Tayi yunqurin tashi ya hanata, yasa yaransa suka riqeta gam sai kuka take Kamar ranta tana kallon inda Assad yake a sume......
Farfaďowar ta yayi dai dai da shigowar Dr. Bakori da nurse a bayansa,
Ta juya tana kallon ďakin da take, a asibitine kafin ta juya tana kallon likitan, Abubuwa na soma dawo mata a kai, tun daga lokacin da aka fito dasu a mota hr xuwa lokacin da aka bigi Assad akai da lokacin da...... tayi Saurin rumtse idanuwanta da ta tuna, wasu hawaye masu xafin gaskene suka xubo mata, sautin kukanta na fito sosai,
Dr. Bakori ya dube ta,
What is wrong Farah? Akwai abinda ke maki ciwo ne, tayi shiru tana kuka, ya qara matsowa kusa da ita,Talk to me Farah,ta maida kanta jikin pillow tana kuka sosai, ya dubi nurse ďin bayan ya cire farin glass ďin idanuwansa, Abba ya shigo a hanxarce khamis da Anna na bayansa, tana jin muryar Abbanta ta ďago a firgice duk ta tsorata,
Meya faru, meya sameki Farah?
Assad Abba, ina Assad? Nan da nan ya bata rai shima khamis ya sauya fuska, Anna ta rungumota jikintaMeya sami Assad? Inaji tare kuka fita dashi ko, ina Assad ďin?
Da tsananin mamaki, xuciyarta na bugawa tamkar xata hudo qirjinta ta ďago tana kallon Anna da mutanen dake dakin kafin ta qara kallon Anna,
Anna sun dake sa ne fa, sun buga mashi wani abu aka ni kuma sai suka........ta fashe da kuka mai tsananin gaske, nan da nan hankalin Anna na tashi,
Bn fahimceki ba, su Waye suka dake sa, meya sami Assad ďin? A ina yake ynxu?
[02/12, 10:10 p.m.] Pherty👯: Abba ya dubesu,Dama da Assad kuka fita,
Farah ta gyada Kai tana kallonsa idanunta jawur,
Subhanallah amma.... tor... ina Assad ďin ya shiga, meya samesa, ke kadaice akace angani bakin hanya,
Na shiga uku, Assad Anna sun gudu dashi, ki taimakeni, Abba Ka taimakeni, dan Allah ku taimakeni ku dawo min da Assad kada Su kashe shi, wlhy baxan iya rayuwa ba sai da Assad, sun cutar da rayuwata Anna,
Jikin Abba nayi sanyi sosai, tor Ina Assad ďin ya shiga, ya juya yana kallon khamis,
Assad fa? muje akai report police, ya juya khamis yabi bayansa ba dan ya so ba, shima baiga dalilin Su na damuwa ba, likitan ma ya fita
Anna Assad xai tsaneni, Assad xai daina sona, ki taimakeni,
Meyasa Farah, me kika yi masa? ta girgixa kanta tana wani irin kuka,
Anna ma hankalinta a matuqar tashe yake badan komai ba sai dan rashin Assad, idan mahaifiyarsa ta dawo me xasu gayamata akan batan yaronta?
Kwana biyu ba Assad ba labarinsa, duk inda ake sa ran ganinsa an duba babu sa, abokaninsa duka suna cikin tashin hankali musamman wadanda suka xo auren, barin ma kamar Farah da bata cikin hayyacinta, Anna Kuwa hr kuka tayi saboda baqin ciki,
Umar da jabir sun fi xargin kamar da sa hannun khamis a batan Assad, duk bincikensu sun kasa gano komai Sannan khamis ďin yana tare dasu a koda yaushe gurin neman Assad, tor Ina Assad ya shiga? 🤔
One week,
Farah xaune da Anna a falo, ta rame tayi wani xuru kamar ba Ita ba, Abu biyu ke matuqar damunta a xuciya,
Ki Shanye wannan tea ďin Farah, shikenan sai ki xauna da yunwa cikinki ba komai,
Anna baxan iya sha ba, ko wane lokaci xuciyata xata iya bugawa, ki nemo min Assad, ta fashe da kuka, jikin Anna na soma rawa inda sabo ta saba da kukan Farah akan Assad amma ita babban damuwarta rashin sanin inda Assad ďin yake, cikin wane hali yake, idan ummansa ta dawo bayanan me xasu gayamata, ta soma hawaye ganin Anna na kuka Farah ta qara rikicewa haďe da tsananta kukanta, kenan ma baxaa ga Assad, kada fa sun samesa a mace ne ake boye mata,
Abba ya shigo falon, jikinsa a sanyaye da farar takarda a hannunsa kai tsaye ya miqawa Farah takardar fuskarsa ba walwala, ta ďago tana kallonsa tana kallon takardar kafin ta karba,
_'Ni Assad Aliyu na saki Farah saki ďaya, ba dan komai ba sai dan bana sonta, ban taba jin son ta a xuciyata bane, dama nasha gaya miki baxan iya soyayya dake ba, Sam *ni da ke* bamu dace ba, duk soyayya ta dake yaudarace,ina jajantamiki Kan abinda ya sameki da waďancan yaran idan kin sami miji kiyi aure, Assad ya miki nisa._
_'Malamataaa_,Jikinta hr wani rawa yake, takardar ta faďi daga hannunta, Anna ta ďauka tana dubawa,
Idanunta sunyi jawur cike da kwallah ta ďago tana kallon abbanta da shima ya kafeta da Idanunsa Ransa a matuqar bace........
YOU ARE READING
NI DA KE....
Historical FictionBayan fitarsa Farah ta tashi ta nufi dakinta da sauri tana kallon madubi, Ita baqar mace ce, Assad ma yafita Haske, ita ba ma'abociyar hijab bace sai gyale, haka xalika bata iya xama da Fuska batare da make up ba, tana da kawaici amma bata da haqur...