Part 18

530 25 0
                                    

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

   *MATAR UBA*

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀




*By Miss_ayusha*




*🌈Kainuwa writers asso🤝*




        *3⃣7⃣&3⃣8⃣*







Haka ta fito da dan k'wali a hannunta tana dariya.

"Kuyi hak'uri na barku ku kadai wallahi Abba ne yayi kirana"

  "Ayya bakomai"

"To ku tashi ku tayani gyara sauran wuraren mana"

Haka suka tashi ba musu suka shiga tayata gyara sai anan ta tuna maganar Amir.

"Yawwa Munnira ga sako daga wurin Amir akwai wani abokin sa daya ganki kuma harga Allah sonki yakeyi bana wasa ba so shine yace nai miki magana idan har kin amince yazo ku daidaita"

"To Heedaya Allah ya kawo shi"

"Amin"

"Yawwa Heedaya nikam ina abokiyar zaman ki? "

"Tana part din ta"

"So dan Allah babu ruwanki da shiga harkartar duk abinda tai miki karki kulata plus"

"Insha Allah"

Haka suka tayata ta gyara ko ina tsaf abin sha'awa sai gab magrib suka tafi itako sai anan ta samu tai wanka Amir na yayi sai soyayyar su da suke zubawa.

Haka rayuwa ta kasance tsakanin masoyanan kullum cikin nunawa junan su so da kauna suke kowa bai san yaga ran dan uwan sa ya baci a b'angaran Kausar ma Amir yana iya bakin kokarin ta dan bata farin ciki amma ina Kausar kullum hudubar shedan dana abokai take dauka.

Kwanci tashi ba wuya auran Amir da Heedaya wata biyu kenan yayinda cikin Habiba haihuwa yau ko gobe.

Yau takama monday tsaf Amir yagama shirin shi dake a d'akin Heedaya yake shi dai bai san meya sameta ba amma kwata kwata kamar ba Heedayar shi ba haka dai ya barta ya tafi office shima dan ta matsa ne bai jima da fita ba sai ga kawayen Kausar sunzo dan tafiya gidan Rakiya

Zaman jiran Kausar sukayi akan ta shirya su tafi dan sun dau alwashi yau sae ta bar gidan nan.

Itako b'angaran ta banda amai babu abinda take kwara ba ta galabaita iya galabaita data ga de abin ba mai karewa bane ta kira Amir

"Habibi"

"Na'am Habibaty"

"Pls kazo gida ba lafiya"

Jin abinda tace yasa shi tashi a firgice ya kwashi key yama manta da Dr Tsalha a wurin

"Frnd lafiya kuwa? "

"Wallahi Heedaya ne wai ba lafiya bansan meya faru ba kaga barin tafi ina b'ata lokaci"

"Allah ya bata lafiya" amin ya amsa haka Amir ya figi mota sai gida

B'angaran Kausar tagama shiri haka kawayen nata suka tasa ta gaba akan sai anje anci ubanta haka kuwa duk suka shiga cikin d'akin ko sallama babu

Daga ita sai vest iya gwiwa dai dai fitowan ta a toilet kenan idon ta yana kallon mutane uku uku dan bawai ta gane su bane kawai dai ta gane maganar Kausar ne.

"La kawata kiga ma ko dai ciki take dashi"

"Kan bala'i lallai dana barar da cikin wallahi kuwa"

"Batayi auni ba taji saukan mari"

"Kausar nayi warning dinki akan Heedaya duk abinda ya sameta a gidan nan wallahi you will pay for it kinji na rantse marar hankali kawai kina biye wannan banzayen frnds din naki stupid kawai ko ki fita ko na tattakaki anan"

" Amir nika mara saboda wannan 'yar iskar"

"You better mind your tongue if not zan gwada miki rashin hankali a wurinan yanzu kuwa"

Kai kawai ta girgiza tabi bayan kawayen nata suna kara hure mata kunne basu dauki hanyan ko ina ba sai na gidan Rakiya a cikin napep din ma maganar suke har dai suka iso gidan suka sallami mai napep itama ta wurin ta sun gama shiri itada falmata dama su suke jira da isansu kuwa ta rufe gida suka dau hanya sai wurin boka.







Kuyi hak'uri wallahi sanda nagama typing tas sannan ya goge.










Miss_ayusha 💋

MATAR UBAWhere stories live. Discover now