EL'MUSTAPHA
Haske Writers Association
Home of experts and perfect writersFertymerh Xarah💞
_dis page 4 u bestyna Ummi Aysher_❤
40
'Washe garin ranar da sassafe ibrahim ya shiga asibitin,
Yana xuwa kai tsaye dakin da aka kwantar da uwani ya nufa, ta farfado tana xaune tana shan tea abinta hankalinta a kwance ba wata damuwa a tare da ita.
Shine ya taimaketa amma bata jin xata iya gaidashi illa idanu da ta xuba mashi,
An tashi lafia, ya jikin uwani.
Ta tabe baki tana yatsina fuska,
Ina so na tambayeka jiddah tana da rai kuwa?
Baiyi mamakin tambayar ba idan da sabo ya saba da wannan tambayar a duk lokacin da ya xiyarci uwani, yana tuna shine ya dauki nauyin kula da ita maganin ta da komai na asibitin duk cikin aljihunsa ne amma yarinyar ko godiya baxata iya masa ba hassalima kallon kirki baya samu daga gareta ballantana yayi darajar da xaa gaidashi, ita bata da damuwa sai ta jiddah.
Bata san cewa albarkacin jiddah da iyayenta ya saka ya taimaketa ba da kasancewar ta musulma.
Dama hausawa na fadin duk inda musulmi yake dan uwan musulmi ne kuma xuciyarshi tasha banbam da ta Arne ko ya take, dama Allah ya halicci musulmi dan xumunci da qauna ga dan uwansa musulmi,
Koda basu hada jini ko yan uwanta ka ba, ko da kuwa haduwar hanyace, amma uwani ta kasa gane darajan mutanen da taci.
Ya dubeta fuskarsa a daure, naxo na duba jikin kine xuwa gobe xaa wuce dake a rufe ki kamar yanda el'mustapha ya bada umarni.
Ta fiddo idanuwanta tana kallonsa cikin tsoro,
Ni xaa rufe? Me nayi, jiddah ce kuma ya ganta saboda me xaa rufe ni, laifin me nayi, saboda mugunta da cin amana ana baqin cikin ganina a raye ake son kulle ni a hana min walwala da jin dadin rayuwata.
Ke har kina da bakin da xaki kira wani mugu ne, akwai wanda ya kaiki mugunta a duniya ne, ki shiga taitayinki uwani kisan me kike, wlhy idan baki roqi gafarar jiddah da iyayenki ba alhakin su baxai bar ki ba.
To naji ban warware ba, kuma baxan warware ba dan har yanxu ina jin xaxxabi.
Ya fiddo mata ankwa ya nuna mata kin ganta anan tuntuni ya bada ita kuma ya rantse sai ya rufe ki gobe ko dani ko ba dani ba, naso na taimakeki amma nagane ke wawiya ce bakida hankali gwanda ya rufe ki din ya axabtar dake kamar yanda kika sa aka axabtar da jiddah, wannan qafar taki Ma naso ta lalace ta rube acire a yarda kowa Ma ya huta da baqin halinki.
Uwani ta fusata tace idan remote din duniya a hannunka yake ka maidoshi baya ka barni inda ka ganni ba sai ka taimakeni ba, waya sani Ma ko sona kake shiyasa ka nace min kai baxaka yi xuciya ka barni ba, baka ganin kowa ya gujeni ba mai xuwa inda nake harda wadanda suka kawoni duniyar saboda suna min baqin cikin rayuwa ta, nidai baxan soka ba mata biyu ne dakai baxan je a ta uku ba, el'mustapha nake so kuma sai na mallakesa.
Murmushi yayi mai cike da takaici,
Yace uwani ana maganar ki gyara rayuwarki waya kawo maganar so anan? Wace alama kika gani ta so a tare dani, daga taimako? Ko mace na rasa a duniyar nan baxan iya auren mai mummunan hali irin naki ba, mata biyu nake dasu kuma alhamdulillah basu samin damuwa ba kamar yanda kika sawa el'mustapha da yan uwansa, Kuma ina so kisani burin ki baxai taba cika na mallakar el'mustapha ba qarya kike ba sonsa kike ba, ban taba ganin irin wannan son naki ba.

YOU ARE READING
El'mustapha
Romans'Mijin yar'uwata nake so, farin cikin da yake baiwa matarsa nake son samu fiye da hakan, so nake na rabashi da matar sa da ya'yan sa ya zamto ba kowa a xuciyar sa sai ni. El'mustapha ya shiga cikin rukunni wasu mutane da nake ganin matuqar qima da...