47

5K 411 103
                                    

Shiru yayi bai qara magana ba, ya tashi xai bar dakin,

Tace ina kuma xaka je yanxu, nayi tunanin xaka kwanta ne,

Ki jira ni yanxu xan dawo, akwai wani magani da likitan ya rubuto ki fara amfani dashi kafin muje, bana so kiyi skipping ko wace rana na kwana bakwai ne.

Ta gyada kai tana kallonsa, a dawo lfy ka kula da kyau kasan dare ne fa.

Yace dan sanda na tsoron dare ne jiddah? Yanxu xan dawo da yardar Allah, ya juya ya fice.

Tabi bayanshi da kallo kafin ta sauke numfashi a hankali tana kallon tsinin cikinta.

Ko menene aciki Allah ya raya shi, Allah ka bata ladan wahalar da tayi da cikin ya kuma albarkaci abinda ke ciki.

Tana xaune taji sallamar banan ta shigo dama taga fitar el'mustapha,

'Anty jiddah munyi waya da kaka tace xata xo duba ki gobe, tayi fama da rashin lfy ne shiyasa bata sami xuwa ba.

Murmushi kawai jiddah tayi,

Allah ya kawo ta lfy,

Banan tace amin tana qoqarin tashi,

'Yauwa hado min tea ki kawo min, nasha golden morn bai ishe ni, yunwa kuma nake ji.

Ko na kawo maki abinci mai nauyi ne?

Aa bani ruwan tea din dai, idan da sauran cake din da anty ikram taxo dashi daxu kawo min.

Banan ta juya ta fice, jiddah ta bita da kallo har yanxu ta rasa gane dalilin da ya sa el'mustapha keda feelings akan yarinyar duk da yana boye mata.

Ba abinda banan xata nuna mata, komai tafi banan illa lafiyar qafafu yanxu, ko saboda qafafun ne el'mustapha ke neman ta, ta saki uban tagumi bayan ta fada cikin tunani mai xurfi.

Har el'mustapha ya shigo dakin bata sani ba, xama yayi yana tabata,

Jiddah..... Ya kirata da qarfi,

Tayi firgigit tana kallonsa,

Yaushe kadawo? Ya bata fuska yana kallonta bayan ya ajiye ledar dake hannunsa,

Meke damunki haka, wane irin tunani ne tun daxu ina magana baki ji ba,

Wlhy ban sani ba,

'Wannan tunanin da kike if d condition becomes worse baxan taba yafe maki ba, kece kika ja komai ina qoqarina na ganin na kaucewa duk abinda xai saka ki damuwa kamar yanda likita ya fada.

Ba abinda xai faru El'mustapha, baxan taba Ma abinda xaka qi yafe min ba, kayi haquri please.

Suna haka banan tayi sallama amma bata shigo ba sai da jiddah ta bata umarnin haka.

Ta gaida el'mustapha ciki ciki ya amsa mata, kwanakinnan bata san meyasa ya canxa mata ba duk da aikin da yake saka ta duk ya daina gaisuwar ta Ma da kyar yake amsawa, kuma ta damu sosai, tana ji kamar xata tambayesa ko tayi masa laifine, ba fuskar yin hakan.

Ta sunkuya a hankali ta ajiye cup din tea din a gaban jiddah, tare da bowl din da ta xubo cake din.

'Anty jiddah xanje na kwanta bakya buqatar komai ne,

Babu Allah ya tashe mu lfy,

Tace amin, ta juya a sanyaye ta fice bata san meyasa ta damu da el'mustapha ba, bata san meyasa ta kasa cire sa a xuciyarta ba duk da tana da Islam.

Kallon abinda banan ta ajiye a gabanta yake kafin ya dube ta,

Ba dai wani abin xaki qara ci ba jiddah,

El'mustapha Where stories live. Discover now