EL'MUSTAPHA
Haske Writers Association
Home of experts and perfect writersFertymerh Xarah💞
*Fatan Alheri*
Faxyfashion
Rabi'atu sk msh
Xee Yabour
Zuhura Ajiya
Kdeey
Hajja Ce
Mmn khady
Billy galadanci22
Kallon Aryan da Arham tayi hade da fadin, kuje inda banan yanxu xan fito nima, duk mgnr da takeyi jikinta rawa yakeyi tun daga kallon da el'mustapha yake mata.
Suna fita ta juya tana kallonsa cikin marairaicewa,
'Dan Allah el'mustapha kada kaqi... Shut up pls ya katse ta cikin tsawa,
'wai me kike nufi ne, me ya same ki, kinsan me kike fada, na auri uwani, akan wane dalili, ni el'mustapha na auri uwani, lallai yau na saka ki cikin jerin mata marassa hankali da wayo, idan har wasa kike kada ki qara kwatanta min irin wannan wasar domin baxakiji dadina ba, ya tashi a fusacce ya bar falon xuciyarsa na tafarfasa.
Kuka take yi sosai, kukan da bashi da mafita illah ta cigaba da convincing el'mustapha har lokacin da xai yarda da auren, su taimaka su ceci rayuwar uwani dake kwance a asibiti tana fama da ciwon qirji.
Binsa tayi dakin, bakin gado ta xauna tana jiransa har lokacin da ya fito wanka, da sauri ta qarasa gabansa kafin yayi wani yunquri ta riqo qafafunsa tana kuka.
Fincike qafafunsa yayi daga gareta, haushinta yake ji sosai, abinta ya xama rainin wayo, taya xata xo masa da maganar ya auri uwani, wai uwani ya qara nanatawa a xuciyarsa yana mata wani irin duba mai cike da dimbin mamaki, tayi saurin sunkuyar da kanta baxata jure kallon kwayar idanun sa ba a yau.
Doguwar jallabiya ya xura ya fita daga dakin gabaki daya, sosai jiddah ta shiga damuwa.
A daren ranar yini tayi sukuku ba walwala a tare da ita, da kyar ta iya yin wanka, binni binni tana kallon agogo dare ya tsala sosai amma el'mustapha bai dawo ba, bai xo yaci abinsa ba ita Ma ta kasa cin abincin, ta kira wayarsa tana ringing bai dauka ba.
A falonsa ta xauna xaman jiransa, barci ya soma fisgarta, sanda ya dawo kallo daya yayi mata ya dauke dubansa daga gareta, motsin dawowar sa ya farkar da ita, tabi bayansa da sauri lokacin da yake qoqarin cire jallabiyarsa.
'Dan Allah ko menene ka ajiye shi a gefe kayi haquri kaxo kaci abinci, dan Allah mijina kada kamin wannan horon, lets save a soul, tana buqatar taimakon mu, ya kake so tayi da rayuwarta Allah ne ya dora mata.
let her die, sai me? Ina ruwan wani, idan ke damuwarta damuwarkice sai akace harda el'mustapha? Duk garinnan ba namiji ne sai ni, ya nuna ta da yatsa cikin matuqar bacin rai,
Look jiddah, I can't take it anymore, kada ki qara xomin da magana irin wannan.
Kwanciya yayi akan gado bayan ya rage hasken dakin, jiki a sanyaye ta hau gadon matsawa tayi sosai xuwa ga jikinsa, dogon tsaki yaja bayan ya janyeta daga jikinsa, juya mata baya yayi hade da Jan blanket ya rufe jikinsa har kansa.
Bata iya daukar wannan fushin ko kadan, xuciyarta ta karaya, ta soma hawaye sosai hade dasa hannu ta toshe bakinta kada sautin kukan ya fito,
Kadan kadan yake jin sautin kukanta, yana jinsa har cikin ransa, he can't take it anymore, ya juyo a fusacce hade da kunna bedside lamb,
Ban nemeki ba kece kika kawo kanki baxaki xo kidameni da sheshshekar kuka anan ba ki hanamin barci You can leave pls, ya fada lokacin da yake qoqarin hada ido da ita.
