Part 23

1.1K 43 2
                                    

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

    *MATAR UBA*

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀




*By Miss_ayusha*




*🌈Kainuwa writers asso🤝*





🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚

         *4⃣5⃣&4⃣6⃣*




Abinda ya basu mamaki bai wuce ganin 'ya yan da Heedaya ta haifo ba 'yan biyu abinsu a kasa da hanzari Umma ta karasa wurin ta bata bi ta kanta ba sai ta kan yaran daukan su tayi ta fita dasu shiko Amir kusan ta yaje yanda yadan tabata.

"Habibaty dan Allah ki dawo hayyacin ki ki dawo kiga babies din da kika haifa mana kuka kuma ya shiga yi kadan kadan"

"Habibi"

A firgice Amir ya kalleta nuskuta idon shi ya shiga yi anya ba mafarki yakeyi ba yaushe rabon dayaji muryar abin son shi

"Habibaty dan Allah kar ki sake komawa wannan halin dan Allah karki sake kinji"

"Habibi ka tashe to ji yadda ka daure ni kamar nayo sata"

"Idan bahaka nayi miki bane guduwa zakiyi ai shiyasa na daure miki hannu"

"Bangane ba"

"It's a long story yanzu ki tashi ki gyara jikin ki"

Da kanshi ya kaita har toilet ita dai tana mamakin ya ta ganta haka amma koma meye zai yi mata bayani ai

Umma ce ta shigo cikin d'akin

"Amir kardai ita kadai ka bari a toilet sai taje taji ciwo ko"

"Umma Heedaya ta dawo dai dai yau Allah ya karba addu'an mu"

Heedaya dake cikin toilet sae anan ta lura da ba gidan su bane sosai take sauraran abinda suke fada tunani ta fara to ko dai hauka tayi ne dan ga dukkan alamu taga haka tunda har daure ta sukayi da wannan tunanin ta shiga yin wanka.

Murna wurin Umma ba'a magana gashi ta gama gyara yaran tas abinsu sai zaman jiran Heedaya kuma da akeyi nan fa Umman Amir ta fada ma Abban shi aiko shi din ma murna ne ya gama cika shi Abban Heedaya da suke hanyar zuwa gidan Abban Amir ya kira yake sanar dashi hamdala ya shiga yi wanda bazai fadu ba.

B'angaran Rakiya abin fa ba sauki hauka takeyi wanda ta fita titi tana tambatse ihu ta da dariyan hauka takeyi haka take tafiya bata tsaya a ko ina ba sai kofar gidan su Amir ta b'angaran  Kausar ma haka abin yake duk kansu abu daya ne yake damun su

Cikin gidan kuwa murna farin ciki ba'a magana kowa sae nan nan yake da Heedaya kamar kwai haka aka maidata ana haka su Dr Tsalha suka zo har bakin gate Amir ya fito aiko tuni suka shige cikin gidan wanda tsaban mamaki ya rasa me zaiyi.

Cikin gidan gaba daya suka dunguma sae parlon anan suka tarar da kowa nan kuwa Rakiya da Kausar suka shiga tunawa kansu asiri kuka a wurin Heedaya da Habiba ba'a magana itakam da bata shiga sabgar ta amma har Kausar tai mata wannan cutarwar haka ko Abban Amir ya kira Umman Kausar nan da nan tazo taji abinda 'yar tata tayi kuka wiwi ta shiga yi kamar me tana ala wadaran da hali irin na Kausar itako Rakiya Abban Heedaya a take ya manna mata red card din ta itako da bata san abinda akeyi ba sai dariya take tuni ta kama hanyar fita aiko ba wata wata mota yayi gaba da ita nan fa mutane suka taru gidan su Amir akayi da ita amma fur Abban Heedaya yace a fita da ita mutane basu fi goma ba wanda suka sallaceta suka kaita.

Itako b'angaran Kausar rufeta sukayi a wani d'aki wanda Maman Kausar ta shiga rokon musu gafara da kyar da lallashi aka shawo kan Heedaya tace ta yafe amma Abban ta ko gefen su bai kalla ba.

Itama falmata ta wurin ta haka take yawo a titi tana sunbatu kowa ya ganta sae yayi wadaran da kalaman da take fadi.

A cikin gidan su Amir aka yayyafe juna inda su Abban kausar suka koma gidan su inda Amir da Heedaya suka cigaba da zama a gidan.

Haka rayuwar su ta kasance yanda akayi taron suna mace taci sunan Umman su Heedaya namiji yaci sunan Abban Amir haka rayuwar su take cikin kwanciyar hankali da nutsuwa.

Bayan Arba'in

Shiri sosai akai ma Heedaya tsaf Umman Amir ta gyarata da misalin karfe 8 Amir ya dau matarshi suka koma gidan su

Gidan su Rakiya Abban su ya saka Heedaya a gaba nasiha sosai ya mata nasiha aiko har gidan su Heedaya ta daura niyar zuwa da Habiba kuwa.

Ranar fa tsakanin Amir da Heedaya babu kanta ba'a magana sai wanda ya gani nikam ganin abin yafi karfina yasa nayi gaba na barsu.

Fanni Munnira fa abu ba sauki har an kamalla komai na auran ta jira kawai akeyi rana tazo

Ta wurin kawayen Kausar ma har gidan Heedaya suka zo neman yafiyar ta aiko ta yafe musu haka Rahina ma tazo duk sun nemi yafiyar juna daganan kuma zaman lafiya ya samu.

Sosai Rahina ta maida hankalin ta wurin neman mijin aure Abban su ma ya sami matar da zai aura kasancewar ba bikin yara bane yasa su aka daura auran nan babu wani bata lokaci kuwa ta tare.

Itama ta b'angaran Munnira an daura auran su da Kamis abinsu gwanin sha'awa.

Yaran Heedaya sai girma sukeyi wanda kowa ya gansu sai sun bashi sha'awa sosai da shak'uwa kuwa tsakain masoyan ba'a magana sai dai Allah ya kara dankon soyayya.



ALHAMDULILLAHI anan na kawo karshen wannan littafi wurin danayi ba dai dai ba ubangiji Allah ya yafemin.

Godiya gareku masoya wannan littafi a duk yanda kuke Allah ya bar so da kauna sai kuma Allah ya sake had'a mu littafi na gaba mai suna .........





Miss_ayusha💋

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Jul 29, 2018 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

MATAR UBAWhere stories live. Discover now