tela" shine answer da Amir ya baiwa Kamis haka suka dau hanya sai kawo dan zuwa wurin tela.





Kuyi manage da wannan banijin dadi ne wallahi idan na wartsake zaku sake jina.









Miss_ayusha💋

MATAR UBAWhere stories live. Discover now