Haduwar idanuwansu ya sanya xukatansu bugawa lokaci daya, akwai soyayya mai tsanani tare da wadannan masoyan, bacin rai ke dawainiya dasu, yanda idanunta sukayi luhu luhu ya sanyashi weakness, bai qara magana ba ya juya ya kwanta abinsa, ganin haka ya sanya ta rungumosa ta baya, daga shi har ita suka sauke numfashi lokaci daya ba kamar ita kamar wacce tayi gudun fanfalaqi.
*
Kusan sati daya babu canji daga el'mustapha, tun da safe xai fice ya barta baxai dawo gidan ba sai tayi barci, sosai ta shiga damuwa, ga uwani tunda ta fuskanci akwai matsala ta kwanta ciwon qarya bata cin komai sai Lipton, daga ita har jiddah sukayi wata irin rama,
Ana haka mama taxo gidan, yanda taga jiddah sai da hankalinta ya tashi,
jiddah ko dai ciki ne dake kikayi wannan ramar?
Ta girgixa kanta cikin jin nauyin ta,
'ki gayamin damuwar ki, idan el'mustapha ne inji, kinga yanda kika lalace kuwa?
Shiru kawai jiddah tayi batare da tayi magana ba, sosai mama ta matsa da sai taji damuwar jiddah har lokacin da tagayamata komai tana kuka.
'Wannan mgnr babu dadin ji Sam jiddah, el'mustapha baxai auri uwani ba ni kaina bana son yarinyar.
Mama ki duba halin da take ciki, tana axabtuwa da qaunarsa, dalilinsa ta kamu da ciwon xuciya, kije kiga yanda uwani ta koma a yanxu, baxan iya samun nutsuwa a yanxu ba har sai uwani ta sami abinda take so, dan Allah ki saka baki ya amince da mgnr mama, ta soma kuka sosai,
Mama taji tausayin jiddah, ke kam rayuwarki dabance jiddah, kowace mace tana gudun kishiya ke kina roqo da kukan ki, kuma yar uwarki kike so a aura, ina ma laifin wata qawar kice daban amma Sam rayuwar uwani bata dace da 'dana ba.
Uwani ta canxa daga yanda kika Santa mama, xo kiga yanda ta dawo, sukaje dakin uwani na kwance tsakiyar dakin tana jin motsin shigowa dakin ta soma wani irin numfashi gwani ban tausayi.
Mama ta riqe haba cikin salallami da mamakin yanda uwani ta dawo,
Yanxu saboda el'mustapha ne yarinyar nan ta dawo haka, lallai abin a duba mata ne.
Suka koma falo suka bar uwani na murmushi, sosai mama ta tausayawa halin da ta tsinci uwani akai tana tunanin idan yar'ta ce a haka ya xataji.
Bayan kwana biyu sai ga el'mustapha ya shigo dakin jiddah tana xaune tana tana duba wayarta, yanda ta ganshi sai da ta tsorata.
'lallai ashe da gaske kike, kinfison farin cikin uwani akan farincikin ki da nawa, har xaki iya gayawa mama ta tursasani akan uwani batare da kinyi tunanin ni kin cutar da tawa rayuwar ba, kinyi nasarar aure na da uwani amma abinda xai biyo baya daga ranar da aka daura auren ki kuka da kanki....
Ya watsa mata wata harara yana mata wani duba kafin yaja dogon tsaki ya bar dakin.

YOU ARE READING
El'mustapha
Romance'Mijin yar'uwata nake so, farin cikin da yake baiwa matarsa nake son samu fiye da hakan, so nake na rabashi da matar sa da ya'yan sa ya zamto ba kowa a xuciyar sa sai ni. El'mustapha ya shiga cikin rukunni wasu mutane da nake ganin matuqar qima da...