EL'MUSTAPHA
Haske Writers Association
Home of experts and perfect writersFertymerh Xarah💞
31
Jiddah ta dake xuciyarta wajen baiwa el'mustapha lokacin ta a rana, kulawa take bashi kamar yanda shima yake dar'dar da ita na ganin ya kauce duk wata hanya da xata saka ya batawa jiddansa.
'Washe garin ranar da uwani xata karbi girki, tun da sassafe aka tashi aka shiga kitchen, abinka da wanda bai saba shiga kitchen yayi girki ba sai dai ayi mata a kawo mata taci, duk sai ta rasa yanda xatayi bata san inda xata fara ba, sai ta kunna gas ta dora ruwan xafi tasan dole dai dasu ake hada tea,
Tasa yatsanta a baki tana tunani, ai taga kamar ruwan tea din suna da kayan hadi harda masu qamshi a ciki to menene ake sakawa bayan Lipton?
Ita abin kunyane yanxu taje gun jiddah ta tambayeta ai xata raina mata wayo musamman da ta tuna sanda suna gida jiddah ta taba yi mata fada akan ta daina kwanciya kawai ta riqa xuwa suna aikin abinci tare yanda xasu iya amma taqi, ita a ganinta tafi qarfin shiga kitchen.
Banan ta fado mata a xuciya, ta nufi sashen masu aiki,
'Yauwa banan xo muje ki tayani girki dan Allah, ta fada cikin murmushi tana kallon banan tunda ita ke nema.
'Anty uwani kaina yake min ciwo tun jiya kiyi haquri.
Masu aiki dan suna ciwon kai shikenan baxasu yi aiki bane ko me, kada ki bata min lokaci fa.
Kallonta banan tayi tana fadin, ana dole ne ai ba ke nakeyiwa aiki ba, in haka ne ki sami taki mai aiki mana ni anty jiddah kadai nake Ma aiki a gidan nan.
Ganin in batayi da gaske ba banan din baxata xo ba sai ta marairaice tana rarrashin banan dan kawai taxo, suna haka jiddah taxo, jin abinda ke faruwa ya saka tayiwa banan din magana akan taje ta kama mata.
Anan suka bar jiddah cikin masu aikinta,
Cikin lokaci qanqani suka gama komai, uwani aka yi wanka, wata doguwar riga ta saka gaba ki daya ta matseta ta fito da surar jikinta, qirjinta Ma a sama duka a bayyane, Arham ya fara ganin ta aikuwa da gudu yaje cikin gida yana kiran jiddah,
Momy xo kiga mamman anti uwani a waje,
Kallonsa jiddah tayi ko kadan hankalinta bai bata sauraren abinda yake fada ba,
Kai kuma daga ina haka, daddy ya tashi barci ne, ya gyada kai yana kallonta, tashi tayi ta nufi cikin gida.
Lah daddy dubi mamman anty uwani, aryan ya fada yana nunawa el'mustapha lokacin da suke fitowa.
Kallonta el'mustapha yayi daga qasa har sama sai ya dauke kansa dining ya nufa dai dai lokacin da jiddah ta shigo tare da arham,
Idanunta akan na el'mustapha tana murmushi, shima murmushin ya maida mata,
Arham ya dubi el'mustapha, daddy kaga mamman anty uwani.
Uwani ta dubeshi a fusacce, a ranta tace xakaci ubanka ne bari na damqeka, sai a lokacin jiddah ta kai kallonta ga uwani, ta kasa boye mamakin ta, wannan wace shiga ce uwani tayi.
'Nikam uwani da kin sauya wannan rigar cewar jiddah tana qoqarin xama kusa da el'mustapha.
Saboda me? Uwani ta tambaya tana kallonta cikin harara.
Saboda ya'yana, basu saba ganin wannan haukar ba kinga sai magana suke ai kada a lalatamin tarbiyar yara, su taso suna sabawa iyayen su.
Sai ki kauda idanunsu daga kallon jikina, amma nida gidan mijina baxaa xabamin kayan da xan saka nayi masa kwalliya ba, ke idan bakya masa ni kinga inayi.
![](https://img.wattpad.com/cover/155715841-288-k362863.jpg)
YOU ARE READING
El'mustapha
Romance'Mijin yar'uwata nake so, farin cikin da yake baiwa matarsa nake son samu fiye da hakan, so nake na rabashi da matar sa da ya'yan sa ya zamto ba kowa a xuciyar sa sai ni. El'mustapha ya shiga cikin rukunni wasu mutane da nake ganin matuqar qima da...