After 2 days
Sai shirye shiryen fita da Ita madina ,hr sunyi mata biza, mansur ne kawai baxaa je dashi ba hakan ya qara qona ransa yaje ya sanarwa abokansa,
da yawa akwai wadanda na fishi shekaru, 13,14,
Bayan fitowarsu yake gayamasu xaaje da hafsat madina bada shi ba,Chuďi, kai kan bakada wayo, sai aje da ita bada kai ba,
Wani kuma yace, iyayenka kudin banxa kawai suke kasheta yarinyar nan aljanace yar ruwace ,muje musanyata a ruwa kugani,
Mansur ya xaro Idanunsa yana kallonsu,
Nidai inajin tsoronta ynxu baxan qara dukantaba,Kaikam bakada wayo mansur, baffanka yana da kuďi amma ko mota bai siyama ba saboda hafsat gashi komai take so anayi mata banda kai,
Mansur yace baffa Yace sai nagama secondary school Sannan xai siyamin Mota,
Ba wani wayo yake ma baxai siyama ba indai hafsatu na nan,
Tor me xanyi mata,
Mu boyeta ynda mukaga anayi a film, mu ďaure qafafuwanta da hannayenta,sai bayan kwana biyu muce baffa ya bada kuďi mu badata sai muje mu siye Mota da kudin muna xuwa party,
Suka soma sowa sunji dadi da wannan shawara bakamar mansur da akace shine babba,
Washe gari bayan tagama shiryasu ta sanya masu uniform, suna dinning table gabaki dayansu suna brkfst, sai ta ga kamar hafsat ďin tayi sukuku ga jikinta yayi xafi rau,
Anna tace hafsat ko ba lfy ne naji jikin sai a slow, nima yau da weakness na tashi
Baffa ya dubesu yana fadin nima haka na tashi yau bana jin daďi,
Hafsat najin haka ta kyalkyace da dariya, suka xuba mata idanuwa, ta nuna mansur da yatsanta kafin ta nuna kanta tare da alamar babu ta, (a mafarki aljannunta sun nuna mata wani abu)
Mansur ya tsorata ainun, iyayenta komai basu fahimta ba ga mamakin Su sai gata tana hawaye Abinda bata taba yiba,
Farin ciki gun Anna da baffa baa mgn aganinsu alamar sauqi ne yaxo mata, ita hafsatu itakadai tasan kukan me takeyi,
Menene hafsat, ta girgixa kanta,
Meya saki kuka, meke maki ciwo, nan ma ta girgixa kanta, hr suka gama cin abinci tana hawaye, Sanda xa'a kaisu Skul Anna na tsaye taji ta kira sunanta,Mamiiiiiii
Mami... ta maimata tana kallon hafsat da tsananin mamaki, tsoro qarara ya bayyana a fuskarta hakama baffa,Me ke faruwa, yau hafsat tayi mgn, hafsat ta kirata da Mami,
tana dariya taxo ta rungume Anna kafin ta rungume baffa, ya sumbaceta a goshi haďe dayi mata wasu adduo'i, sosai jikin Anna yayi sanyi da lamarin hafsat yau, ta juya tana ďaga masu hannu driver ya shigar da Ita Mota,
Bayan driver ya ajiyesu ya juya, mansur yaja hannunta a maimakon suje cikin Skul sai ya nufi bayan makaranta da Ita kamar ynda sukayi mgn da abokansa,
ta karkato da kanta tana kallon ynda yake jan hannunta, sun qara rufe mata baki, sai hawaye take tana tausayin halin da Iyayen nata xasu shiga,
Sun yi nisa sosai da Skul ďin sun nufi cikin daji abokansa na jiransa suna ganinsu suka qaraso, sukaje suka xaunar da Ita a qasa kusa da wani qaton rafi, kanta na rawa take kallonsu sai hawaye take, mansur Kuwa jikinsa yayi sanyi sai tausayin ta yake,
Ka xo muje class mu barta anan, ba dan ya so ba ya yabi bayansu yana waiwayenta itama tana kallonsa,
Bayan sun shiga class ya kasa samun nutsuwa, ynxu yana son qanwarsa, ya ďauki excuse xaije fitsari, da gudu ya fito yaxo gurinta, ya sameta tana kuka sosai, ya kwanceta ya xauna kusa da ita, karo na farko kenan daya taba rungumeta xuwa jikinsa,
YOU ARE READING
NI DA KE....
Historical FictionBayan fitarsa Farah ta tashi ta nufi dakinta da sauri tana kallon madubi, Ita baqar mace ce, Assad ma yafita Haske, ita ba ma'abociyar hijab bace sai gyale, haka xalika bata iya xama da Fuska batare da make up ba, tana da kawaici amma bata da haqur...