56

5K 445 77
                                    

*EL'MUSTAPHA*

*Haske Writers Association*
Home of experts and perfect writers

Fertymerh Xarah💞


_God bless this special best friend of mine with all happiness and accomplishment in life,  I’m truly blessed to have you as my best est buddy  *khadija Ahmed KDEEY*_ 🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂

_Happy Birthday to my best daughter, Thinking of you with love on your birthday and wishing you everything that brings you happiness today and always, I’m truly blessed to have you as my best est buddy *Sumayya Halliru Dikko*_🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂



56

Uwani ta xube gurin hankalinta a tashe,

Me jiddah ke nufi da ko xata mutu baxata taba aura mata el'mustapha ba, kenan jiddah tana nufin ko ma me xatayi sai dai tayi amma baxata qara auren mijinta ba.

Yaushe jiddah ta canxa haka? Waye ya bata mana jiddah ta xama mai xafi haka, da alama yanxu bata ma da haquri qila idan an bincika ko tausayi bata da shi, waye ya bata min yar'uwa haka? Indai ba ta sami qawa mai xugata irin jamcy ba.

Taja dogon tsaki kafin ta nufi dakin su hajiya dan ta lura hajiya ma na mata wani gani gani tana so ta tambaya dalili idan itama tana baqin ciki da dawowarta gidan uban tane ta sani, ko tana baqin ciki da xata dawo gidan mijinta ne oho.

Jiddah ta ajiye airah akan bed tana kallon el'mustapha,

Wani abin mamaki, Uwani ke roqona na barta ta auri mijina a karo na biyu, bata neman gafara ta sai ma ta mijina take.

El'mustapha ya matsa kadan inda ta shimfide Airah barci take, ya tsurawa fuskarta ido yana kallonta,

Yace ai nasan jiddah mai haquri ce da tausayi, ina tunani ma yanxu tausayin ne ya saka taxo ta gayamin uwani na son komawa dakin mijinta, nasan yanxu xaki fara kuka kina roqona na maida uwani yar uwar kice ciwon xuciya zaya kamata ke kuma baki so ki rasata saboda halaccin iyayenta.

Ta xauna da murmushi a fuskarta wanda bai kai ciki ba, batayi magana ba illah fadawa da tayi kogin tunani, banan da uwani sune matsalar ta a yanxu kuma tana roqon Allah ya taimake ta ya raba ta dasu lafia.

El'mustapha ya daqo yana kallonta,

Tunanin me jiddatulmusty take yi?

Tace ba komai,

Ya tashi ya cire doguwar jallabiyar dake jikinsa, kafin ya qara kallonta,

Ina so na dauko wata mai aiki saboda Airah ke kuma kiji dani,

Ta ware idanu tana kallonsa,

What? Mai aiki, wace irin mai aiki kuma el'mustapha? Kai baka ga halin da nake ciki bane, Dame xanji ni kuma me xanyi da mai aiki.

Ban fahimce ki ba jiddah, wane hali kike ciki wanda ni ban sani ba, menene laifin mai rainon da xan dauko?

Ta tashi tana bata fuskarta tana fadin babu amma ba yar iskar da xata qara xuwa gidannan da sunan aiki ana fakewa akan mijina, kowace mace ta taso mijina, dame el'mustapha yafi sauran maxan ne, why only you?

Sai yanxu el'mustapha ya fahimci inda ta dosa, ya tsura mata ido dubi yanda ta birkice masa daga magana, sam jiddah ta canxa sosai, amma shi baiga laifi anan ba saboda ya dauko mai rainon airah shi me xaiyi da matan ne.

Yace jiddah menene dan na dauko mai tayaki rainon airah, qaramar yarinya ce fa..... ta katse sa,

Qananan yaran ne kemin raino nima ina rainon su da sun girma basu da abin so sai mijina, ni xan iya rainon airah saboda ba abinda nake yi a gidannan sai girkinka da kula da sashen ka, idan ka matsa dole sai an dauko mai raino na amince amma fa namiji xaka dauko yayi rainon airah.

El'mustapha Where stories live. Discover now